← Book details Abinda Ke Cikin Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 48 OF 108

Sashe 48

Abinda Ke Cikin Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Ina son ku dauki kaddara Khadija, aure dama mukaddari ne, ki godewa Allah ya baki lafiya damar raya sunnar ma'aikin mu annabi Muhammad S.A.W. Wannan itace jarabawar ku, ya kamata ace kunyi tawakkali wajan karbar ta yadda Allah zai ji tausayin ku a wani barin na rayuwar ku ta nan gaba. Muna muki fatan alkairi cikin auran da zaki yi, daman Allah ya riga ya rubuta ba zaku auri junan ku keda Mas'oud ba, ki yiwa iyayen ki biyayya mun san tabbas bake kika guje shi ba daga Allah ne. Sai anjima Khadija Allah ya yi miki albarka kinji, Allah ya kare rayuwarki kuma a duk inda zaki tsinci kanki.”

Tana kaiwa nan ta katse. Ni kam me zanyi ban da sulalewa kasa na rushe da kuka, na dinga yi ina yin cilli da duk abin da na gani kusa dani. Su Zarah suka zo suna bugun kofar saboda sun ji abin nawa ya yi yawa, naki budewa shine suka je suka kirawo su Mami sannan na bude tare da fadawa jikin matar kawu Hashimu.

“Ya isa Dije wannan kukan na meye kuma?”

Na samu kai na da cewa.

“Baffa na da Ummata duk basu cikin duniyar nan.”

“Lahhh haba Dije baga mu ba, ko mu baki yi farin ciki da ganin mu ba sai mu koma inda muka fito dan farin cikin ki.”

“A a Aunty wallahi ba haka nake nufi ba, kawai tuno dasu nayi.”

“Allah sarki, daman haka ne wata rana zaka ji ina ma kana tare da su. Amman kiyi hakuri ki dena kuka kinga gidan aure zaki je kar kije kiyi rama dama gata nan duk kin fada.”

Haka suka dinga lallashi na damin nasiha har sai da nayi shiru sannan suka rabu dani. Ban kuma yin kuka ba saboda bana so a zauna ayi ta min magana kar naje na bata musu rai su ji haushi na bayan bani da kamar su a duniyar nan.

*RANA BATA KARYA...*
(Sai dai uwar diya taji kunya.)

Tun da ya tashi yake jin wata ni'imatacciyar iska tana ratsa sassan jikin sa, a cikin ransa yasan hakan baya rasa nasaba da auran Khadija yar jarida da zai yi, yarinyar da ta tafi da rabin imanin sa. Yaji a duniya yana son kasan cewa tare da ita a cikin gidan shi, komai sabo haka ya tana da, koda yake an tanade su ne dan yau ce ranar da zai yi tafiyar nan zuwa Cyprus. Amman shi a nashi bangaren zasu kasan ce ne matsayin na daurin aure. Daure da towel ya fito ya tsaya wajan dressing mirror yana karewa kanshi kallo. Matashin sarki kenan mai ciki ta nagartacciyar haiba da cikar zati. Mijin Shaheedah angon Khadija a yau da ikon Allah.

Lotion d'in sa ya dauka tare da bin sassan jikin sa yana shafawa. Bayan ya gama tsab ya kuma bin jikin da oil perfume da kuma body spray masu azababban kamshi.

Shiga ya yi wacce take bayyana cewa shi din sarkin ne ba wai carki ba. Ya Subahanallahi tsarki ya tabbata ga wanda ya halicci wannan bawan nasa, ya kawata shi da gabobi managarta masu cikakkiyar haiba. Lallai ba karamin kariya rawanin da yake sawa yake bashi ba, dan irin su sarki Salman ne suke sawa yan mata suna mafarkin mallaka a matsayin mazajen aure, abokan rayuwa na har a mutu. Kamshinsa kawai ya isa rikita zuciyar mai shaka.

Ya riga yayi sallama da kowa tun a daren jiya, shiyyasa yana kammala shirinsa kai tsaye ya fito falon farko na sashen nasa. Cikin hanzari Jakadiya ta zube tana mika gaisuwarta. Kafin ta mike ta fita da hanzari ta sanar da fitowarsa.

Taku yake tamkar wani hawainiya, ga kuruciya ga jinin mulki na kai kawo a kowacce jijiya da gabban jikinsa. Tun kafin bayyanarsa garesu hadiman sashen nasa duk suka zube domin mika gaisuwarsu gareshi. Tafiya yake kawai batare da amsama kowa ba. Kamar kullum idanunsa na sake cikin gilashinsa na ka'ida.

Sai da ya wucesu gaba daya kafin wasu suyi saurin mikewa su dafa masa baya. Sun iske fadawa suma tsaitsaye a kofar fada suna jiran fitowar mai martaban. A take suma dai zubewar duk sukayi suna mika gaisuwa.

Suma dai basu samun amsar ba, sai cikin fadawanne ke ansawa da fadin,

"Sarki yaji ku, shima ya gaisheku".

Lumshe idanu sarki Salman yayi daga cikin gilashinsa yana sauke wata ajiyar zuya a hankali, wani irin yanayine ke sauka masa a gabban jiki da baisan na minene ba. Haka dai akai masa rakkiya har gaban jerin motocin dake a jere zuka-zuka suna jiransa.

Ruf dogarai sukai masa da rigunansu har ya shige daya daga cikin motocin data fi kowacce koshi da daukar hankali, sai da aka rufe kofar sannan suka marmatsa suma suka nufi motocin da zasu shiga.

Kamar yanda ya saba sai da ya karanto addu'ar fita a gida a cikin ransa, kafin motocin su fice daga masarautar zuwa airport.

