← Book details Abinda Ke Cikin Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 108

Sashe 24

Abinda Ke Cikin Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Dan Allah Mamah, ko zan iya sanin dalilin daya dawo daku nan kasar kuke zaune kuna rayuwar ku ba tare da dangin ku ba? Ranar da mukayi magana da Baba ya fad'a min wata magana data tsaya min a rai, yace

"Ba ko yaushe ne rayuwa take tafiyar wa mutum a yadda yaso ba, sau da dama abubuwa na chanja salo da alkibla daga inda bakayi zato ko tsammani ba, kuma yace min zuciyar mutum birnin sa, sannan yace min Abinda Ke Cikin ZUCIYA, baki ba zai iya furta shi ba, haka kuma yafi gaban a tona, ya kuma kare da cemin mutum mugun icce, kar nayi saurin yarda da mutum domin akwai cuta me muni da girma tsakanin mutum da mutum."

"Tun daga ranar nake bitar wadannan kalaman nasa, na kuma yi musu waje na musamman a cikin zuciya ta, na kuma auna su na dora su a mizanin abinda nake tunanin shine makasudin zuwan ku nan."

Da gefen dankwallin kanta tasa ta share hawayen da suka fito tunowa da tayi da abubuwan da suka faru a baya, abubuwan da suka kasa barin birnin tata zuciyar suke cigaba da nakastata suka yi mata raunin da warkewarsa zai yi matukar wuya. Sai dai bata cire mijinta a cikin mutanen da suka taimaka wajen rugujewar rayuwar ta ba, duk kuwa da ya bata TABBACIN bashi da hannu akan duk abinda ya farun ya kuma yi iya kar kokarin sa wajen son tabbatar mata da gaskiyar sa, sai dai har xuwa yanzun bai xo mata da gamshashiyar hujja ba!

"Idan har ka shirya sauraron labarin mu, zan sanar dakai, ko hakan zai taimaka wajen rage abinda nake ji."

"In sha Allah." Yace cike da zakuwa

****
*Masarautar Saji*

*Tuna baya*

Duhun da ya mamaye sararin samaniya ne ya shiga yayewa yana maye gurbi da hasken asubah, mirza idanun ta tayi, ta mik'e ta sauke kafafuwanta a hankali suka sauka a lallausan carpet son din dake ajiye a gaban gadon, agogo ta fara kalla, sannan ta wuce zuwa toilet ta dauro alwala, ta fito ta shinfida abin sallah tayi sallah, ta zauna tana azkar har rana ta d'aga, tashi tayi ta zauna saman gadon sannan ta daga waya tayi kira, kofar ta bud'e sannan suka shigo su uku, suka zube suna diban gaisuwa

"Barka da tashi tauraruwa me haske, gimbiya me tashe, Allah ya ja da kwanan ki, ki dade kiyi karko gimbiyar masarautar Saji."

