← Book details Abinda Ke Cikin Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 50 OF 108

Sashe 50

Abinda Ke Cikin Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Idan har ka iya shiga Masarautar Saji, ka wuce wadannna masu tsaron kofofin, ka dangana da turakar Maimartaba Sarki Bello Moddibo Saji, a cikin wata katuwar akwatin karfe akwai barin zobe guda biyu a rarrabe da juna, su nake so ka dauko min, ka kawo min bakin gari ni kuma a lokacin zan sadaka da iyayen ka."

"Masarautar Saji!?." Ya fad'a yana mikewa da sauri

"Eh ita, kasan wani abu akanta ne?."

Girgiza masa kai yayi

"Ko kad'an, ina dai son sanin menene alakar neman iyayena da masarautar?"

"Zaka sani gaba kad'an."

"Shikenan." Yace yana murmush wanda yasa Madaki kallon sa da mamaki,

"Me ya sani?" Ya tambayi zuciyar sa

"Ko yasan?" Da sauri ya girgixa kansa

"Be sani ba gaskiya, da bazai zo tambaya ba." Ya bawa kansa amsa cike da gamsarwa.

"Idan har wannan shine zai sada ni da iyayena, zanyi, sai dai ka sani, ka cika alkawari kamar yadda kace zakayi, idan har na same ka da cin amana, zan yi maka abinda bakaa taba tunani ba."

"Nayi alkawari." Yace

Tashi Sultan yayi ya d'an rissina kad'an yace

"Zan tafi."

Sai yayi hanyar fita, bayan ya kai kofa ya juyo yace

"Rana ita yau, a daidai wannan lokacin mu hadu a chan, na barka lafiya."

Ya karasa ficewa, cikin takun sa da ya darsar da tsoro a zuciyar Madakin

"Anya abinda yake shirin yi daidai ne?" Ya tambayi kansa

"Toh amma ai abinda yayi shekara da shekaru yana jira kenan, ba zai kasa a guiwa ba har sai ya ga yayi nasara, kuma nasarar tana tare da Sultan!
Kira ya shigo wayar sa,ya daga yana cigaba da kallon hanyar da Sultan din yabi ya fice

"Hello Musa? Babu labari ko? Eh suna hannu na yaran,toh shikenan ka cigaba da bincikawa idan bamu sameta ba toh lallai sun same ta su, ba damuwa sai ka jini."

Ya ajiye wayar ya tashi ya shiga ciki.

***Yana fita ya samu wani waje yayi parking ya dora kansa a saman sitiyari, tunanin abinda ya kamata yayi kawai yake, tun bayan da sunan Masarautar Saji ya fito a abinda zai yi domin samun iyayensa, yaji wani irin karfi yazo masa, karfin da be san yana dashi ba, karfi ba na jiki ba, karfin tunkarar duk wani abu da zai zo masa. Dago kansa yayi da sauri ya dauko takardar nan ya sake binta, sai kuma ya dauki biro da wata takardar ya shiga rubuta duk sunayen da zai iya tunawa a labarin da Babah ya bashi (mutanen da suka hadu a Canada) kansa yayi matukar daure wa ganin yadda duk sunayen da suke jikin takardar da ya karbo a gidan marayu sun fito a dayar da ya rubuta. Me hakan ke nufi? Ya ambata a dan tsorace
Karar wayar sa ta dawo dashi tunanin da ya tafi da yayi matukar daure masa kai, sunan Mah-Mah ne hakan yasa yayi saurin dagawa

"Sultan kana Ina? Kayi sauri dan Allah kazo jikin Safwan ya matsa."

"Gani nan yanzu yanzu." Yace da sauri, ya kunna motar ya bata wuta w ransa yana mamakin abinda zai tada ciwon Safwan din a irin wannan rana. Ya yasan an riga an daura auren toh me kuma ya faru? Tunawa da yayi da an daura auren yasa yaji wani iri.

"Ya rasata har abadah."

Rano

Forgive the typos

KUNA BUƘATAR A TALLATA MUKU KAYAN SANA'ARKU A PAGES ƊIN BOOKS ƊIN ZAFAFA BIYAR 2021?.

