← Book details Abinda Ke Cikin Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 52 OF 108

Sashe 52

Abinda Ke Cikin Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ga duk mai buƙatar a saka masa tallan kayan sana'arsa a shafin littatafan mu na zafafa biyar zai iya tuntuɓar waɗan nan Numbers 0903 234 5899 or 09033181070 ta WhatsApp, idan har agama buks ɗin kana buƙata a sakamaka talla zamu saka maka akan farashi mai sauƙi. Idan kuma wasu adadin pages kake buƙata koda ɗaya ne duk zamu saka maka akan farashi mai sauƙin gaske🤓.

Kuyi maza ku kawo, mai haja shike talla, mai saya kuwa shike neman sauƙi😻😻😄🤗.

______________________

_ZAFAFA BIYAR 2021_*🔥

_*SUKAR BAYA*_💚
_BILLYN ABDUL_
( _kwai cikin qaya_ )
( _raina kama_)
( _wutsiyar raqumi_ )

*_SIRADIN RAYUWA_*💛
_SAFIYYA HUGUMA_
( _alqawarin Allah_ )
( _daurin boye_ )
( _Dangantakar zuci_ )

💙

_*KIBIYAR AJALI..*_💜
_MISS XOXO_
(Sulke baya tsare ta sai ta wuce)
( _Igiyar zato_)
( _Kaimin halacci_ )
( _Naufal_ )

*_ABIN DAKE CIKIN ZICIYA_*🧡
_HAFSAT RANO_
( _ruhi daya_ )
( _Sauyin qaddara_ )
( _Daurin goro_ )

*_MIN QALB_*❤️
_MAMUHGEE_
( _buri daya_ )
( _tarayya_ )
( _eznah_ )

Duka BIYAR 5 zaku samesu akan garabasar naira 700 kacal,

Guda hudu 4 Kuma 500,

Guda uku 3 Kuma 450,

Guda biyu 2 Kuma 400,

Guda daya akan 300.

Ma'ana
Each one is 300
2 is 400
3 is 450
4 is 500
5 is 700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO- *0812652655*
ACCOUNT NAME- *HAFSAT LAWAN GAMBO*
BANK NAME: *ACCESS BANK*

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

09033181070

Karku Bari ayi Babu ku domin wannnan salon na daban ne
SABUWAR SHEKARA
SABON SALO

TEAM#ZAFAFABIYAR🔥Page 24
Hafsat Rano

***Ta k'asan idon sa yake kallon ta, yadda ta takure a waje daya ta kasa daga Ido ta kalle shi ma, yadda ya cika wajen da kwarjinin sa yasa tayi lakwam ta dinga jin sanyin da take ji na karuwa sosai.
   Nazarin ta yayi sosai, sai yayi murmushi ya taso daga inda yake zaune ya dawo gaban gadon, ya dan tsaya kad'an sai kuma ya zauna a gefen gadon.

"Me kike ji apart from zazzabin?"

Muryar sa ta ratsa ta, ta sake dunkulewa waje d'aya tana jin yadda kamshin turaren sa ya sake cika wajen.

"Babu komai." Tace a gajarce.

Hannun rigar sa ya nannade zuwa saman damtsen sa wanda hakan ya zama kamar wata al'adar shi, sannan ya jawo bowl din da Afrah ta shigo dashi da dan karamin towel ya dora saman bedside drawer.

"Lay down." Yace a hankali, da sauri ta kalle shi, kallon da yasa shi jin kamar zai yi melting a wajen, kallon da yayi nasarar dawo da wata irin zazzafar kaunar da yake mata wadda ya dauke ta ya kaita chan bayan zuciyar sa ya rufe ta ruf, amma da kallo d'aya tak, sai gata ta dawo inda take a da wanda dama dole akayi mata babu yadda ta iya.

"Taimaka miki zan, jikinki yayi zafi sosai."

Yace yana matse towel din,girgiza kanta tayi da sauri sannan cikin murya kamar zatayi kuka tace

"Wallahi zan iya."