Dan murmusawa tayi, yana cikin abinda take so a al'adar masarautar, wannan kirarin da ake mata tun bayan da sahibin ta ya d'ane kujerar Mulkin Masarautar take amsa sunan gimbiya sarauniya. Shekarar ta, ta biyar kenan a cikin masarautar, tun bayan da ya aurota ya kawo ta, abubuwa da yawa sun faru a shekarun nan, sai dai bata taba daga kai ta kalle su balle har su daga mata kai, kai tsaye take abubuwan ta kasancewar ta wadda tazo daga nahiya daban da tasu, karatu ne ya had'a su, daga nan suka fad'a soyayya har ta kaisu da aure ya kuma dauko ta ya kawo ta nan din, daga dangin ta har nasa babu wanda yaso auren, sai dai tun da suka samu albarkar iyayen su suka rufe idon su, suka cimma burin su na zama a inuwa daya. Bata fuskanci wani abu a zaman ta da sirikinta saboda yana kaunar ta a matsayin ta na Matar babban dansa, wanda ya kasance sarki a lokacin har zuwa yanzu da Allah ya karbi ransa, matan sa uku na aure wanda ya mutu ya bari, sai mahaifiyar Usman da ta rasu tun yana yaro, be taso da ita ba, haka kuma be taso cikin masarautar ba har sai ya kammala karatun sa baki daya ba kuma akasar yayi ba, a lokacin kuma yan uwan sa da suke uba daya kowa ya kawo karfi, kuma dukkaninsu kowa yana da burin gadon mahaifin nasu, da farko sun dauka dadewar da Usman din yayi a kasar waje ya sauya masa tunanin sa akan sarautar, sai dai yadda ya dawo da karfin sa tare da maganar aure yasa jikinsu yayi sanyi. Tun da ya dawo kullum suna tare da mai-martaba mahaifin nasu suna tattaunawar da babu wanda yasan me suke cewa, haka har akayi auren kowa kuma yayi tunanin a lokacin sarkin zai yi murabus ya bashi amma sai akaji shiru, hakan ya kwantar musu da hankali har aka kawo yanzu da babu ran mahaifin nasu kuma ba tare da wani dogon tunani ba aka nad'a shi ya haye kujerar.

Juya ruwan take tana wasa da hannun ta, sosai ruwan yayi mata matukar dadi ga wani kamshi na musamman dake tashi, sai data dau dogon lokaci tana wankan sannan ta fito, ta shirya cikin shigar manyan mata yan kwalisa, sannan baiwa guda ta taimaka mata wajen saka alkyabbar da ta zama mata kamar dole daga satin da ya wuce zuwa yanzu. Katafaren falon ta ta isa,tare da jagorancin bayi masu yawan gaske da aka kara yawansu a shashen nata tun bayan nadin sarautar, suke mata dukkanin hidima daidai da magana da suna da yadda zasuyi su karbar mata da tabbas ba zaà barta tayi ba, abinci ne birjik kala kala aka jere mata, ta kishingid'a kadan dan bata da muradin cin su a halin da take ciki, burin ta d'aya ta ganshi, ta kuma zauna dashi kamar yadda suka saba kafin satin da ya gabata komai ya chanja ciki harda ganin sa da yayi mata wuya, da farko ta kasa sabawa da hakan sai dai a hankali ta fara sabawa tunda ta riga ta gane hakan shine mulkin, shine sarautar Kuma shine girman da mutane da yawa da suka shigo yi mata Allah sanya alkhairi suke fad'a mata. Amma dole ne ta ganshi dan gaskiya ba zata iya rike abinda ke cikin zuciyar ta ba na tsawon wani lokaci. Baiwa guda ta tasa ta aika zuwa wajen jakadiya tayo mata iso ta sanar da ita tana bukatar ganin sarkin a yanzu. Sakon da baiwar ta dawo mata dashi ya bata mata rai sosai, ba zata samu ganin sa ba saboda wani muhimmin tattaunawa da suke da manyan fada, ranta a bace ta koma ciki tana jin kamar mijin nata be chanchanci sarautar ba idan har hakan zai hana mata ganin sa a duk sanda taso ta kuma yi muradi.
   Wunin ranar gaba ki daya ta kasa sukuni, tun bayan data tabbatar da juna biyun dake jikinta bayan shekara biyar da sukayi da aure,burin ta kawai ta ganshi ta bashi kyakkyawan labari, sai dare sannan jakadiya tazo tafiya da ita zuwa shashen nasa, tana shiga ya taso da sauri ya tare ta, ta dan bata rai ta zauna a gefe, sai da yayi ta ban baki sannan ta sanar dashi labarin cikin, yadda tayi tunanin zai je sai ma taga kamar yafi hakan, farin ciki sosai ya nuna yayi ta gode wa Allah.
    Sai dai, a lokacin da suke cike da farin cikin wasu mutane dake ciki da kewayen masarautar na cikin bakin ciki, bakin cikin abinda zai faru watan watarana.
    Kasancewar cikin ta bame laulayi bane sai ya zama bata shan wahala,babu kuma wanda yasan da maganar cikin tun da tsohuwa Hajja ta kirawo su ta hanesu da d'aga zancen, dukkan su basu kawo komai ba, dan basuyi tunanin akwai wani abu da zai iya shiga rayuwar su, da zuciya daya suke zaune da kowa musamman ma ita da bata san kan dawar garin ba.
    Tana kwance daga gefen sa, hannun ta a saman cikin nata tana ta jujjuya shi, ta rasa dalilin da yasa take mafarke mafarke sosai yanzun wanda da batayi, wani lokacin har idan tayi irin mafarkin bata sha'awar sake komawa baccin saboda tsoron kadda ta sake yi, hakan ce ta faru yanzun ma, bayan ta farka sai ta kasa komawa ta cigaba da juyi, gefe ta kalla ta ga yana baccin sa hankali kwance, sai ta muskuta ta cigaba da aikin tunani kafin a hankali ta fara jin kamar ana motsa window din d'akin da suke ci, kallon wajen tayi sai taga kamar inuwar mutum ta jiki, damke idon ta, tayi taja jikinta ta matsa sosai kusa dashi, tana tunanin waye zai zo wajen a wannan daren, bayan haka ma kewaye wajen yake da masu tsaron su, tana kwance luf taji magana k'asa-k'asa, tayi kokarin gane me aka cewa ta k'asa, sun d'an jima suna tattaunawa a wajen kafin taji an bar wajen. Da safe ta tashi da wata irin kasala, ta k'asa mikewa daga gadon, har ya gama shiryawa ya fita idonta na kulle tana jin wani abu yana mata yawo aka, wajen goma na safiyar ciwo ya turketa, kafin Sha d'aya jini ya balle mata, da k'yar aka samo kanta dan ba karamin galabaita tayi ba, sai dai cikin dake jikin ta ya lalace.
   Ko da ta farfado aka fad'a mata cikin ya zube tayi kuka sosai dan ba karamin son yara take ba, ta kwallafa rai da cikin sai dai dole ta hakura tayi tawakkali. Haka rayuwa ta cigaba da garawa duk sanda ta samu ciki toh sai ya lalace, sosai hakan yake damun su,sai dai basu kawo komai ba a ransu balle su zargi wani akan hakan ba.

