Sashe 98
Abinda Ke Cikin Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"You are the best mother in the whole world."
"And You are the best son any one can have."
Sai ta juya da sauri ta bar dakin, ya koma da baya ya zauna dabas a saman kujerar dakin yana tunanin abinda ke shirin faruwa, tabbas akwai abu a zuciyar Mah-Mah da bata so ya sani, ko menene sai ya binciko shi dan hankalin sa ba zai taba kwanciya ba.
Gidansu Mah-Mah ta wuce dan tana bukatar space, space daga wajen Daddy, tana bukatar ta zama ita kad'ai tayi tunanin yadda abubuwan suka zama, ta kuma yi tunanin yadda maganar zata buya ba tare da wasu sun sani ba, son samun ta ba tare da Safwan din ma ya sani ba, duk da a maganar Daddy da yayi mata ya nuna lallai Safwan dole ya sani, amma sam bata yarda ba, bata amince ba domin ko babu komai ita din itace uwar Safwan, dan ta shayar dashi dan haka take jin babu Wanda zai raba ta dashi bayan ta gama wahalarsa.
****Shirye shiryen tafiyar ya kankama, Maimartaba ya riga ya gama shiryawa ranar, ya kuma kudire a ransa ba zai raga ma kowa ba, shiyasa ma yayi komai akan lokaci, ya kuma kira mutumin da yafi yarda dashi akan kowa yanzu, wanda ya hadu dashi lokacin da yake cikin tsananin bukatar wani ya taimaka masa, ba kuma wai da kudi ko wani abu ba, dan zai iya cewa baya jin har ya kare rayuwar sa zai bukaci kudi, domin Allah ya bashi ba kad'an ba, kamfanonin da yake dasu da gidajen mai ba zasu lissafu ba, shi yake kular masa dasu,bai kuma taba samun wani abu a tare dashi ba, tun bayan barin sa k'asar sau biyu suka taba haduwa wanda shi ne yazo wajensa, amma duk da haka suna waya kusan kullum saboda yaji progress din yadda abubuwan suke tafiya, akwai wani kuduri a ransa na mika dukiyar sa zuwa gidajen marayu da masallatai da dai abubuwan da zasu kara nauyin mizanin sa kasancewar bashi da kowa banda gimbiya, sai ga Sultan a lokacin da suka cire rai, wannan ya saka ya chanja shawarar komai ya kuma tsara abinda ya kamata yayi idan sun koma.
Be taba kiran sa be daga ba sai yau, yayi mamaki k'warai da har yayi masa kira uku babu ansa, sai yaji kamar akwai abinda yake faruwa dashi, har la'asar yana jiran kiran sa amma be kira din ba, ya sake gwadawa amma yanzu sai akace masa switch off, yayi mamaki sosai amma sai ya bar hakan a matsayin wani abu ne ya samu wayar tasa.
Yana kishingid'e suka fito zasu fita, Sultan ne a gaba Amrah na binsa a baya, kafin su karaso wajen sai da suka tsaya a dan corridor din ya taimaka mata ta gyara zip dinta wanda bata san be kai chan sama ba, ya mintsine ta bayan ya gyara matan tayi yar kara ta kai hannu yayi saurin gocewa ya shigo falon yana kunshe dariyar sa.
A kusa da Maimartaba ya zauna, ya dora hannun sa a saman kansa yayi addu'a, hakan cikin al'adar Maimartaba ce wanda yake saka Sultan a cikin matukar farin ciki.
"Sannu da hutawa Babah."
"Yawwa Muhammad, fita zakuyi ne?".
"Eh wai chan gidan zamu je akwai mutanen da zata wajen su."
"Ya kamata, yaki 'yata."
Matsawa Amrah tayi gabansa suka sashi a gaba ita da Sultan din, ya dora hannun sa a saman kanta itama yayi mata addu'ar sannan ya saka musu albarka baki daya, sallama sukayi masa suka fita, ya bisu da kallo yana sauke ajiyar zuciya.
A baya suka zauna, ya cire pad dinsa ya shiga dannawa,lokaci zuwa lokaci yana kallon titi, har suka iso inda zasu, be dago ba yace mata zai danje wani waje ya dawo,fita tayi tana gyara zaman rolling din kanta, suka ja motar suka tafi, a hankali ta taka zuwa gidan, ta danna door bell ta tsaya tana kallon hanyar da motar tabi, me yasa yake acting haka? Yanzu zai yi wasa yanzu zai yi kamar baya wajen. "Sarauta" zuciyar ta, ta tunasar da ita, jijjiga kai tayi kawai ita sam bata son wannan side din nashi, tafi son yayi ta tsokanar ta, tana jin dadin haka, bud'e kofar da akayi ne yasa ta maida hankalin ta kài, malamar su ce da ta koya musu karatu, wadda zata iya cewa tafi kowa kusanci dasu a k'asar tunda ba wani harka sukayi sosai da mutanen ba, ganin Amrah yasa ta saurin rungume ta,
"La'ila, da gaske wai ko da wasa?"
"Anty..."
"Shigo ciki." Ta matsa mata tana fad'ad'a fuskar ta, gefe Amrah tabi ta shiga falon,
"Bismillah." Ta nuna mata wajen zama,zama tayi ita kuma ta nufi kitchen, ta hado mata ruwa da lemo da snacks akan tray ta kawo mata, sannan ta zauna suka gaisa
"Yaushe kuka zo?" Ta tambaye ta
"Ranar Wednesday."
"Yasu Umma da kowa da kowa? Ke kad'ai kika zo Ina Afrah da Abba?"
"Suna Nigeria."
"Ke kad'ai kika zo kenan?"
"Ni da shi muka zo, tare ma muka zo har kofar gidan nan ya wuce wani wajen."
