Sashe 83
Abinda Ke Cikin Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
***Sai da suka tabbatar da babu wani abu apart from ciwon jikin sa wajen da bullet din ya shiga, heartbeat din sa ta dawo daidai he's stable, dan har ya bud'e idon sa ya kuma yi magana da SULTAN duk da ba me tsaye bace. Murnar da Sultan yake ciki fad'a ma bata baki ne, har tsokanar sa su Dr Labaran sukayi, yayi dariya kawai dan yasan duk bayanin da zai musu akan waye Safwan a wajen sa ma bata baki ne, shiyasa kawai yayi dariyar ya cigaba da mika godiyar sa ga Allah da be dauke Safwan a lokacin da yafi ko yaushe bukatar sa ba, lokacin da shima zai ji dadin Sultan din fiye da kowanne lokaci.
Sallama sukayi masa suka bashi sauran abubuwan da Safwan din zai bukata, ya matsa ta side din kansa murmushi kwance a fuskar sa, duk a lokacin ya koma bacci amma bacci ne wannan normal kamar wanda kowa ma yake yi, ba kamar wanchan da ba zaka tantance wanne hali mutum yake ciki ba.
Fitowa yayi su Mah-Mah da sauran yan uwa suka dunguma suka shiga,bai koma ba sai kawai ya nufi gate din asibitin a kafa, ya tsallaka titi kai tsaye wajen wasu mutane masu neman taimako yaje, ya rarraba musu kud'i sukayi ta murna suna sa masa albarka, sannan ya koma ciki ma yabi wasu dakunan ya basu kud'in. Yana cikin wannan zagayen ne ya tuna da su Maman Yara duk da ba wai ya manta dasu bane, amma ya kamata ace ya koma ya gansu. Abubuwan ne da yawa sosai, shiyasa shaf ya manta sai yanzu. Da sauri ya nufi bangaren nasu, sai dai kafin ya karasa suka hadu da Muhammad a hanya.
"Muhammad?" Ya tambaya yana son tabbatar wa
"Eh nine." Ya amsa yana daga kai
Hannu ya bashi suka gaisa sannan yace
"Ina ka shiga tun ranar ban sake ganin ka ba?"
"Gida na wuce bayan sun dauki statement dina, shine yau na dawo na sake duba jikin nasu, ina fatan da sauki?"
"Alhamdulillah wallahi, da sauki."
"Allah ya kara sauki. "
"Muje daga chan muyi magana please idan babu damuwa." Sultan yace yana nuna masa wasu kujeru daga gefe,
"Ok." Suka nufi wajen, suka zauna sannan Sultan yace
"Dan Allah Muhammad tambayar ka zan, ina fatan zaka fad'a min gaskiyar komai, da farko na taba ganin ka a gidan Safiyanu Madaki, duk da ba wai munyi magana bane na zo fita kai kuma kun shigo, ba lallai ma idan kun lura dani ba, amma ni na ganku,sai kuma abinda ya kai ka wajen nan har ka taimakawa Amrah, menene hadin ka da mutum irin Madaki?"
Shiru Muhammad yayi, ya shiga tunanin ya fad'a masa ko kuma kar ya fad'a masa? Ya kamata kuwa ya yarda dashi haduwa daya? Idan kuma shi dinma yana da alaka da Madakin ko kuma shi din ba abin yarda bane? Toh amma kuma be yi kama da mutum mugu ko macuci ba, bisa abinda ya faru ma kamar dai shi din ma wani abu Madakin ya yi masa, ko kuma wani abu ya nema a wajen sa. Sake kallon Sultan din yayi, kaso mafi rinjaye na zuciyar shi na yarda dashi, yarda irin wadda zaka bawa mutumin da ka gama sanin halin sa, girma da kimar Sultan din cike da wani irin kwarjini da haiba ya saka babu wani bata lokaci ya budewa Sultan din komai, har zuwa lokacin da aka tafi da Ammi da abubuwan da suka faru bayan nan. Zumbur Sultan ya mike, ya kama hannun Muhammad din ya mika dashi yace
"Yanzu baka san inda ita Ammin take ba?" Girgiza masa kai yayi
"Abinda naje nema kenan, sai kuma nayi rashin sa'a, ba ita bace a wajen matar ka ce."