"Lay down." Ya sake cewa yana saka idon sa cikin nasa.

"Please..." Taja kalmar tana sake matse wa

"Please." Shima yace, ba tare da wani dogon tunani ba ya saka hannun sa ya kama nata, wani irin shock suka ji a tare da sauri duk suka janye hannun su, ya mike tsaye yana maida towel din cikin ruwan ya juya zuwa wajen da ta ajiye magungunan ya ballo ya dawo ya mika mata. Karba tayi ya mika mata ruwan tasha tana yamutse fuska dan ta sani magani. Ajiye cup din yayi wanda wajen karba sai da hannun sa ya sake haduwa da nata,inda ya sake jin yadda zafin zazzabin ya karu. Be yi shawara da itaba kawai yasa hannu ya mikar da ita a saman gadon, tayi yinkurin tashi yasa hannu a saman bakin sa

"Stay still Malama, babu abinda zan miki just wannan help."

Runtse idon ta tayi lokacin da taji saukar towel din a saman goshin ta, a hankali ya dinga goge mata har zuwa saman wuyanta, sannan ya kama hannayen ta ya goge mata, sai kuma ya tafi zuwa kafarta, wadda tasha jan lalle da yayi masifar karbar fatar ta, tsayawa yayi yana bin zara-zaran yan yatsun kafarta ta da kallo. Dan bud'e idon ta tayi kad'an sannan ta mayar ta kulle da sauri sanda taji ya sake dawowa sàman kan nata.

"Zaki iya juyawa."

"Naam?" Tace da sauri.

"Bayan wai dama..."

"Dan Allah ya isa haka." Tace still idanun ta a rufe, murmushi yayi kad'an sannan ya ajiye towel din

"Shikenan na bari."

Ajiyar zuciya ta sauke da karfi wadda tasa shi kallon ta. Girgiza kansa yayi yana kallon kofa, kafin ya dawo da kallon sa kanta yace

"Kinci abinci?"

"Um um."

"Why? Tun yauhe?"

"Jiya."

"What? Are you serious? Kina so ulcer ta kama ki ko?"

Bata ce komai ba, sai ya ciro waya ya kira Afrah

"Ki kawo mata abinci, idan tea zai samu ki hado dashi." Ya ajiye wayar

"Bansan baki ci komai ba, nazo na baki magani kuma."

"Umm." Tace a zuciyar ta mamakin abinda ke faruwa take, Safwan take expecting gani a wajen nan ba Sultan ba, amma mesa Sultan ne, kuma kai tsaye yake komai kamar ya manta da wacece ita a  wajen shi yanzu, matar Safwan dinsa, bata gane komai ba gashi bata san wa zata tambaya ba. Bude kofar da akayi ne ya sa ta kalli kofar, ajiye kayan hannun ta tayi tana dariya k'asa-k'asa.

"Ya Sultan gashi, akwai wani abun?"

"Babu for now, idan ta ci abincin nasan zata samu bacci idan yaso sai ki dinga zuwa kina dubata."

"Toh, toh ai hakan ma yayi." Tace tana murmushi

"Bari na tafi toh." Tayi gaba abinta, tana musu dariyar mugunta.

Tana fita ta maida kofar ta rufe ta yadda take, tayi tafiyarta, sai dai wannan karon mammakon ta koma cikin gidan waje tayi abinta bata kuma san yaushe zata dawo gidan ba.

"Sit up." Yace mata bayan ya zuba mata abincin a plate, ya had'a mata tea me kauri a cup. Zama tayi ta jingina da fuskar gadon ya mika mata tea din ta karba ta fara sha a hankali.

"Wai duk zazzabin nan nawa ne?"

