← Book details Abinda Ke Cikin Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 40 OF 108

Sashe 40

Abinda Ke Cikin Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Shi aure ana gina shi ne bisa so da kaunar juna, yarda da juna akan abu guda sai komai ya fi tafiya daidai, idan aka ce ko yaushe bangare daya ne zai yi ta kidan sa yayi rawar sa, rayuwar ba zatayi dadi ba, dole sai an samu commitment from both sides sannan ne za'a samu abinda ake so, zaman aure zama ne ba na dan lokaci, zama ne wanda ba'a san ranar kareshi ba, wala'alah sai daya ya mutu ko kuma shi auren ya mutu sannan ne za'a rabu, me yasa kowa ba zai gane hakan ba? Me yasa idon kowa ya rufe ya kasa gane hakan?"

"Ki bani dama dan Allah Amrah, ki bani damar da zaki san ni waye, nayi miki alkawari idan har still baki ji kina so na ba zan barki kamar yadda kika bukata."

"Me yasa sai na baka dama sannan zaka katse wannan one sided alakar tamu, duk damar da zan baka ba zaka taba samun waje a zuciya ta ba, na fad'a, zan kuma fad'a yanzu, Safwan bana son kaa."

Idan har akwai wani tashin hankali toh ya biyo bayan mutum ya kalli tsabar idon ka ya ce baya son ka, musamman mutumin da kake ganin shi kad'ai ne zaka iya bawa zuciyar ka, kalaman ta sun yi ma zuciyar sa nauyi, nauyin da tasa hannayen sa suka shiga kakkarwa, idanun sa suka shiga juyawa a hankali kamar na wanda ya sha wani abun maye, bata kula da halin da ya shiga ba, ta mik'e jin ruwan na kara karfi, tayi nufin barin dakin, sai dai kafin ta kai ga kofar taji karar faduwar abu, ta juyo da sauri, hannayen sa na cigaba da kakkarwar idanun sa sun k'afe suna neman rufewa, da gudu tayi kansa jin yadda yaja sunan ta da karfi kafin komai na jikin sa ya cika ya daina aiki.

**Daya bayan daya kalmomin suka shiga amsa kuwwa a kunnen sa, ya dinga jin suna shiga suna fita da sauri da sauri, jujjuyawa yaji kansa nayi, zuciyar sa tayi zafi ainun, ya shiga yin fashin baki a duk kalmomin yana so ya ware su ya ajiye kowacce a mazaunin daya dace, ciki babu maganar data fi daga masa hankali kamar wadda Mah-Mah da kanta ta kirashi maci Amana sannan ta jefi iyayen da suka kawo shi duniya da kalmomin da yake jin kamar ta dauki fetur ne ta zuba ta kawo ashana ta kyesta masa, zafin da yake ji ba kadan bane, sai yaji yana bukatar yayi abinda ya dace tun kafin komai ya kwabe, idan har mutanen da suka zauna dashi tun yana karamin sa har ya kawo yanzu zasu iya yi masa shaidar wani mugun abu, bayan shi din tarbiyyar su ne, su suka rene shi suka nuna masa yadda zai iya banbance what's wrong and right, toh be san kalar kallon da mutane zasuyi masa ba, Idan har abinda ke cikin zuciya ya bayyana, ya zama dole ya san abinda ya kamata yayi. Juyawa yayi da nufin ficewa daga gidan duk kuwa da yayyafin dake kara karfi sai yaji kamar faduwar abu, sai kuma yaji kamar muryar Safwan cikin mawuyacin hali, a take ya tuno, ya ga sanda Amrah ta nufi bangaran bayan da Mah-Mah ta bar wajen, tashin hankalin da yake ciki be barshi ya gane abinda take son yi ba, da sauri ya nufi dakin hankalin da a matukar tashe, ya bud'e kofar,be san sanda ya kai kansa tsakiyar dakin ba, ya hau jijjigashi da karfi yana kiran sunan sa, babu alamun motsi a tattare dashi, daga shi yayi ya dora shi saman gadon, yayi saurin jawo first-aid kit din sa ya shiga fito da komai na ciki yana hada abinda zai bukata waje daya.
  A hankali numfashin sa ya soma daidai ta amma be farfado ba, sai ya daura masa drip ya juya da sauri zai fita domin samo wata allura da be san ya akayi bashi da ita ba, sai kuma ya tsaya ya kalle ta, kuka take sosai kamar ranta zai fita, tausayin su dukka ya sake kamashi, suna cikin tsaka me wuya.

"Ki kula dashi zanje na samo allura."

Gid'a masa kai tayi ya fita da sauri ita kuma ta matsa gaban gadon tana kare masa kallo.

****Da karfi sosai ruwan yake sauka babu alamun tsayawar sa nan kusa, iska ce me karfi hade da walkiya me tsananin haske ke kara yanayi da karar saukar ruwan, karfe biyar da yan mintuna agogon dakin ya nuna sai dai yadda garin yayi duhu sosai zaka dauka dare ne, tsaye take tsam a gaban gadon tana dubansa cikin zubar hawaye, bata damu da ta share su ba ko tayi yinkurin tsaida zubowar tasu dan hakan ne kadai saukin da take samu a radadin da zuciyar ta ke mata. Turo kofar akayi ta dago da sauri tana sauke idonta akansa, kayan jikinsa sun jike jagaf, idanunsa sun kada sun yi ja jajur ya iso gaban gadon da sassarfa, allura ce a hannun sa, yayi saurin hada ta a jikin sirinji ya dure ta cikin drip din dake sauka a mugun hankali wanda sai ka lura sosai sannan zaka iya gane fitar sa.