*_GIDAN BIKI KHADIJAA(DIJE)_*

———-
_Afuwan! Kunji shiru ko? Wallahi kwana biyu inata fama da chronic ulcer. Har takai na kwanta a asibiti na yan wasu kwanaki shysa kukaji shiru, Ina fatan na same ku lpy? Nagode k’warai da addu’oin ku. KIBIYAR ajali zai cigaba da samuwa Insha Allah da zarar naji karfin jiki na sosai.. Na gaishe ku, Gaisuwa mai kima.._

ZAFAFA BIYAR
NA KUDI NE:::

Duka BIYAR 5 zaku samesu akan garabasar naira 700 kacal,

Guda hudu 4 Kuma 500,

Guda uku 3 Kuma 450,

Guda biyu 2 Kuma 400,

Guda daya akan 300.

Ma'ana
Each one is 300
2 is 400
3 is 450
4 is 500
5 is 700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO- *0812652655*
ACCOUNT NAME- *HAFSAT LAWAN GAMBO*
BANK NAME: *ACCESS BANK*

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

*+234 903 234 5899*

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

*09033181070*

Karku Bari ayi Babu ku domin wannnan salon na daban ne
SABUWAR SHEKARA
SABON SALO

TEAM#ZAFAFABIYAR🔥Wannan littafin na kudi ne, AMANA CE, duk wanda yayi mana sharing dinsa shi ALLAH! Idan kina/Kana so ki/ka karanta ki/ka tuntubi numbobin nan*

*0903 234 5899*
Or
*09033181070*

Page 22
Hansatu Rano

***
Hannu tasa ta toshe kunnuwan ta saboda hana su jin yadda ake gudanar da daurin auren wanda kamar a tsakiyar dakin da take ake daurawar, daidai saitin gidan nasu akwai loudspeaker din masallacin a jikin wata pole shiyasa duk abinda ke faruwa a masallacin kowa na jinsa. Rawa taji jikin ta ya fara, alamun zazzabi na neman rafketa daidai lokacin da mutumin dake fad'an duk abinda ke faruwa a cikin masallacin saboda wadanda ke waje suji, ya ce

"An daura auren S..." Bata iya bari taji karashen ba ta kwalla k'ara da karfi tana sake matse kunnenta. Da sauri Umma ta shigo d'akin a rikice,jin karar ta, wanda yayi daidai ta sanarwar daurin auren da kuma yadda abin ya sauya salo, babu wanda mamaki be kamashi ba, amma kafin su kai ga neman karin bayani suka ji ihun ta. A kwance take a k'asa tana kuka sosai,har tana kokarin shid'ewa, da sauri Umma ta riko ta

"Baki da hankali? Ko kuwa baki da tawakkali ne? Bance miki kiyi hakuri ba komai yayi zafi maganin sa Allah ba? Why? Wannan sam ba halin k'warai bane, rashin yarda da kaddara ne, Allah na jarraba bawan sa ta fuskoki daban daban, domin yaga karfin imanin sa. Kika san dalilin da Allah ya zaba miki shi a matsayin miji? Ko kinsan cewa sau da dama muna son abu amma ba alkhairi bane a garemu, sai Allah ya barmu da zabin mu yaga yadda zamuyi. A komai zabin Allah shine gaba, dan haka ki tashi kafin mutane su gama gane halin da kike ciki a samu abin magana daman ana ta kus-kus, ki karfafa jikin ki, ki karbi zabin da Allah yayi miki."

"Umma an daura fa." Tace tana jan kuka

"Eh an daura, kuma aure ya dauro ba."

"Shikenan." Tace sai kuma ta sake saka kuka

"Wallahi Umma mutuwa zanyi."

"Amrah?" Umma ta kirata tana bata rai

"Kar na kuma ji kin fad'i haka."

Sai ta mik'e

"Ki karfafa jikin ki, uwani zata shigo ta taimaka miki ki shirya."

Da kai ta amsa ta koma ta kwanta, da gaske kenan har Umman ma ta daina sauraron ta, ta daina tsaya mata kenan?"

   Toh idan ta tsaya mata ma me zata iya yi tunda an riga an daura? Ta zama matar shi sai abinda yaga dama yayi, shikenan ita rayuwar ta, ta kare babu sauran abinda zai kuma birgeta.

Tana jin sanda Uwanin ta shigo, ta shiga ta had'a mata ruwan wanka sannan ta fito, da k'yar ta tashi ta shiga, ta taba ruwan jin da d'an sanyi sai ta kara na zafin yayi zafi sosai saboda yadda take jin sanyi na hudata, ta dade a ciki tana fatan ace ba gaske bane duk abinda ke faruwa, komai ma be faru ba tana chan tana rayuwar ta hankali kwance. Jin an taba kofar ne yasa tayi saurin karasawa ta fito, ta zauna bayan ta saka kayan da aka ajiye mata na wani rantsattsen lace fari tas da Afrah tasa aka dinka mata shi, ba yadda batayi da ita akan bata so ba amma ta share ta suka je da wasu cousins dinsu suka rakata wajen wani tela. Kayan sun yi kyau kuma sun zauna a jikinta sosai, tana zaune saitin mirror tana kallon kanta da fuskarta da tayi fayau babu ko mai balle ta sami arzikin powder aka turo dakin. Afrah ce da mukarraben ta, sai wata matashiyar budurwa a bayan su dauke da jaka.

"Ga Amaryar nan Feedo, dan Allah ki fito da ita sosai saboda angonta ya kasa gane ta, ya kara akan sadakin da ya bayar."

"In sha Allah."
Chapter 48 · 0% Book details