KUNA BUƘATAR A TALLATA MUKU KAYAN SANA'ARKU A PAGES ƊIN BOOKS ƊIN ZAFAFA BIYAR 2021?.

To kuzo ga dama ta samu💃🏻💃🏻.

        Ina ma'abota son a tallata musu hajojinsu a kafafen yanar gizo suke?.

Tofa kuzo dama ta samu, dan jerin gwanon haziƙan marubanku ƴan biyar sun fiddo muku da hanyar da kuma kasuwancinku zai zagaya lungu da saƙo ta dalilin shafukan littatafai.

Ga duk mai buƙatar a saka masa tallan kayan sana'arsa a shafin littatafan mu na zafafa biyar zai iya tuntuɓar waɗan nan Numbers 0903 234 5899 or 09033181070 ta WhatsApp, idan har agama buks ɗin kana buƙata a sakamaka talla zamu saka maka akan farashi mai sauƙi. Idan kuma wasu adadin pages kake buƙata koda ɗaya ne duk zamu saka maka akan farashi mai sauƙin gaske🤓.

Kuyi maza ku kawo, mai haja shike talla, mai saya kuwa shike neman sauƙi😻😻😄🤗.

______________________

_ZAFAFA BIYAR 2021_*🔥

_*SUKAR BAYA*_💚
_BILLYN ABDUL_
( _kwai cikin qaya_ )
( _raina kama_)
( _wutsiyar raqumi_ )

*_SIRADIN RAYUWA_*💛
_SAFIYYA HUGUMA_
( _alqawarin Allah_ )
( _daurin boye_ )
( _Dangantakar zuci_ )
Chapter 24 · 0% Book details