Sashe 88
Abinda Ke Cikin Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Dama me sultan? Sai bayan da komai ya lalace? Banji dad'i ba gaskia, kuma baka kyauta ba."
"Ayi hakuri Daddy in Sha Allah hakan ba zata sake faruwa."
"Allah yasa..."
"Yanzu ina shi Madakin yake?"
"Yana DSS office."
"Owk." Yayi shiru
Tunanin ta yadda zai masa magana ya shiga yi, shiru kake ji a falon sai karar talabijin din kawai da har sun gama program din da Daddyn yaso kalla. Daurewa Sultan yayi ya kira sunan shi
"Daddy dama akwai wani abun."
"Ina jinka."
"Ranar da naje wajen Madakin nayi masa maganar dan uwan nawa da yake tare dashi wanda binciken da nayi ne ya sa na gane hakan..."
"Ya fad'a maka inda yake.?"
"A ah..."
"Ehen...Nasan ba zai yi saurin fad'a maka ba dama ai."
"Be fad'a min ba, amma sai ya nuna min hoton Ka yace kai ne zaka fad'a min inda yake..."
Da sauri Daddy ya mike
"Hotona... Ni kuma Sultan?"
"Abinda ya saka ni a matukar damuwa kenan, nasan Madaki so yake yayi wasa da hankali na, ban yarda ba ko da ya fad'a ba Wallahi, ban kuma yi maganar ba wai don na tuhume ka, a ah... Ina so na kawai na samu nutsuwar zuciya, nasan idan nazo wajen ka mukayi magana zan ce da gaske Madaki karya yake min, zan kuma san yadda zanyi na cigaba da neman sa."
"Sultan?!" Ya kira sunan sa da karfi
"Kayi hakuri Daddy idan magana ta, ta bata maka rai."
"Ko daya Sultan, ko daya wallahi..." Ya dora
"Be fad'a maka komai akai ba?"
"A ah..."
"Shikenan, ka kaini in da yake na ganshi."
"Ok yanzu ko sai anjima?"
"Yanzu Sultan."
Wayar sa ya ciro yayi dialing number Farouk D abokin nasa da case din ke hannun sa, ya fad'a masa zasu zo tare da Daddy idan zai yiwu su ga Madaki, yace zasu iya zuwa babu matsala. Tashi Daddyn yayi ya shiga ciki ya shirya ya fito suka tafi. Har suka isa babu wanda yayi magana, shi Sultan tunanin abinda zai faru idan sunje din wanda tun daga response din Daddyn ya gane da gaske ya san Madakin, tsoron kar abinda yake tunani ya zama gaske yasa ya kasa yin magana har suka isa. Suka fito suka shiga ciki ta wata kofar baya bayan Farouk D din da kansa ya fito yayi musu jagoranci zuwa ciki. A saman wani benci suka taddashi yana zaune ya juya bayan sa, karasawa Daddy yayi Sultan kuma ya koma da baya ya fita saboda ya basu damar yin magana.
"Madaki."
Daddy ya kira sunan shi, da sauri ya waiwayo, ganin wanda be yi zato ba ya saka shi mikewa fuskarsa dauke da mamaki
"Nasan dama zaka zo!" Yayi maganar yana takowa zuwa wajen sa.
"Menene hadin ka da Sultan?"
"Menene hadin mu dashi dai zaka ce."
"Na zata mun dade da rufe wannan maganar, mesa ka dago ta har kace ya same ni, bayan kasan ba haka mukayi ba, kasan dai akwai sharadin da muka gindaya kafin hakan ta kasance."
"Amma kasan da haka, ka daina daga wayata, ka chanja layi domin kar na neme ka,sannan na kira ka bayan na tura maka message kaki dagawa?"
"Saboda babu abinda yayi saura tsakanin mu." Daddy ya fad'a kai tsaye
"Ina yaron yake?"
"Allah yayi masa rasuwa tun da dadewa."
"What! Haba Sulaiman, kar ka maida ni karamin mutum mana, ya zaka zo min da maganar da hankali ba zai dauka ba."
"Baka yarda da mutuwa ba kenan."
"Ban yarda da wannan din ba dai."
Mikewa Daddy yayi yace
"Ka gaya wa Sultan dan uwan sa Allah yayi masa rasuwa, sannan ka tabbata da ka wanke ni, zanyi kokarin ganin ka bar nan."
Ya juya ya fice yana jin kamar be kyauta ba,amma idan be yi haka ba ya zai yi? Ta ina zai fara ma? Sultan na ganin shi ya taso da sauri.
"Kaje kuyi magana dashi."
Wucewa Sultan yayi shi kuma ya zauna a inda Sulthan din ya tashi.
Yana shiga ya tarar da Madakin ya kifa kansa a kan tafin hannun sa,daga nesa dashi ya tsaya,jin motsin mutum ya saka Madakin dagowa
"Yaushe zaka saka su sallame ni daga nan?"
"Sanda ka shirya fito min da d'an uwana, sanda ka shirya karbar hukuncin mugayen laifukan daka dade kana aikatawa, da kai da duk wani wanda yake da hannu a ciki,kasan kuma su DSS ba kamar sauran police bane balle ka basu cin hanci su sake ka, idan har kaga ka fita daga nan, toh sunyi bincike sun tabbatar da kai din ba mai laifi bane, saboda haka ya rage naka."
"Idan na fad'a maka gaskiya akan maganar dan uwanka zaka saka su barni na tafi?"
"Ina jinka."
