Sashe 101
Abinda Ke Cikin Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sati guda suka kara a k'asar suka shirya tahowa inda suka yanke shawarar fara ziyartar dakin Allah su yi addu'a sannan su tafi., daga Gimbiyar har Maimartaban wani irin yanayi suke jin su, zasu tafi k'asar su abinda suka riga suka cire rai ma akai.
A chaan Masarauta kam suna cikin farin ciki, saboda labarin da Buzu yazo musu dashi na cewa lallai Ahalin Usman basu isa su tako kafarsu su shigo ba, ya kuma basu tabbacin anyi aiki sosai akan hakan,wannan ya kwantar da hankalin su ainun, suka shiga farin ciki da murna, har da had'a wata gagarumar walima akaci aka sha akayi hani'an sannan kowa ya kama gabansa a matsayar ranar da suka zaba zasu hadu dukkan su.
Yarima Bilal ko nace Sarki Bilal dai yadda zaku fi ganewa na kurbar tagomashin mulki,mulkin da zuba masa ido kawai sukayi zuwa lokacin da komai zai daidaita,shi a haukan ma gani yake kamar wai tsoron sa ne ya hana su tankawar, be san duk cikin su babu me raga masa, don ma ana ganin idon mahaifin sa shiyasa har suka kyaleshi ya kai wannan lokacin.
***Tun da suka ha wo jirgi sai jikin su ya kara sanyi, da wani irin tsoro tsoron abinda zasu je su tarar, amma sai zuwan su saudiyya ya rage musu kaso mafi rinjaye na cikin zulumin da suke ciki.
A wani babban hotel suka sauka nan kusa da harami, suka dukufa ibadah babu dare babu rana, aikuwa sunji dadin kwanakin nan fiye da tunani har suka dinga jin kamar babu wani abu a gaban su da suke shirin tunkara.
A dan zaman da su kayi a kasar sukayi sabo da wata mata yar k'asar Sudan da take zaune a k'asar me suna Hafsah, anan ta basu sirrukan turare da gyaran jiki, babu kunya Ummi ta saka Amrah a gaba sai da ta koyi komai a cewar ta wai su sun tsufa Amrah kuwa yarinya ce, chan k'asan zuciyar ta kuma ta nayi ne domin farin cikin Sultan.
Ko da suka zo tafiya sai da sukayi kuka, musamman Amrah da suka yi masifaffen sabo da Hafsah tare suke zuwa duk inda zasu tsawon kwanakin nan, tayi musu hidima sosai shiyasa da suka zo tafiya suka ji duk babu dad'i, amma a haka suka hakura dan tafiyar su ta zama dole. Ta kuwa had'a musu sha tara ta arziki musamman kayan gyara da hadaddun turarurruka na jiki da na gida.
***Kana ganin shirin da Daddy yayi kasan ko ba'a fad'a maka ba, mutanen da zai hadu dasu yau masu matukar muhimmanci ne a wajen sa, duk da tun ranar da sukayi maganar nan da Mah-Mah bata sake ko da kallon sa bane balle tayi masa magana, musamman da ta nuna masa zasu iya cigaba da boyewa ba sai Safwan din ya sani ba ko dangi, amma yaki yace ko da hakan shine last abu da zai yi dole ne, ba wai don baya son Safwan ba, sai dan sanin su waye tsatson Safwan din.
Da zai fita kamar ko yaushe sai da yayi mata sallama, ta amsa a ciki, ya girgiza kai kawai har yaje kofa sai kuma yace
"Yau muna da manyan baki, bawan ALLAH da nake kulawar wa da dukiya da gidan marayun sa yana hanyar sauka a k'asar sa, sannan kinga su Sultan ma suna hanya, sai ayi abinda ya dace."
Bata ce komai ba har ya fita, haka kawai sai taji duk wani iri, taji kamar zuwan nasu zai taso wani abu ne musamman da yace mata Sultan ma suna hanya tasan kuma dole ne idan tare suke cikin jirgi daya da bawan Allahn nan toh kuwa tabbas tare zasu sauka, kuma dai tare zasu iso gida tunda dole ne Sultan ya biyo Daddy su tawo. Daga nan kuma tasan da SULTAN din ya dawo za'a tada zancen Safwan dinta, shiyasa labarin zuwan nasu be mata dad'i ba, amma kuma tuna girma da martabar da bawan Allah nan yake dashi a wajen su, dole ne tayi wani abu, ko dan halacci da yayi musu da karamci.
Kamar ba zata tashi ba sai kuma ta mik'e tana kwala kiran mai aikinta Fati, da sauri ta shigo ta kofar kitchen hannun ta rike da duster,
"Gani Hajiya." Ta dire akan kafarta
"Akwai baki, muna da snacks din nan da yawa ko?"
"Eh akwai jiya ma bayan kin shiga daki Maman su Afrah ta aiko da wasu."
"Ok Allah sarki bata gajiya, toh ayi warming din su sai a dora abinci, zanzo na saka hannu amma ki dora ruwan abincin."
Juyawa tayi bayan ta amsa ta wuce ciki, kaya Mah-Mah taje ta chanja ta dawo kitchen din tana tunanin abinda ya kamata a tanadar musu.
Har suka kammala komai wajen karfe ukun rana basu karaso ba, duk da dama Mah-Mah ba wai tasan lokacin saukar tasu bane amma kuma bata dauka zasu dauki lokaci haka ba, dakin Safwan ta nufa ta tarar a rufe, tasan shima inda yayi baya wuce airport din duk da be taba fita ba tun da aka sallame shi sai yau din, ta kuma san da k'yar idan bashi da Adnan bane kila har da Afrah ma suka tafi, komawa tayi ciki tayi kwanciyar ta bayan ta saka an kunna turaren wuta a babban falon da Daddy ke ajiye manyan bakin sa.
