Sashe 73
Abinda Ke Cikin Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Daya bayan daya suka dinga karbar takardar suna dubawa, gashi nan bayanin komai a rubuce ga kuma saka hannun Maimartaba da kansa. Sosai kansu ya daure suka cika da mamakin abinda zai saka Maimartaba murabus ya dora Yarima bayan kowa yasan sarautar itace rayuwar sa.
Babu lokacin bincike ko bin kwakkwafi domin komai da ake bukata Yariman ya gabatar dashi, babu bata lokaci aka shiga bikin nadin sarauta, aka nada Yarima Bilal a matsayin sabon sarkin Masarautar Saji. Mutane da yawa ransu be so ba, musamman da kowa yasan waye Yariman da mugun halin sa, amma basu da bakin magana tunda suka kori Sarki Usman Muhammad Moddibo, shikenan komai ya lalace musu,Komai baya tafiyar musu yadda ya dace, sun dauki hakan a matsayin hakkin da suka dauka na adalin Sarki me son talakawan sa, me dora duk wata bukatar su a saman tasa. Sun jima suna saka ran dawowar shi, har suka hakura suka fitar da rai. Sai gashi yanzu a maimakon su samu chanji me kyau daga mulkin Sarki Bello, sai gashi sun kuma samun wanda yafi shi muni ta kowacce fuska, domin duk mutumin da aka ce mashayin giya ne, toh babu kuma sauran wanda za'a hada shi dashi indai a kima da mutunci ne, domin mashayi babu abinda ba zai iya aikatawa ba.
Bayan an gama nadin ne wasu daga ciki suka bukaci ganin tsohon Sarkin, amma sai Yarima ya nuna musu baya nan wata tafiya me muhimmanci ta taso masa a daren jiya ya tafi, duk da basu yarda da hakan ba, amma babu wanda ya isa ya musa,haka duk suka ja bakin su sukayi shiru dan abinda zai biyo baya ba zai kyau ba.
***
Da k'yar ya tashi yana jin kansa yayi wani irin mugun nauyi, leben sa ya bushe jikin sa yayi wani mugun sakayau kamar wanda aka kwashe masa kayan cikin sa, yunkurawa yayi ya tashi yana tuno abinda ya faru da shi last kafin ya daina gane komai, da sauri ya kalli hannun sa, ya kurawa zoben ido yana kallon yadda yake walwali sosai. Komai da ya faru dashi ya faru ne akan zoben nan, saka shi da yayi a hannun sa shine dalilin da ya sume har ma ya dau tsahon lokaci kafin ya farfado. Be san wanne irin zobe bane haka, amma yana da yakinin akwai wani abu babba game da zoben, wanda yafi tunanin zai iya rusa dukkan Masarautar idan ya fad'a hannun da bai dace ba, tsawon lokacin nan karfin zoben ya ragu ne saboda kasancewar sa a rarrabe, amma yanzu da ya zama a waje daya, be san me zai faru ba kuma, be kuma san wanda zai tambaya ba kuma.
Zagaye dakin ya shiga yi yana tunani abubuwa da yawa, gefe daya kuma zuciyar sa na azalzalarsa da son wani abun da be san menene ba. Jikin window ya matsa ya yaye laluben yana kallon waje, takun tafiyar da yaji yasa shi waigo wa da sauri. Shigar sa ta jiya ta banbanta da ta yanzu, inda yake cikin shigar Saraki, fuskar sa a rufe da rawani, sosai shigar ta burge Sultan a karo na farko a rayuwarsa har yaji yayi sha'awar hakan, kauda tunanin yayi ya fuskance shi ganin yazo daf dashi.
"Idan ka shirya akwai wanda zai maka jagora zuwa hanya, ina fatan zaka cika alkawarin ka na barin Masarautar."
"Ban taba yin alkawari na saba ba, saboda haka bazan fara a yanzu ba."
"Madallah." Yace yana matsawa
"Ba lallai mu sake haduwa ba, saboda sake shigowar ka nan din abu ne me matukar wuya kasancewar yanzu nayi maka nisan da sai dai hange daga nesa, amma ka sani, idan har kayi kokarin yin wani abu, ka tabbata zan maka abinda baka taba zato ba."
"Wannan din gargadi ne ko shawara?" Sultan yayi masa tambayar yana d'age gira.
"Gargadi ne kuma umarni ne daga Maimartaba Sarki Muhammad Bilal Bello Moddibo Saji."
"Maimairta?"
"K'warai, kamar yadda kaji."
Juya maganar Sultan ya soma yi da sauri da sauri a cikin zuciyar sa, kenan Bilal yayi amfani dashi ne wajen samun sarauta, kenan dama shi abinda yake bukata kenan, toh amma mesa be damu da zoben ba shi kamar yadda Madaki ya damu dashi fiye da sarautar?
Zagaye shi yayi ransa na baci ganin yadda yayi wasa dashi
"Kayi amfani dani ka samu sarauta,kana tunanin ka fini wayo kenan? Ko kana tunanin bansan abinda nake ba?"
"Kusan haka ne, duk yadda ka dauke shi toh haka din ne, tunda na har ka yarda nayi Amfani da kai toh kuwa duk ta sigar da ka kira hakan daidai ne."
"Lallai ka tafka babban kuskure."
Sultan yace muryar sa na sake fito da bacin ran da yake ciki sosai.
"Dakata!" Ya daka masa tsawa
"Karka manta da wanda yake gaban ka, bare kace zaka fadi duk maganar da tazo bakin ka, zan iya sa a rufe min ka kare rayuwar ka a kurkuku, dan haka ka iya bakin ka."
