Sashe 2
Abinda Ke Cikin Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
***
Tun da Safwan ya farka ya ga Sultan sannan Daddy da Mahmah suka tabbatar masa da ya dawo gidan su baki daya sai ya sake, ya hau wasa da tsalle tsallen sa kamar ba mara lafiya ba, Sai kawai suka nemi sallama suka wuce gida.
Tun daga lokacin komai ya sauya a familyn, duk in da kaga Safwan toh zaka ga Sultan, komai tare suke, haka ma iyayen komai tare suke musu dan ko sun so yiwa Safwan shi kadai ba zai yarda ba, sai yace ina na Sultan. Ajinsu daya a makaranta, daya daga cikin manyan makarantun da ake ji dasu a birnin Kano. Haka ma islamiyya komai daya, idan suka dawo daga school zaka samesu a dakin su suna wasa, rayuwar Sultan ta chanja gaba daya, duk Sunday's suna kai ziyara _SMM OPANAGE_ tare da Daddy sai kuma su wuce chan family house din su Daddy din, sai dare suke dawowa.
***Watarana Daddy na zaune bayan ya dawo daga office da yamma aka turo ana sallama dashi, fita yayi ya dan jima sai gashi ya dawo, ya zauna yana kallon Mah-Mah.
"Makocin nan namu ne da suka tare kwanaki ashe Dr ne a Bayero University, shine yazo neman alfarma, wai zai chanja wa yaron sa makaranta yana so yasa shi a ta Sultan sai su dinga tafiya tare, idan matar sa ta kaisu sai ke kuma ki dauko su, ko kuma ke kaiwa ita dauko wa, yace idan har mun amince sai ya turo matar tasa ta shigo ku daidata."
"Ok me kace masa?" Ta tambaya
"Eh nace babu komai amfanin zaman taren kenan, kinga dama muna tunanin neman driver saboda aikin ki da nawa, kinga shikenan idan zamu fita sai mu mika su idan yaso ita tunda yace house wife ce business take a cikin gida sai ta dauko su da yamma."
"Good idea, toh Allah ya bamu ikon sauke nauyin juna."
"Amin."
Yace sai kuma suka shiga hirar iirn halin iyayen dah da yadda ake daukar makoci kamar danuwa amma banda yanzu da komai ya baci, sai ka dade a unguwa ma baka san makocin ka bam
Da yamma kuwa sai ga Matar ta shigo rike da hannun yaron taa wanda yake sa'ansu Safwan din, da fara'ah Mah-Mah ta karbe ta, suka d'an taba hira da tsara yadda zasuyi kafin ta kira yaron nata me suna Adnan da ya shige wajen su Safwan sukayi musu sallama suka tafi.
Tun daga lokacin zumunci me karfi ya kullu tsakanin gidajen biyu, tuni matan suka dinke dan dama Mah-Mah bata da kawa a unguwar, yaran ma ko yaushe suna tare da juna.
***Rayuwa ta cigaba da garawa cikin hukuncin Allah, har zuwa lokacin da yan samarin suke shirye shiryen gama primary school dinsu, a lokacin ne kuma Umman Adnan ta samu ciki, farin cikin da both families din suka shiga ba kadan bane, Safwan, Adnan da Sultan basu da magana da magana sai ta kanwar da za'a haifa musu, Mah-Mah ta kusan fin kowa murna dan yadda take son haihuwa ba'a magana, gashi tun bayan Safwan ko batan wata bata sake ba, shi ma tazo ta haife shi da ciwon zuciya tun ranar da ya iso duniya, ga matsalar numfashi da ta zamar masa asthma, sai ya zama dukkan rayuwar su suna yin ta ne da farin cikin Safwan, duk abinda ya nema in dai be fi karfin su ba suna yi masa, duk da haka basu sangartashi ba. Zuwan Sultan rayuwar su ya kara musu kwanciyar hankali, kadaitar da Safwan yake fama da ita duk ta tafi, hakan yasa Suke son sultan kamar yadda suke son Safwan.
Ranar wata juma'ah Mah-Mah na zaune bayan ta dawo daga aiki da wuri, yaran na daki suna shirya zuwa masallaci da zuwa gidan Hajiya kakar Adnan, kiran Umma ya shigo wayar ta, da sauri ta dauka don tasan haihuwar zata iya tasowa ko yaushe, aiko tana daga wa taji yadda take magana da kyar tayi saurin daukar hijab dinta ta shiga gidan, tana zuwa ta tarar har Umman ta soma shiga cikin mawuyacin hali, a rikice ta kira Daddy ta sanar masa yace gashi nan zai shigo layin nasu, a daidai lokacin kuma Dr ya shigo kamar an jego shi, ya taimaka suka saka ta a Mota, sannan suka barwa Daddy yaran suka tafi.
Isar su asibitin kenan ta sauka, ta haifo kyakkawar yarta cike da koshin lafiya, da sauri Mah-Mah ta dauki waya ta kira Daddy ta fad'a masa, tana jiyo ihun yaran ta wayar lokacin da Daddy yake fad'a musu sunyi kanwa, sai kawai ta kashe ta koma wajen Maijegon!
*_ZAFAFA BIYAR 2021_*🔥
_*SUKAR BAYA*_💚
_BILLYN ABDUL_
( _kwai cikin qaya_ )
( _raina kama_)
( _wutsiyar raqumi_ )
*_SIRADIN RAYUWA_*💛
_SAFIYYA HUGUMA_
( _alqawarin Allah_ )
( _daurin boye_ )
( _Dangantakar zuci_ )
💙
_*KIBIYAR AJALI..*_💜
_MISS XOXO_
(Sulke baya tsare ta sai ta wuce)
( _Igiyar zato_)
( _Kaimin halacci_ )
( _Naufal_ )
*_ABIN DAKE CIKIN ZICIYA_*🧡
_HAFSAT RANO_
( _ruhi daya_ )
( _Sauyin qaddara_ )
( _Daurin goro_ )
*_MIN QALB_*❤️
_MAMUHGEE_
( _buri daya_ )
( _tarayya_ )
( _eznah_ )
Duka BIYAR 5 zaku samesu akan garabasar naira 700 kacal,
Guda hudu 4 Kuma 500,
Guda uku 3 Kuma 450,
Guda biyu 2 Kuma 400,
Guda daya akan 300.
