← Book details Abinda Ke Cikin Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 97 OF 108

Sashe 97

Abinda Ke Cikin Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Alhamdulillah, ko da yake kar Safwan yayi ta jiran abincin, muje akai masa idan yaso da daddare sai muyi maganar."

"Owk tam shikenan."

Asibitin suka nufa, suka tarar da Safwan din a zaune ma suna hira da wani abokin karatun sa, ya gaida su yayi musu sallama ya tafi, tare suka zauna suka ci abincin a kwano daya, duk da Daddy be wani ci sosai ba amma still yaci don kar ya saka Mah-Mah a tunani tunda ta riga ta sanshi tasan abinda yake hanashi sukuni har yaki cin abinci ba karami bane. Har dare suna nan, sai da wanda zai kwana a asibitin wani dan sister din Mah-Mah yazo sannan suka tafi gida.
A gajiya Mah-Mah take, tayi saurin wucewa dakin ta, ta kwanta saboda yadda take jin ta babu dad'i, tana kwance bacci ya soma daukar ta, Daddy ya turo dakin ya shigo, ya kalle ta cike da tausayawa, ya matsa gaban gadon ya zauna ya bata baya. Motsin sa yasa ta tashi ta zauna.

"Bansan me yasa ba nake jin duk babu dad'i, baccin ma sama sama yake daukata ko me yasa?"

"Zamu iya yin maganar yanzu?"

"Ya Salam, kaga har na manta zamuyi magana,Allah ya yaye min mantuwar nan tawa."

Shiru yayi yana harhada maganar, ya hada ta yafi sau goma tana kwacewa, har ta kosa tayi tunanin ba zai ce komai ba, sai kuma yace

"Da farko ina so na fara da baki hakuri, tabbas nayi miki laifi me girma, amma dan Allah ina rokon da ki yafe min."

"Iya zama na da kai ban taba samun ka da wani abu ba, kullum burin ka shine ka faranta min, ni kuwa me zakayi min har haka da zaka nemi yafiya ta?"

"Tabbas nayi amfani da kokari na faranta miki,wajen bata komai, amma sai dai banyi dan nasan gaba zai zama abinda zai goge duk farin cikin da na samar miki ba, idona ya rufe a lokacin buri na, na samu yadda zan faranta mikin, bansan cewa akwai gaba ba, dole komai daren dadewa gaskiya zatayi halin ta."

"Dan Allah Daddy ka fad'a min me ya faru? Aure kayi baka fad'a min ba? Kana da wata matar saboda ta haifa ma yara ko?"

Girgiza kai yayi da sauri

"Idan wannan ne zai fi min sauki ai."

"Toh menene, dan Allah ka fad'a min."

Juyowa yayi gaba daya, ya kama hannun ta ya rik'e sannan ya saukar da kansa k'asa sosai

"Kiyi hakuri,kiyi hakuri,Safwan ba dan mu bane!"

_"Safwan ba d'anmu bane!"_

_"Safwan ba dan mu bane!"_

_"Safwan ba dan mu bane!"_

Haka ta shiga jin kalmomin na amsa kuwwa a kunnen ta, kanta yayi wani irin sarawar da be taba yi ba, bakin ta ya gagara furta kalma daya sai ma rawa da jikin ta ya hau yi, da k'yar ta iya daidaita bakin bayan ta fisge hannun da ya rike ta mike tsaye tace

"Safwan ba d'anmu bane?"

"Tabbas... mune iyayen Safwan amma ba mune mahaifansa ba, bamu muka haife shi ba."

"Ta ya haka ta faru?" Tayi maganar cikin kuka sosai

"Kaddara ce wallahi"

"Ina d'ana? Ina yake toh?"

"A ranar da yazo duniya a ranar ya koma."