_"Bayan Mun baro Masarautar, ina rik'e da yaro daya, safiya tana rike da daya har muka kai gidan dana shirya zata zauna ita da yaran. Na bud'e muka shiga, na nuna mata duk abinda ya kamata ta sani sannan na fita na siyo wa yaran madarar da za'a basu wanda tuni sun fara kuka. Na dawo aka shiga basu Madara, kwana biyu tsakani daya daga cikin yaran ya fara wani irin rashin lafiya,dama chan mun lura da rashin kuzarin sa akan dan uwansa, haka muka tafi muka kaishi asibiti, bayan anyi masa abinda ya kamata likitan hankalin sa ya tashi ganin yaron na dauke da mugun ciwo, ciwon zuciya."_
Wani irin bugawa zuciyar Sultan tayi, irin bugawar da bata taba yi ba, wani irin tsoro ya shige shi, yaji kamar kafar sa zata zame shi ya fad'i a wajen
_Mu kanmu hankalin mu ya tashi, musamman Safiya tunda ita mace ce, kuma gata da tausayi sosai kuma ta kwallafa rai akan yaran. Muka fito bayan likita ya bamu shawarwarin da zai bamu akai, da abinda ya kamata muyi da kuma wani babban likitan zuciya da zai had'a mu dashi. Tafiya muke kowa da abinda yake tunani a tsakanin mu, a lokacin bani da komai sai yan kudaden da basu da yawa, gashi irin wannna ciwon akwai cin kud'i sosai. Wajen zama na nunawa safiya nace ta zauna ta jirani, sannan na koma cikin asibitin ina son nayi wa likitan wata tambaya, ban karasa ba, na hadu da wani mutum a zaune, ya had'a kansa da guiwar sa, daga gani yana cikin tashin hankali mara misaltuwa, dafa shi nayi ya dago da sauri, sai dai yadda idanun sa suka yi masifar ja yasa nayi baya cikin mamakin abinda zai saka shi a wannan halin.
_"Bawan Allah me yake damun ka?"
Nayi masa tambayar ina kallon sa, girgixa kai yayi hawayen dake kwance a cikin idanun sa suka gangaro.
"Subhanallahi." Nace
_"Dan Allah ka fad'a min abinda yake damun ka." Domin ni a tunani na ko kudi aka yanka masa da zai biya a asibitin bashi dasu kuma bashi da hanyar samun su, duk da yanayin shigar sa bata nuna hakan ba. Abinda ya fito daga bakin sa ya bani mamaki matuka
_"Bawan Allah ina cikin gagarumar matsala, bana jin akwai wanda ya kai ni shiga cikin tashin hankali, na kashe d'a na da kaina, d'an da muka dad'e muna addu'ar Allah ya bamu,d'an da muka sameshi bayan tsawon lokaci da muka dauka muna nema, bansani ba, bansan yana ajiye a wajen ba wallahi, na zauna akan jinjirin d'ana da aka haifa yau kwana uku, wanda uwar sa ke cikin halin rai ko mutuwa, duk saboda wahalar haihuwar sa, ya zanyi da raina?"_
"Innalillahi wa Inna ilaihi rajiun, garin yaya bawan Allah?"
"Kaddara! Tsautsayi, bayan yazo duniya ne aka dauke shi aka kaishi nursery inda ake ajiye yara saboda lura da sukayi yasha ruwa wanda ya faru saboda doguwar nakudar da mahaifiyar tayi kafin daga karshe ayi mata aiki a ciro d'an. Ina zaune dazu na dawo daga dubo yaron wanda har ma sun ce gobe zasu bamu yaron saboda ya samu sauki, sai ga kira daga chan nursery din, suna nema na, nayi sauri naje suka bani takarda suka ce naje na siyo wata allura, na tafi naje na siyo na dawo, sai ban ga kowa a cikin wajen ba, sai na shiga kai tsaye da niyyar na jira su, tsautsayi ashe sun ciro shi daga cikin kwalbar da yake sun saka masa kaya, da niyyar su bani shi idan akayi masa allurar sun sallame shi daga nursery din, fita me kula da wajen tayi ta dauko wani abu, ganin ba dadewa zatyi ba yasa ta ajiye shi a kan doguwar kujerar dake ajiye a gefen dakin, ta nannade shi a cikin shawl dinsa, ban sani ba, wallahi ban lura ba ban kuma yi tunanin yana wajen ba, na zauna akan sa."
"Innalillahi wa Inna ilaihi rajiun, Allahu Akbar, gaskiya bawan Allah na tausaya maka, Allah ya jikansa yasa masu ceton mu ne."
"Amin." Ya amsa min cikin yanayi, na danyi jim kad'an sai kuma nayi gaba, har na wuce shi sai na dawo bayan wani tunani ya darsu a raina
"Idan na baka yaro jinjiri haihuwar kwana uku zaka karba?"
A zabure ya dago, ya tashi tsaye da sauri
"Wallahi tallahi zan karba, zan kuma kula dashi tamkar dan cikina, zan bashi ingantacciyar rayuwa nayi maka wannan alkawarin, dan Allah ka taimaka min."
"Yan biyu ne, sai dai an haife shi da ciwon zuciya gashi bani da kud'in da zan iya daukar nauyin ciwon sa, Idan ka yarda zaka kula dashi, za kuma ka bani wasu kudade masu yawa da zan kula da d'an uwansa, nayi maka alkawarin bar maka shi har abadah, na fita daga rayuwar sa ba zaka sake gani na ba kuma."
Da sauri yace
_"Na amince wallahi, ko nawa kake so zan baka."_