A chan airport abun da ya faru yayi matukar daurewa Daddy, da Maimartaba rai, har da Sultan ma da be yi tunanin akwai wata alaka tsakanin su ba amma kuma sai yaga akasin abinda yayi tunani, tabbas Daddy tarar su Babah yazo airport din tunda shi dai basuyi magana ba bayan wadda sukayi ya fad'a masa ranar da zasu iso k'asar. Shi kansa Daddy ya shiga mamakin ganin Sultan din da kuma Maimartaba a tare, ga dukkan alamu ma tare suke, duk da iya kar dadewar da sukayi suna mu'amula da Maimartaban daidai da rana daya be taba sanin shi waye ba, be taba tambayar sa akam rayuwar sa ba, amma kuma a yadda ya gansu da Sultan da yadda yaga koman su tare sai yaji ya sake sinkewa da lamari, kenan bawan Allah nan da bashi da kamar sa a kaf Duniya shine mahaifin yaran sa Sultan da Safwan? Ko kuwa Yaya?
Isowar su Safwan wajen ya saka SULTAN jin wani iri, ya kama hannun Safwan ya jawo shi har gaban Maimartaba, yayi k'asa da kansa, da sauri Safwan ya durkusa har k'asa ya gaida mutumin da yaji wani irin kwarjinin sa ya kamashi, hakan da Sultan yayi yasa Maimartaba gane waye Safwan, ya kafe shi da ido kwalla na taruwa a kurmin idon sa, Allah hakim, shine yake tsara komai a yadda yaso, a kuma san da yaso, hannun Safwan din ya kama ya mikar dashi,ba tare da yace komai ba ya jawo shi jikin shi ya rungume yana jin kaunar shi na kama shi, kauna irin ta d'a da mahaifi wadda bab irin ta a kaf duniyar nan.
Wani irin abu ne ya daki Daddy, da ya gama fahimtar komai cikin dan kankanin lokaci, wannan bawan Allah, shine mahaifin Sultan da Safwan, kuma shine wanda ya jima be ga mutum me karamci da dattakon sa ba,kuma shine tsohon Sarkin Masarautar Saji wanda a lokacin labarin abinda ya faru dashi ya zagaye ko ina a fadin k'asar.
Sai yaji ya sake masa girma a ido, ya cika wajen gaba d'aya, cikar kamalar sa abun kallo ce, sai abu daya da ya lura dashi ta farat daya, komai nasa irin na Sultan ne hatta da yanayin tsaiwar da yayi, yadda yake magana a nutse da kuma yadda yake murmushin sa, duk na Sultan ne, hankalin sa ya maida wajen gimbiya, wadda ya tuna ta, itace dai wadda suke tare a wanchan lokacin, sai girma da ya sake nunawa a tare da ita akan wanchan lokacin, sai yaji wani irin tausayin ta,shigen wanda yaji a lokacin da basu da d'a, ita kuma da aka raba ta da nata fa? Ya taji kenan? Lallai tayi tawakkali fiye da shi wanda yayi a lokacin da ya tabbatar da ya rasa nasa, ya k'asa hakuri ya godewa Allah wanda dama shine ya bashi ya kuma karbe, amma sai yabi son zuciyar sa yayi abinda ayanzu zai zamar masa abinda zai dame shi ya hana shi sukuni. Duk da yasan be cuci daya daga cikin su ba, daga Sultan din da suka same shi daga sama har Safwan din da suka same shi tun yana summa, yasan yayi musu rikon da duk wani uba zai wa dan sa, ya kuma san sun chanchanci zama iyayen Safwan na gaskiya ko da basu haife shi ba, ko dan shayar dashi da Mah-Mah tayi. Amma kuma ba zai taba hana iyayen sa na asali suma su ji dadin dansu ba, dan su suka ma fisu bukatar shi.
Har aka shiga motar, aka kuma dauki hanyar gida Daddy be dawo daga tunanin da ya tafi ba, wanda a daidai lokacin shima Sultan ya shiga tunanin alakar Daddyn da Maimartaba, sai da suka kusa isa gida Sultan da yake zaune a gefen Safwan da yake tuka motar, inda Ummi da Amrah da Afrah suke a a baya, ya ciro wayar sa ya kira Adnan, sukayi magana sannan ya kashe ya jingina kansa da jikin kujerar ya fad'a tunani. Yana so ayi komai a gama dan haka ne ma ya saka Adnan yaje ya dauko Maman Yara da Aminatu ya kuma tawo da Muhammad da Aysha zuwa gobe idan Allah ya kaimu ayi komai saboda yafi so su isa Masarautar Saji da karfin su.
***Nagode sosai da sakonnin ku, naji dad'i Allah saka da alkhairi, na samu sauki sai abinda ba za'a rasa ba. Masu korafi ban yi niyyar magana ba, amma duk wanda kaj ance bashi da lafiya toh fa bashi da lafiyar ne domin ba'a karya da ciwo, kwanana hudu kenan ana min karin ruwa (drip)har leda goma. Dole mutum ba zai samu lokacin kansa ba ballantana rubutu, shi rubutu dan nutsuwa ne, idan baka da nutsuwa ba zaka iya ba. Ina neman alfarmar zan dinga fashin kwana daya daya har muka abinda Allah zai yi. Nagode sosai Allah ya bamu lafiya baki d'aya.[7/6, 10:00 PM] Maman Maryam: ©® Hafsat Rano
*Page 55*