"Innalillahi wa inna ilaihi rajiun." Ta shiga furtawa da sauri da sauri, ta kasa gasgata abinda taji, wane irin al'amari ne wannan? Shekaru masu yawa kana tare da d'an ka, rana daya sai azo ace ba dan ka bane, tabbas dole ka rude,kokari take ta ajiya komai a ma'aunin tunanin ta amma ta kasa, kokari take ta tabbatar da shin gaske ne ko mafarki take irin mugayen mafarkan nan wanda idan kana yinsu zaka yi ta Allah Allah ya farka ka tabbatar da ba gaskiya bane, sai dai wannan al'amarin yasha banban da mafarki, wanda duk duniya shine mutum na farko da yafi kowa kusanci da ita, ya kuma fi kowa sanin yadda take son Safwan, shine a tsaye a gabanta yake jaddada mata cewa Safwan ba danta bane, toh idan ba danta bane dan waye? Ya akayi haka ta faru? Waye yayi musu wannan aika aikar, wanne irin abu ne haka? Ta kasa gane komai sai jijiiga kanta kawai take tana kuka sosai, kokari yake ya rik'e ta yayi mata bayani amma taki sauraren sa, ja kawai take da baya har ta kai jikin mirror dake dakin,jin taje karshe ne ya saka ta durkushewa a wajen tana jan kukan da take, tana cigaba da maimaita kalmar Innalillahi wa Inna ilaihi rajiun.

***Nagode sosai Wallahi,naga remedies kala kala har ma nayi trying wasu. Alhamdulillah Nagode ma kowa©® Hafsat Rano

*Page 52*

RanoNet
www.ranonet.com.ng
Register for your amazing data at a very cheap price.
Mtn 1gb @300 naira only

***
Idan tace kukan da take zai rage kaso mafi yawa na abinda take ji a zuciyar ta tayi karya, tun bayan da Daddy ya gama yi mata bayanin komai, ta kuma fuskanci komai taji komai ya dawo mata sabo fil,taji dama ace gaskiya ya fad'a mata tun a lokacin, da bata ji irin abinda take ji yanzu ba, da tun a lokacin ta sawa zuciyar ta salama ta hakura, amma sai yanzu da ta riga ta gama sakankancewa, sannan rana daya yazo mata da irin wannan mummunan labarin. A wanne bangare zata ajiye wannan mummunar ranar?
   Da k'yar ta karfafa kanta, ta shirya ta nufi asibitin da safe saboda ranar za'a sallame Safwan din, ba zata ce ta runtsa ba gaba d'aya ranar, yanayin fuskarta kad'ai zaka kalla ka gane cewa ba daidai take ba. Ko da ta isa asibitin sai data fara tsayawa ta kalli kanta sosai a jikin mirror, sannan ta sake gyara fuskarta ta sosai sannan ta nufi cikin asibitin. Duk yadda ma'aikatan wajen ke gaisheta ta kasa sakin fuskarta yadda ta saba musu, duk sun tabbatar babu lafiya amma kuma sunyi mamaki saboda yau za'a sallami Safwan sun zata sai tafi kowa murna.
   Da taje kofar shigar ma sai ta kasa shiga, taji kamar an bige kafafuwan ta, taji kwalla na taruwa a idonta, tayi saurin maida ita, tayi sallama ta shiga tana rufe gefen fuskar ta da mayafin ta. A tsaye ta tarar da Safwan din gaban yar durowar, da sauri ya juyo da fara'ar sa, sai yayi turus ganin yanayin ta

"Mah-Mah..."

"Na'am Safwan, ya jikin naka?"

"Alhamdulillah, are you sick?"

"A ah Safwan."

"Mah-Mah kuka kikayi?" Ya matso da sauri, bata sanda hawayen da take rikewa ba suka shiga sauka akan kuncin ta, tayi saurin saka mayafi ta rufe fuskar ta, ta shiga yin kukan a hankali. Sosai ya rikice yana tambayar ta me akayi mata? Waye bashi da lafiya amma ta kasa amsa masa, kokarin tsaida kukan take amma yaki tsayawa, a haka Daddy ya shigo ya tsaya ya kasa karasowa, da dauri Safwan yayi wajen sa

"Daddy me akayi ma Mah-Mah? Me akayi mata dan Allah."

"Bata jin dad'i ne Son, karka damu idan muka je gida zamuyi magana."