Yana kaiwa nan ya fice daga dakin, dafe kai Sultan yayi yana jin kamar ya kurma ihu, anyi amfani dashi wajen sake tura bayin Allah a cikin halin tashin hankali,
"Ya Allah!" Ya furta da karfi yana zubewa a wajen.
"Sarki ya bada umarnin muyi maka rakiya zuwa mararraba." Daya daga ciki yayi maganar, be ce musu komai ba, ya tashi ya tattare komai dinsa ya tura a cikin jakar sa, ya rataya ta suka fito bayan sun rufe shashin gaba daya.
Kai tsaye kofar Masarautar suka nufa, ba tare da ya sake waiwayen komai ba ya fice daga ciki yana ji a ransa zai dawo nan kusa, zai dawo idan ya gama tabbatar wa kansa da shi din waye a Masarautar!
A chan k'asan wata bishiya suka tsaya dashi sannan suka koma, matsawa yayi da sauri jikin bishiyar ganin mutane a zaune.
"Maman Yara?" Ya kira sunan ta, da sauri ta waigo, fuskarta ta fad'ad'a da farin cikin ganin sa.
"Sultan!?".
"Ya akayi kuka zo nan?" Yace yana kallon matar dake kwance akan kafar maman yaran idon ta a rufe tayi masifar ramewa ta d'ashe kamar ma bata da jini.
"Muna kwance cikin dare wasu su biyu suka zo, suka fito damu suka kawo mu nan suka tsaya suna gadin mu har gari ya waye, daf da zaka iso wajen nan suka bar nan."
Shiru Sultan yayi, kenan da gaske Yarima Bilal yake da yace baya bukatar ya sake dawowa, yasan kuma tabbas zai dawo saboda su shiyasa ya fito masa dasu.
"Taimaka mata ku dan matsa bari na samo mota."
Yace kawai ba tare da yace komai akan maganar ba, wayar sa ya ciro ya kunna ta, messages suka fara rige-rigen shigowa, na Madaki da ya shigo karshe ya fara budewa
"Idan ka shirya bani abinda nake so, ni kuma zan baka matar ka, idan kuma ka shirya hanani, ka sani matar ka na hannu na."
"Innalillahi, Amrah!" Ya furta da sauri, ya fita daga kan message din Madakin ya shiga sauran.
*Afrah*
_"Ya Sultan wasu sunzo sun dauke Amrah#Sobs"_
*Safwan*
_"Where are you, wayar ka off, call back ASAP."_
_"Are you ok? Kana ina please ka kunna wayar ka."_
Kasa cigaba da karanta messages din yayi, kafar sa har rawa take ya tafi da sauri ya tsallaka titi, ya tawo da wani me mota, Maman yara ta taimaka aka saka Aminatu a motar, suka dauki hanya yana ta faman kira duk taki shiga. Hankalin sa ya kai kololuwa a tashi, be so Madaki ya saka wani nasa a cikin harkar su ba, ba zai barshi ba wallahi idan har yayi wani foolish abun. Sake ciro wayar yayi ya tura masa message
_"Karka kuskura kayi wani abu, idan har wani abu ya samu iyali na, ba zan barka ba Wallahi."_
Ya tura masa sannan ya sake gwada kiran wayar Safwan, yayi sa'a kuwa ta shiga.
"Hello Sultan, kana ji?"
"Ina ji Safwan, yanzu na ga message dinka..."
"Kana Ina? Wayar ka a kashe."
"Na dan shiga matsala ne,kayi kokarin kwantar wa su Umma hankali, zan dawo da Amrah safe and sound, nayi wannan alkawari, Amma pls ka ji dasu, nasan suna cikin tashin hankali."
"Shikenan, please come back soon, abubuwan sun fara baci, Hajiya ta dora laifin a kanka,Infact ka shiga cikin suspects bayan bayanin da Hajiya ta bayar a station."
"Ya Salam, shikenan Safwan, ka kula da komai, ina hanya da na shigo zan maka waya ka fito mu hadu."
"Owk Allah ya kiyaye."
Ajiyar wayar yayi, ya kwantar da kujerar da yake kai yana kulle idon sa.
ZAFAFA BIYAR
NA KUDI NE:::
Duka BIYAR 5 zaku samesu akan garabasar naira 700 kacal,
Guda hudu 4 Kuma 500,
Guda uku 3 Kuma 450,
Guda biyu 2 Kuma 400,
Guda daya akan 300.
Ma'ana
Each one is 300
2 is 400
3 is 450
4 is 500
5 is 700
Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇
ACCOUNT NO- *0812652655*
ACCOUNT NAME- *HAFSAT LAWAN GAMBO*
BANK NAME: *ACCESS BANK*
saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇
*+234 903 234 5899*
IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇
*09033181070*
Karku Bari ayi Babu ku domin wannnan salon na daban ne
SABUWAR SHEKARA
SABON SALO
TEAM#ZAFAFABIYAR🔥 ©®Hafsat Rano
Page 35
Zafafa Biyar na kud'i ne!
***Kai tsaye asibiti ya wuce dasu, be shiga ba ya kira wani colleague din sa ya had'a shi dasu sannan ya roke shi da aka basu muhimmiyar kulawa musamman dayar matar dan ba karamar jigatuwa tayi ba.
Kiran Safwan yayi, ya fad'a masa inda yake so yazo, cikin kankanin lokaci ya iso tunda dama shi yake jira tun dazun. Da yake a mota yake sai kawai Sultan din ya shiga ba tare da Safwan din ya fito ba, yana shiga ya kwantar da kujerar motar ya jingina da kansa da yake masa masifaffen ciwo ga wani abu me nauyi daya tokare masa makoshi ya hanashi hadiyar yawu.
"Ina ka shiga duk kwanakin nan?"