To kuzo ga dama ta samu💃🏻💃🏻.

        Ina ma'abota son a tallata musu hajojinsu a kafafen yanar gizo suke?.

Tofa kuzo dama ta samu, dan jerin gwanon haziƙan marubanku ƴan biyar sun fiddo muku da hanyar da kuma kasuwancinku zai zagaya lungu da saƙo ta dalilin shafukan littatafai.

Ga duk mai buƙatar a saka masa tallan kayan sana'arsa a shafin littatafan mu na zafafa biyar zai iya tuntuɓar waɗan nan Numbers 0903 234 5899 or 09033181070 ta WhatsApp, idan har agama buks ɗin kana buƙata a sakamaka talla zamu saka maka akan farashi mai sauƙi. Idan kuma wasu adadin pages kake buƙata koda ɗaya ne duk zamu saka maka akan farashi mai sauƙin gaske🤓.

Kuyi maza ku kawo, mai haja shike talla, mai saya kuwa shike neman sauƙi😻😻😄🤗.

______________________

_ZAFAFA BIYAR 2021_*🔥

_*SUKAR BAYA*_💚
_BILLYN ABDUL_
( _kwai cikin qaya_ )
( _raina kama_)
( _wutsiyar raqumi_ )

*_SIRADIN RAYUWA_*💛
_SAFIYYA HUGUMA_
( _alqawarin Allah_ )
( _daurin boye_ )
( _Dangantakar zuci_ )

💙

_*KIBIYAR AJALI..*_💜
_MISS XOXO_
(Sulke baya tsare ta sai ta wuce)
( _Igiyar zato_)
( _Kaimin halacci_ )
( _Naufal_ )

*_ABIN DAKE CIKIN ZICIYA_*🧡
_HAFSAT RANO_
( _ruhi daya_ )
( _Sauyin qaddara_ )
( _Daurin goro_ )

*_MIN QALB_*❤️
_MAMUHGEE_
( _buri daya_ )
( _tarayya_ )
( _eznah_ )

Duka BIYAR 5 zaku samesu akan garabasar naira 700 kacal,

Guda hudu 4 Kuma 500,

Guda uku 3 Kuma 450,

Guda biyu 2 Kuma 400,

Guda daya akan 300.

Ma'ana
Each one is 300
2 is 400
3 is 450
4 is 500
5 is 700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO- *0812652655*
ACCOUNT NAME- *HAFSAT LAWAN GAMBO*
BANK NAME: *ACCESS BANK*

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

09033181070

Karku Bari ayi Babu ku domin wannnan salon na daban ne
SABUWAR SHEKARA
SABON SALO

TEAM#ZAFAFABIYAR🔥Wannan littafin na kudi ne, AMANA CE, duk wanda yayi mana sharing dinsa shi ALLAH! Idan kina/Kana so ki/ka karanta ki/ka tuntubi numbobin nan*

*0903 234 5899*
Or
*09033181070*

Page 23
Hansatu Rano

***
A high speed yake tafiya yana fatan ya isa akan lokaci dan yadda Mah-Mah ta kirashi kad'ai da kuma yadda yaji muryar ta ya gane akwai matsala. Yana isa ya kashe motar ya fito, mutanen da ke waje suka bishi da kallo, ya wuce su da sauri ya shige ba tare da ya kawo komai ba, yana shiga yayi saurin wucewa part din Daddy yana dan jin wani iri ganin yadda kowa ke masa wani kallo da be san na menene ba. Tura kofar dakin yayi, Mah-Mah zaune gaban Safwan da kai tsaye ba zaka gane bacci yake ko ido biyu ba, idon sa yayi k'asa sosai dan sai da yaji Mah-Mah tà ambaci sunan Sultan sannan ya dago, fuskar sa dauke da murmushin karfin hali.

"Karka tashi." Sultan yace ganin yana kokarin mikewa.

"Mah-Mah me ya faru dashi?" Ya tambaya sanda ya isa gaban sa,ya ciro stethoscope yana son jin heart beat dinsa.