Cikin yanayi mara dad'i Safwan din ya koma gaban Mah-Mah, ya durkusa yana jin kamar ya maida abinda take ji har ya sata kuka kansa, duk tsawon rayuwar sa, ta kula dashi, tayi masa dukkan gata , ta dauki lalurar sa akanta bata iya runtsawa duk sanda yake cikin ciwo,ya kanyi tunanin anya akwai wanda ya kaishi sa'ar uwa kuwa?
   Soyayyar da take masa ba kad'an bace, duk da kowacce uwa dama tana son yayanta, amma shi tashi soyayyar da take masa was beyond... Yana lura da ita har aka gama cike cike aka sallame shi ta kasa had'a ido dashi, ya lura kamar ma kallon sa ne yake saka ta kuka, ya rasa dalili duk ya damu, me zai saka Mah-Mah a cikin irin wannan halin haka?
   Ana discharging dinsa ya kira Sultan a waya, ya fad'a masa sukàyi magana sannan ya kashe, suka dunguma suka wuce gida. Ko da suka isa gidan ma sai da mamaki ya sake kama shi, yasan babu yadda za'a yi Mah-Mah ta kyale shi musamman daga fitowar sa daga asibiti, amma sai yaga abun mamaki, suna zuwa tayi saurin shigewa daki ta bar shi da Daddy a falo, da k'yar ya isa dakin sa, ya kwanta a saman gado yana tunanin sabon al'amarin da ya shigo gidan nasu, wanda ya lura daga Mah-Mah har Daddy kamar wani babban al'amari ne yake damun su, kawai shi Daddy dan namiji ne shiyasa ya daure yake kokarin nuna babu komai, amma fuskarsa ta nuna akwai damuwa babba, ta yaya zai bullowa al'amarin? Gashi Sultan dinsa baya nan balle ya taimaka masa as always. Yana kwance ya k'asa katabus har aka turo kofar, Mah-Mah ce dauke da tray kamar ko yaushe mafiya yawan lukuta idan bashi da lafiya, ta chanja shigar ta zuwa wasu kayan na daban kamar fita zatayi, ta ajiye kayan a gefe ta matso, lokacin ya mike zaune yana kallon ta cikin kalar tausayi

"Kayi wanka kuwa?"

"Ban ba, tun da na shigo kwanciya kawai nayi."

"Ai da kayi wanka zaka fi jin dadin jikinka, oya tashi." Tayi maganar still bata kallon sa, kin tashi yayi, a raunane ya kira sunan ta,

"Mah-Mah."

"Na'am Safwan?"

"Mah-Mah dan Allah me yake faruwa? Na kasa samun sukuni, Mah-Mah ko nayi muku wani laifin ne ban sani ba, dan Allah ki fad'a min ko yafiyar ku ce sai na nema."

Dafa kansa tayi kwalla na taruwa a idonta, ta k'asa magana dan idan tayi zata iya fallasa asirin zuciyar ta, kokari tayi ta karfafa kanta, ta kakalo murmushin da ita kanta tasan ba wai na gaske bane tace

"Bana jin dad'i ne Safwan, yanzu ma asibtii nake son zuwa naga doctor."

"Subhanallahi, are you dat sick?Bari nayi wanka sai muje toh,ko kuma muje haka kawai idan na dawo nayi."

"Calm down, ba wani abu bane da zaka tada hankalin ka, kawai dai zanje su dan duba ni, ba dadewa zan ba, kayi wanka kaci abincin kafin na dawo."

"Please muje Mah-Mah, hankali na ba zai kwanta ba kika tafi ke kad'ai."

"Please Safwan, kar muyi haka da kai, get some rest ba zan dad'e ba in Sha Allah."

"Shikenan, Allah ya dawo dake lafiya."

"Amin ya Allah."

Zama tayi ya juya, har ta kai kofa ya kira sunan ta

"Mah-Mah..."

Juyowa tayi bata amsa ba, murmushi yayi mata sannan yace
Chapter 97 · 0% Book details