"Ya sunan Ammin na gaskiya?"
"Safiyya!"
"Kai kad'ai ne ko kuma ku biyu ne?"
"Ni da kanwata ne Aysha."
"Aysha? Mace kenan? Kanwar ka? Ko kuma..."
"Kanwata ce."
"Ok Ammi bata taba ce maka kai din yan..."
"Ta fad'a min, ranar da wasu yan biyu masu kama daya suka zo wajen matar da muke gida daya dasu, shine Ammi take cewa ai ni ma yan biyu ne, amma bama kama mu."
"Ina dayan?"
"Bata ban amsa ta ba a lokacin dana tambaye ta, sai kawai tace min ba yanzu ba."
Shiru Sultan yayi yana tattara bayanan yana kuma jin tabbas matar nan da Maman Yara ta fad'a masa da k'yar idan ma ba ita ce ba,
"In Sha Allah Ammi zata dawo cikin koshin lafiya, karka damu zan taimaka maka." Ya dafa kafad'ar sa cikin son kara masa k'warin guiwa.
"Nagode sosai."
"Karka damu, samin number wayar ka in case ko zan neme ka" Ya mika masa wayar sa, ya saka masa ya kirashi shina ya ga tasa yayi saving sannan suka yi sallama ya tafi shi kuma ya karasa dakin da su Maman Yara suke.
"SULTAN!" Ta taso da sauri ta rik'e masa hannu, durkusawa yayi ya gaishe ta, bata amsa ba ta zura masa ido ganin muguwar ramar da yayi
"Me yake damun ka?" Tace tana taba saman kansa
"Zazzabi na danyi ne kwana biyu, shiyasa ma ban shigo ba, ya jikin naki?"
"Ayya sannu Allah ya kara sauki, gashi nan duk ka rame wallahi, ni kalau nake Aminatu ce dama itama gashi nan ta dàwo hayyacin ta, dama wahala ce da rashin kula.".
"Sannu kaji? Allah ya kara sauki."
"Ina wuni?" Ya dan rissina ya gaishe ta, bata iya amsawa a haka ba, ta sauko kanta na k'asa sosai ta gaishe shi cike da mutuntawa, sosai hakan yasa shi jin babu dadi ganin Babbar mace na durkusa masa,
"Kice dan Allah ta daina durkusa min, ina jin kunya Wallahi?" Ya fadawa Maman Yara yana chanja fuskar sa zuwa kalar rashin jin dad'i
"Tana da dalilin ta babba nayin haka, hakan kuma shine ka'idar gidan sarauta, dole ta girmama ka a matsayin ka na Yarima, kuma sarkin gobe da yardar Allah."
Wani irin banbarakwai SULTAN yaji, ya kasa cewa komai kawai ya shiga hasaso kansa a matsayin jinin sarauta, wadda be taba tunani ko hasashen zama cikin ta ba, ta ina ma zai fara idan har abinda Maman Yara ta fad'a ya tabbata? Kamar tasan zancen da yake kenan a zuciyar shi sai ji yayi tace
"Idan har lokacin da duk muke jira yayi, zaka gane abinda nake fad'a maka, gado ba karambani bane Sultan, dole ne zaka iya, domin ko a yanzu ka tabbata jinin sarauta, tun yanayin tafiyar ka da yanayin komai naka cike da nutsuwa babu baragada, lallai za'a yi gagarumin Sarki wanda baa taba yin irin sa ba a kaf tarihin Masarautar Saji."
Murmushi kawai Sulthan yayi, bashi da abin fad'a, idan ma akwai toh be san me zai ce ba, sai kawai ya matsa gaban inda Aminatu take, yace
"Ya sunan matar da ake tunanin itace ta karbi yaran?"