"Adnan?"
"A ah, Ya Sultan."
"Dan Allah, amma shine be shigo ba. Wani abun kuka zo kenan."
"Umm..." Amrah tace ganin yadda Aunty Muhsinan ke mata tambayar kwakwa alamun tana son taji wani abu, ba zata iya ce mata ai tayi aure ba, sai kawai ta share suka cigaba da hirar abubuwan da suka faru bayan barin su garin.
Har azahar suna tare, yau kasancewar babu karatu yasa gidan babu kowa yaranta ma suna chan gidan In-laws dinta, duk motsin ta Amrah na lura da komai, yadda take gudanar da gidan ta cikin kwarewa da iyawa. Har la'asar tana gidan be dawo ba be kuma kirata yace gashi nan ba, ita kuma maimakon ta kirashi sai ta share duk kuwa lokaci zuwa lokaci sai ta duba wayar taga ko ya kira, Anty Muhsina na lura da ita, bayan sun yi sallah ne sai ta karbi wayar Amrah tace zata ga hoton su Ummah a Nigeria, bude mata Amrah tayi ta bata ta shiga kalla har tazo inda take zargi, hotunan bikin Amrah din, tayi saurin cewa
"Tunani na dai ya zama gaskiya, ashe Amrah anyi biki, shine ko ki fad'a min tun dazu da kika zo nayi noticing naki."
Da sauri Amrah ta rufe fuskarta ta saka dariya, ajiye wayar tayi ta dawo kusa da ita,
"Bude fuskarki, ba wai iya kar karatu kawai nake koyawa ba, har da yadda zaki zauna lafiya da mijinki, feel free with me karki ji nauyin komai, wannan rayuwar idan kika tsaya kunya za'a yi babu ke, so ki ajiye wannan kunyar a side, duk kuwa da kunya adon mace ce, amma akwai limit."
Shiru Amrah tayi amma dai ta bud'e fuskar tata, tayi zuguri tana sauraron ta.
"Da farko sai kin zama me tsafta, Idan nace tsafta ina nufin tsafta ba wai kawai shara ba, you have to be neat in and out, jikin ki, gidan ki have to be very tidy shine first step, sai kamshi, kamshi rahma me, kamshi yayi Amrah, ke kanki idan kina kamshi zaki dinga jin ki different balle kuma wanda kike tare dashi, gidan ki ya zama yana kamshi always, safe rana turaren nan babu kiwa, dama bangaren kirki na baki lambar yabo har ma da gyaran amma dole ki kara himma kinji? Karki yi wasa yawwa."
"Know what your husband wants, like and dislike, akwai banbancin tsanaki abinda yake so da kuma abinda yake bukata kin gane? Ki san kuma kowanne da lokacin da yake bukatar tasa, sai ki san abinda ya dace kiyi, kisan damuwar mijinki, ki san yadda zaki magance masa ita, ki zama abokiyar shawarar sa, ki dinga bashi shawarwari idan abu ya taso, ki zama me gyara shinfida ki kin gane me nake nufi, ki zama available duk sanda mijinki ya zo da bukatar sa ."
"Kisan lokacin da yake in the mood, da lokacin da yake bukatar zama shi kad'ai, karki ce dole dole sai ko yaushe ya zama yadda yake, akwai damuwa akwai gajiya akwai matsalolin yau da kullum."
"Ki zama me iya magana, ba kowanne magana zaki iya budar baki ki fadawa mijinki ba, daga lokacin da kike fad'a masa kowacce magana shima ba zai ji kunyar Yaba miki duk wadda tazo bakin sa ba duk kuwa da munin ta, ko matsala kuka samu yayi miki laifi talk to him politely, shine zai fi fuskantar ki har ma kuyi solving matsalar ku ba tare da 3rd party ko hayaniya ba,amma idan kikace zakiyi masa gyara da tashin hankali toh ba zai dauki gyaran naki ba, kuma ba zai tsaya ya saurare ki bama."
"Mata muna da mood swings na yarda da wannan, saboda haka kiyi iyakar kokarin ki wajen daidaita fushin ki ko bacin ranki, saboda mata da yawa mood swing din da muke samu na taka muhimmiyar rawa wajen wasu manyan matsalolin da aure ke fuskanta a yanzu."
"Ki zama me godia, mijinki ko kayan abincin gida ya siyo learn to appreciate him, kiyi masa addu'ar karuwar samu suna jin dad'i sosai da sosai."
"Ki iya hira, ba wadda zata dinga gundurar sa ba, ba kuma gulma ba, yau kice wannan gobe kice wance, zaki ga ba zai wani dinga baki attention ba idan kinayi, kisan me zaki fad'a game da yan uwanki da iyayenki dan wasu mazan will use that against you musamman idan Abu ya taso ko kuka samu matsala."
"Ki koyi sana'ah idan mijinki zai kyale ki, yanzu ba'a zama saboda yawancin maza basa son bani,bayan haka kuma abubuwan na yi musu yawa dan haka idan kina sana'a zaki taimaka ta wanne bangaren."
"Amrah wasu Mazan na da rauni wajen ibadah, sai kun hada karfi wajen gyara gidan ku, kin taiamaka masa wajen tsaida ibadun sa, sannan zaku samu nagartaccen gida. Kiyi addu'a sosai ki kuma lura da komai, karki zama ballazar mace, ki zama mace me aji me class, al-mar'atu saliha."
"Inaga with this little advise, da kula da dangin sa da iyayensa da ban saka ba, da wasu abubuwan da na manta ina fatan zaki yi amfani dasu, ina yi miki fatan alkhairi a sabuwar rayuwarki, ina rokon Allah ya baku zaman lafiya da zuri'ah dayyiba, ya albarkaci auren ku."