Da sauri ta zare cup din daga bakin ta aamma bata yi magana ba, wani irin murmushin gefen baki yayi ya cigaba

"Dan Allah ya Sultan, ka taimaka ka aure ni, dan Allah zan mutu wallah,ah ooo wash my heart zata narke."  Yace yana dafe daidai saitin zuciyar sa yana dariya sosai

"Me?" Tace tana bata fuskar ta

"Kin manta yadda kika dinga bi na kina roko na, kinga handsome dan saurayi ko? Toh shikenan ki gode Allah application dinki da kika yi ta turowa an karba, Allah ya mallaka miki ni, I'm all yours now and forever."

Ya karashe fuskar sa na nuna yadda yake ji, kusan mutuwar zaune tayi da jin abinda yace, sai taji kamar a mafarki, kenan Sultan Allah ya bata ba Safwan ba? Amma take ta fama da wahala kowa yaki fad'a màta,

"Alhamdulillah." Tace a hankali ashe ya ga sanda bakin ta ya motsa da abinda tace, tasowa yayi ya zauna sosai kusa da ita wannan karon har kafad'ar sa na gugar ta ta.

"Alhamdulillah ya Allah. Shine abin godiya dan Allah ne kad'ai yasan dalilin da yasa hakan ta faru."

Sai ya juyo yana fuskantar ta sosai, fuskar sa na nuna seriousness dinsa

"Ga Sultan a gabanki Amrah, maraya wanda bashi da uwa ba uba, abubuwa da yawa sun faru a dan lokacin nan da baki ba zai iya fad'an su ba a yanzu,akwai gagarumin abinda yake gabana Amrah, wanda nake jin kamar wani rami ne me zurfi, sai dai ina bukatar taimakon ki, komin runtsi karki cire tsammani, komai zai faru ki sani Sultan dinki zai dawo gareki,safe and sound, ki yi ta min addu'a dan yanzu ke kika fi kowa kusanci dani,haka kuma Allah na karbar addu'ar mata akan mijin ta. Zaki yi min ko wifey?"

"Zan yi in Sha Allah."

"Nagode sosai, for now zaki zauna a gida zuwa sati daya kamar yadda mukayi magana da Daddy yace zai sanar ma Abba. Wait for me kinji, ki shirya sosai, dan Sultan dinki ba na wasa bane." Ya karashe yana kashe mata Ido daya.

Kunya ta kamata sosai ta cusa kanta cikin kafarta tana yin dariya k'asa k'asa .
Kafadarta ya kama ya mikar da ita tsaye, ya tsaya a gaban ta sosai har tana jin hucin numfashin sa a saman kanta dan sosai ya fita tsawo duk da ba za'a sata a layin gajeru ba amma idan ta tsaya a gaban irin su Sultan toh dole za'a ga gajartar ta.

"Will you wait for me? Zaki jirani?"

"I will wait for an eternity." Tace a hankali

"Masha Allah, bani da abinda zai bani tsoro yanzu, knowing I have you zan yi komai na dawo a karamin lokaci."

"Allah ya taimaka ya bada sa'a."

"Amin ya Allah."

"Amin ya Allah." Ya sake maimaitawa.

Shiru sukayi dukkan su, kowa da abinda yake tunani,  a hankali taji zazzabin na barin ta, taji wani irin mixed feeling na shigar ta, irin kamar ace ka gama sanin cewa ka rasa abu me muhimmanci a gareka har abada, sai kuma ya dawo gareka a lokacin da ka cire tsammani.

Knocking akayi a kofar, sai kuma suka ji an saka hannu an murda kofar,

"Ba dai yarinyar nan tafiya tayi min da key din ba." Suka ji yace. Dan karamin tsaki Adnan yaje sannan ya sake cewa

"Toh Ina ma ta tafi ne? Wannna yarinyar."

Suna ji ya bar wajen, sai ta kalli sultan taga shima ita yake kallo

"Rufe mu tayi?"

Daga kafad'ar sa yayi irin I don't care din nan sannan yace

"Na sani."

"Yanzu ya zamuyi?"

"Kwana zamuyi kawai."

"What!?

"Kwana... Ko haramun ne?"

"Amma fa..."
Chapter 52 · 0% Book details