"Safiyya." Maman Yara ta amsa duk da ba da ita yake ba, juyowa yayi yace
"Ina
***
Kusan kwana uku kenan yana neman number Sultan din amma bata shiga,duk sun damu saboda sun jima rabon da suyi magana dashi, ranar bayan ya gama duk abubuwan da ya saba, ya sake gwada kiran, sai gashi ta shiga, yayi saurin saka ta a kunnen sa, yana addu'ar Allah yasa ya d'aga, kafin ya gama addu'ar yaji an daga, cikin nutsuwar sa yayi sallama
"Babah." Ya kira sunan shi kamar kowanne lokaci, daya daga cikin abinda yake kara masa jin Sulthan din a cikin ransa shine kiran sa da lakanin Baba, ya kan ji dad'i mara misaltuwa
"Muhammad! Ina ka shiga kai kuwa, ka bar Babanka cikin tunani."
Sauke ajiyar zuciya Sultan din yayi yana jin wani irin peace of mind, yana jin cewa wannan din da yake magana dashi shine mahaifin sa, ya kuwa zai ji idan ya samu labarin? Yasan zasuyi farin ciki mara misaltuwa, kamar yadda shi ma yayi,Allah ne ya had'a su ba tare da sun san alakar su ba, ya kuma jefa kaunar junan su a tsakanin su, tabbas babu tantama su din iyayen sa ne, saboda yadda yake ji game dasu be taba jin irin sa akan wasu ba, ko da kuwa Daddy ne da Mah-Mah.
"Ina neman afuwa Baba, ban yi hakan da gangan ba, sai don wata matsala da ta taso min."
"Matsala Muhammad? Wacce irin matsala ce?"
"Ba wata Babba bace, amma zanzo kwanan nan, zanzo na ganku."
"Zaka zo da gaske, kai Masha Allah,wannan labarin nasan zai faranta ran gimbiya,nasan zata yi matukar farin ciki."
"Tana kusa?"
"A ah amma bari na kai mata."
"A ah Baba, da kanka? Zan sake kira anjima dai."
"Toh shikenan."
"Ya kafar? Tayi sauki?"
"Kafa tayi sauki sosai sai godiyar Allah, ciwo kamar cirar k'aya wallahi, Allah dai ya kara mana lafiya."
"Amin Baba."
"Karka manta ka kira fa, karka manta."
"Ba zan manta ba in Sha Allah."
"Allah yayi maka albarka, sai ka kira."
"Amin ya Allah."
Cire wayar yayi,yana jin farin ciki na lullube shi,
"Alhamdulillah ya Allah." Ya furta a hankali sannan kai tsaye ya wuce dakin da Safwan yake yana fatan ya farka daga baccin da yake. Sai dai be same shi ido biyu ba, sai Mah-Mah kawai a dakin da Anty Amina Maman Umaimah, gaishe su yayi ya juya ya rufo musu kofar. Yana so yaje ya duba Amrah amma kuma yasan dakin da mutane, tunda dazu ya wuce yaga alamun akwai mutane. Amma kuma ya kamata yaje ya duba tan, haka zai daure yaje din baya son yadda kowa ke ficewa Idan yaje din ne shiyasa baya sakewa yayi ta xuwa din amma tana makale da tunanin sa ko yaushe.
Yau be tsaya ba kamar wanchan lokacin, yayi sallama aka amsa sai kawai ya shiga, duk suka yi saurin tashi, Umma ma ta tashi da sauri yace
"Dan Allah umma ba sai kun fita ba."
Duk da haka babu wanda ya tsaya din, suka gaisa da Umma da sauran duk suka fice yaji duk kunya ta kamashi musamman saboda abinda Hajiya tace da tazo fita
"Munafurci wai kar a fita, mu babu kalar munafurcin mata da miji da bamu sani ba ehe."