"Gashi nan kamar ciwon nasa ne ke neman kwantar dashi." Tace still tana cigaba da kuka

"Zai samu lafiya,kiyi hakuri Mah-Mah."

"Inyi hakuri... Dama idan kaji ana bawa mutum hakuri toh an cuceshi ne, bayan duk rokon da nayi maka Sultan, bayan duk maganar da nayi maka akan kayi hakuri, amma ka toshe kunnuwan ka bayan kafi kowa sanin halin da zai shiga, me Safwan yayi maka me zafi haka da ya chanchanci wannan hukuncin naka?"

"Mah-Mah dan Allah ki bari."

Safwan yace yana jin ciwon nasa na karuwa.

"Ba zan bari ba, ban san alkhairi yana juyewa ya zama sharri ba sai yanzu, gashi nan kana kallon halin da ya shiga duk akan abinda yafi karfin sa a wajenka, amma saboda ka kuntata mana ka zabi yin biris da abinda nace maka ka zabi ka cutar da shi, nayi dana sanin shigowar ka cikin family dina, nayi dana sani wallahi..."

"Mah-Mah dan Allah ki tsaya ki saurare ni, babu laifin Sultan ko daya akan abinda kike tunani..."

"Babu laifin sa? Babu laifin sa kake ce min?"

"Eh...Babu laifin Sultan a wannan abun. ." Daddy ya fad'a yana shigowa ciki.

"K'warai Sultan bashi da laifi, be masan abinda yake faruwa ba ko nace ya faru, wanda ni da Safwan da mahaifin Amrah mu muka zauna muka yi abinda ya dace, Sultan be san an daura auren sa da Amrah ba, baya wajen kuma kawo yanzu da kike tuhumar sa be san akan me kike magana ba..."

Sai ya matso ciki sannan yace

"Safwan da kansa yazo ya sameni,ya fad'a min duk abinda ke faruwa wanda kin sani amma kika boye min, ya kuma fadi abinda yake ganin shine daidai, muka je muka samu Prof akan maganar ya kuma nuna mana yasan da maganar Sultan din kuma itama yarinyar shi take so..."

"Kina tunanin auran ne zai bawa Safwan lafiyar ciwon da yake fama dashi tun shekaru masu tsawo? Ko kina tunanin aura masa yarinyar da ko k'ad'an bata son shi taimakon lafiyar sa mukayi? Ko daya. Kinsan menene aure, Kinsan wanne irin zama ne, anyi ma ana son juna both side ya aka kare? Babu abinda zai faru sai kara lalata abin da zamu yi..."

Baya jin duk abinda Daddy yake cewa tun bayan da kunnensa ya jiyo masa Daddy yana maganar an daura auren sa da Amrah, a take jin sa ya dauke dif ya kuma daina fuskantar komai, har zuwa sanda Daddy ya dafa shi, yayi firgigit kamar wanda ya farka daga mafarki, ya kalle shi da idon sa da suka chanja launi.

"Karka damu da abinda mutane zasu ce Sultan, da kai da Safwan duk yayanmu ne, ka yi hakuri da abinda mahaifiyar ku ta farfada maka a baya da yanxu, ajizanci ne irin na d'an Adam. Ka sani babu wanda yake auren matar wani, kuma babu Wanda ke ketare kaddarar sa, saboda ita kaddara rubutaccen al'amari ne tun bayan da aka busawa bawa rai, sai dai addu'a ta kan rage karfin kaddara ko ta chanja ta zuwa wani abu daban."

"Haka ne, nagode Allah ya kara girma." Yace yana yin k'asa da kansa.

"Sai ka shirya zuwa anjima sun ce za'a kai amarya, inda aka tsara nan za'a kaitan,idan yaso shi Safwan duk sanda Allah ya kawo tasa matar sai yayi amfani da d'ayan."

"Daddy dan Allah ayi min alfarma, zuwa sati daya kafin a kaitan."

Yace a hankali

"Kana da wani abu ne?"

"Eh." Ya daga kansa.

"Shikenan zan samu Prof da maganar, sati daya dai kayi duk abinda zakayi idan yaso sai a kaita."

"Allah ya kara girma."
Chapter 50 · 0% Book details