"Ya sultan..." Ta kira sunan sa cikin dashewar murya, rinannun idanun sa ya dago ya sauke akanta yace

"Tun bayan fitar da nayi be motsa ba?"

Girgiza masa kai tayi tana matsawa baya, ajiyar zuciya ya sauke da d'an karfi sannan ya gyara masa zaman kansa sosai yana duban sa, duba na tsanaki me cike da tarin manufofi, gefe ya kauda kan sa yana kara karfafawa kansa guiwar abinda yake shirin aikatawa shine daidai.

"Zuwa safiya idan Allah ya kaimu zai tashi kamar babu abinda ya faru." Yace yana motsa jikin ledar drip din kadan. Shiru sukayi na wani lokaci kafin yace

"Amrah... Zan tafi, zan tafi nesa da kowa badon inaso ba, badon hakan shine farin cikin zuciya ta ba, sai dai hakan shine abinda ya dace, abinda ya zama tilas da nayi shi domin shine kadai kwanciyar hankalin mutanen da suka cire rayuwata daga kangin wahala suka lullubeta da tarin alkhairan su wanda ba zasu kirgu ba, suka yanta ni na zama kamar kowanne d'a dake gaban iyayensa. Sunyi min dukkan gatan har na zama abinda na zama a yanzu."

"Magana d'aya kake..." Ta katse shi da sauri

"Me yasa ni ba zaka duba ni ba? Tabbas rama alkhairi da alkhairi shine, amma ka fad'amin, me kayi da ya zama butulci ga alkhairi da suka yi maka? Ka yarda ka kuntatawa rayuwa da ruhin mu akan farinciki su? Wacce irin zuciya ce wannan? Wacce irin zuciya ce...?" Ta karashe tana rufe bakin ta kar kukan da take ta rikewa ya fito.

Jijiyar kansa tayi rud'u rud'u tana harbawa da sauri da sauri, hannu yasa ya dafe kan nasa da yake jin kamar zai guntule daga gangar jikinsa. Takowa ya shiga yi a nutse har ya isa gaban ta inda ta durkushe tana kuka a hankali, kafafuwan sa ya dire a gabanta yana jin tashin hankalin sa na karuwa saboda yadda take fitar da kukan daga chan cikin zuciyar ta, sai dai ya zai yi? Mutumin daya kare rayuwar sa wajen ganin ya samu waraka daga mummunan ciwon zuciyar dake damun sa tun yana zanin goyo, ace kuma sai da komai yazo karshe ya sake maidashi farko, idan yayi haka sam beyi adalci ba,babu abinda ba zai iya sadaukarwa Safwan ba, idan ma rayuwar sa yake so zai iya bashi dan yafi karfin komai a gareshi ciki kuwa harda soyayyarshi. Sai dai hakan na nufin cutar da tasa zuciyar da yake jin tana masa wani masifaffen ciwo da zugi, ya sota tun ranar data fara isowa duniya, tana cilla kafafuwanta tana kuka da d'an karamin bakin ta, a rana Allah yasa masa kaunar ta a zuciyar sa, ya kuma cigaba da dakon sonta har zuwa lokacin daya bayyana mata, ta karbe shi hannu biyu suka raini soyayyar su har zuwa lokacin da komai ya kwabe, lokacin daya tabbatar da ta tsere masa har abada,lokacin daya tabbatar da itace zabin mutum na farko a duniya da yake so da ganin kimar sa, wanda alheransa basa yankewa a gareshi, ya masa dukkan gata ya daga darajar sa a duniya. Dolen sa ne yayi duk yadda zaiyi wajen ganin ya boye *Abinda Ke Cikin Zuciyar sa* har zuwa iya wa'adin kwanakin da Allah ya dibar masa zai yi a doron k'asa.
  Lungu da sako kukan ta ke bin ilahirin jikinsa yana zagaye kowanne sako, da ace yana da damar bude mata zuciyar sa daya bude mata taga yadda take, amma ya suka iya?

"Ki daina kukan nan haka dan Allah."

Ya fad'a kamar zaiyi kukan shima, bata daina ba sai ma kara karfin kukan tayi yayi saurin kallon gadon da Safwan yake kai, ganin be motsa ba yasa ya maida duban sa kanta cikin kasa da murya yace

"Ina sonki, son da ban taba yi wa wani mahaluki irin sa, ina miki so kwatankwacin yadda uwa ke son d'an ta,zan tafi, zanyi nisa dake da d'an-uwa na domin hakan shine kwanciyar hankalin mu. Mubi zabin iyayenmu muyi musu biyayya hakan shine dacewarmu, sai watarana!"

Sai ya mike kamar wanda aka tsikara yayi hanyar barin dakin. Mikewa tayi ta kira sunan sa da sauri tana jan kuka kamar zata shid'e, taku biyu ya kara ya dangana da kofar, sai daya kama handle din sannan ya daga mata hannun sa daya alamun bye-bye ya fita da mugun sauri hannun sa dayan dafe da kirjinsa. Sai ta durkushe a wajen tana sakin kuka ta furta

"Nooo...."

Kukan yake shima wiwi, duk yadda yaso kar su bayyana sai da ya kasa rike su, girgiza kai kawai yake bayan ya gama jin komai, wacce irin soyayya Sultan yake masa har haka? Da ya zabi ya sadaukar masa da abinda yasan da zaman sa a zuciyar sa tun basu mallaki hankalin kansu ba. Dan yana tuna wani lokaci da ake hira da abokai kowa yana maganar budurwar sa, suka matsa masa akan sai ya fadi tasa, lokacin basu fi aji uku a sakandire ba, ya tuna amsa da ya basu

_"Ni bani da budurwa sai mata, na riga na zabi matata tun tana yar jinjirar ta, ku ne a ruwa."_
Chapter 40 · 0% Book details