Ma'ana
Each one is 300
2 is 400
3 is 450
4 is 500
5 is 700
Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇
ACCOUNT NO- *0812652655*
ACCOUNT NAME- *HAFSAT LAWAN GAMBO*
BANK NAME: *ACCESS BANK*
saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇
0903 234 5899
IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇
09033181070
Karku Bari ayi Babu ku domin wannnan salon na daban ne
SABUWAR SHEKARA
SABON SALO
TEAM#ZAFAFABIYAR🔥
[3/4, 11:35 PM] Maman Maryam: *_Abinda Ke Cikin Zuciya_*
©®*_Hafsat Rano_*
Amrah (2)
_Wannan littafin na kudi ne, bamu yarda da sharing ba, idan kina bukata ki tuntubi numbobin dake kasan littafin._
***Ganin both uwar da jaririyar lafiya lou suke sai aka sallame su sukayo gida, tun kafin su karaso gida Hajiya ta iso da kayan ta, suna zuwa suka tarar da ita har ta dora ruwan wanka, nan danan gidan ya soma ciki da yan uwa da abokan arziki kowa da son nuna farin cikin sa, kasancewar tun bayan Adnan sai yanzu Allah ya kawo haihuwar yasa kowa yake jin kamar itace ma ta farkon.
Tun da aka kwantar da jaririyar a daki Sultan da Safwan babu wanda ya motsa daga wajen, duk motsin da zatayi suna kallon ta, chan tasa kuka sosai kuka irin na jarirai sabbin haihuwa, da sauri Sultan ya mike ya koma wajen kofa ya tsaya yana rarraba ido cikin yanayin damuwa, kallon sa Umma tayi ta yi murmushi ta cigaba da hada formula saboda rashin ruwan nono, shigowa Mah-Mah tayi dakin ta tsaya da mamaki tace
"Wai dama yaran nan suna makale anan Adnan na chan yana neman su."
Dariya Umma tayi tace
"Suna nan muna jegon tare."
"Lallai kam, toh Hajiya tace an kai ruwan."
Sai ta mike ta bata madarar ta fice ta barsu, hannu Mah-Mah tasa ta kirawo sultan ya dawo ciki suka sata a tsakiyi ta shiga feeding Little angel din da zuwan ta ya zama wani tsani na cikar bururruka da yawa.
Tun daga ranar har zuwa ranar da akayi suna Safwan da Sultan basu bar umma ta huta ba, idan wannan ya dauke ta sai wannan ma yace sai shi, haka zata sa musu ita a kafarsu suyi ta kallon ta suna jin dadi.
Ranar suna taci suna Fatima sunan Hajiyan Dr, a take Mah-Mah tace Amrah zasu dinga ce mata saboda shine sunan da ta jima tana so, umma bata ki ba, tun daga lokacin sai rainin Amrah ya zama tsakanin Hajiya da bata tafi ba da Mah-Mah, idan ta dawo aiki take karban ta ta goye sai ta gaji tayi kuka sannan take bawa sabuwar mai'aikinta ta mika tah. Haka yaran ma suke faman jeka ka dawo tsakanin gidan nasu da gidan su Adnan, duk yadda wataran Adnan yake musu gori akan Kanwar sa ce ba tasu ba basa kin zuwa.
Shekarar Amrah daya cif Umma ta sake haihuwa, sai dai haihuwar tazo da matsala dan sai da akayi mata aiki, sosai ta galabaita saboda haka tun kafin ma su baro asibitin Hajiya ta sa kanwar Umman me suna Safiyya ta hada mata kayan Amrah ta tafi da ita, hakan be wa kowa dadi ba musamman Mah-Mah da yan samarin ta,wanda basu nan ma suna makaranta. Ko da suka dawo suka tarar da abinda ya faru sun nuna bacin ransu sosai, haka dai Mah-Mah tayi ta lallaba su da alkawarin ana yayentan zata dawo nan da sati
Bayan Sati biyu Dr yaje amma sai Hajiya tace a bari Umman ta sake samun karfin jikin ta, ta kuma kula da yar jinjirar me suna Afrah. Haka Dr ya hakura ya dawo gida ya kara bada lokaci Amma sam Hajiya taki.
Ko da lokacin sata a makaranta yayi Dr (Abba) yazo tafiya da ita sai Hajiya ta daka tsalle tace sam tazo kenan, babu yadda Abba ya iya a haka ya sata a makarantar ya kuma samar mata mai adaidaita sahu da yake kaita ya dauko ta kullum, ajinsu daya da Afrah saboda makaranta daya Abban ya sasu, tare suke komai hatta abinci na mutum biyu umma ke zuba musu haka ma Hajiya.
Bangaren Yan samarin kuwa sun kara girma suna aji uku a secondary, sosai shakuwar su da Amrah ta ja baya, sai ya zama idan ba ranar Friday ce tayi ba suka zo gaida Hajiya ba basa ma haduwa.
Amrah bata son mutane shiyasa ko sunzo bata sakewa dasu sai ta makale a gefen Hajiya har su tafi bata musu magana, ita kuwa Afrah sai ta zama me faran faran da surutu ga wayo sosai.