← Book details Abinda Ke Cikin Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 87 OF 108

Sashe 87

Abinda Ke Cikin Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

_"Ni dai na wuce gida zan dawo gobe, kice wa Ya Sultan ya karasa jinyar ki yau, saura kuma kiyi wannan sanyin jikin naki... Ki"_ da sauri ta wafce wayar wata kunyar na sake kamata,

"Bani dan Allah na karasa..."

Kashe wayar tayi baki daya, yayi dariya yana cigaba da tsokanar ta.

"Allah dai ya shiwa Afrah albarka ta san abinda ya dace wallahi, haba mutum da matar sa sai yayi raragefe sannan zai zo ya ganta, shiyasa fa na dage ayi sallama yau, sai gashi Afrah ta biyani."

Yayi maganar yana fadawa saman gadon.

"Karka karya musu gado."

"Sai a siyo sabo."

Tashi tayi ta sauko, ta wuce toilet shi kuma ya je ya saka key a kofar, ya dawo ya shinfida babbar dardumar dake cikin kayan su, ya zauna ya fito da warmers din abinci, yana zubawa ta fito, ta wuce shi ta dau hijab ta hau Sallah, tana idar ya, ya matso da abincin gabanta.

"Ko tanbayar ina nake samun abinci naci bakya yi, Allah sarki ni."

Tasan neman magana yake, ita kuma bata shirya hakan ba, sai ta share shi ta dau spoon din da ya saka a gabanta ta shiga cin abincin, nan ma sai da yayi ta tsokanar ta, karshe ta tashi ta koma saman gadon tayi kwanciyar ta. Toilet din shima ya shiga, yayo alwalar yazo yayi shafa'i da wutri ya jima yana addu'a sosai, tana kallon sa har ya gama, sannan ya taso ya zauna a gefen gadon, sai kuma ya tashi ya bud'e jakar da aka saka blanket din gidan su da ya tawo mata dashi bata ma yi amfani dashi ba saboda Umma ma sunzo da wani, ya shinfida a saman dardumar, ya dawo yace ta sakko, ta kalle shi sai kuma ta sakko din, ya dauki pillown da dayan bargon ya saka pillow ya kwanta, a gefe ta zauna ya mika mata hannu,

"Zo muyi magana."

Kama hannun nasa tayi, ya jawo ta zuwa saman chest din sa, tayi shiru tana jin fitar heartbeat dinsa.

"Da farko dai zan fara da..." Ya fara bata labarin komai tun daga farko har karshe zuwa sanda aka kama Madaki, da kuma su Maman Yara da ya kai su gida sannan da zancen tafiyar su Canada, ya karkare da

"Kinji duk abinda ya faru, sai dai duk ciki babu wanda ya fi daga min hankali irin karshen,hoton da Madaki ya nuna min, ya zanyi?"

Sosai tayi mamakin yadda abubuwan suka kasance kamar a film musamman zuwan sa Masarautar,a nutse cikin hikima babu baragada ta bi dukkannin maganar tasa kowacce gaba ta yi magana akai, yayi shiru yana sauraren ta, hannun sa na zagayawa a cikin gashin kanta, yana kuma daukar duk abinda take fada masa, cikin hikima ta nuna masa abubuwan da yayi na kuskure sannan ta yaba wasu abubuwan da yayi suma, batun hoton nan kuma ta bashi shawara, shawarar da ta saka shi kankame ta yana jin dad'i da relief, lallai mace ta gari rahma ce, tun yaushe yake ta tunanin yadda zai yi amma ita cikin abinda be fi yan mintuna ba ta warware masa komai. Tabbas mace abokiyar shawara ce, maza da yawa basa bawa mata wannan damar wadda suke rasa shawara me matukar muhimmanci a cikin duk abinda suka saka a gaba. Sun dade suna hira har ma basu san iya kar dadewar da sukayi ba, hira ce me dad'i da saka annashuwa, basu san lokacin da bacci barawo ya sace su ba.

***Da sauri ta karasa shiga dakin ganin shi a kwance ko motsawa bayayi

"Maimartaba, Maimartaba!" Ta shiga kiran sunan sa tana jijjigashi, kuka ta saka ta fito da sauri, ta dauki wayar sa ta kira emergency number, cikin abinda be kaza yan mintuna ba sai ga mota daga nearest asibiti, suka dauke shi suka saka shi a mota aka wuce dashi asibiti.
Number Sultan tayi ta gwadawa amma taki shiiga, duk ta rikice ta rasa me zatayi, kuka kawai take tana jin ta tsani komai da kowa da irin rayuwar da sukeyi su kad'ai babu dangi babu yaya.
Ba dan Allah yasa ta shigo dakin nasa a lokacin ba, da bata san me zai faru ba, sosai tausayin sa ya kamata ganin da gaske a wannan lokacin babu abinda yafi bukata sama da yaran sa, su tallafe shi su tsaya akansa, hakan ya kara saka ta a matukar damuwa, gashi babu wanda zata kira balle ta samu sassaucin abinda take ji idan sukayi magana da wani.

***Ita ta fara tashi, ta yunkura zata mike ya maida ita yana lumshe Ido

"Asubah tayi fa." Tace tana kallon fuskar sa ta dan hasken da ya shigo ta saman kofar dakin.

*Um um.." ya sake kankame ta, yana makale ta sosai

"Ka tashi please".

"Bafa muyi bacci sosai ba." Yayi maganar yana kin bud'e idon. Daddagewa tayi ta mintsine shi, yayi saurin ware idanun, ya sake da sauri ya hau sosai wajen

"Maimartaba kike yiwa haka? Lallai yarinyar nan." Lokacin har ta kai kofar toilet, tayi masa gwalo ta shige da sauri ta saka key, ko da ta fito yana zaune ya kunna wutar dakin,ya harare ta irin hararar wasa.

"Allah sai na rama, zaki gane baki da wayo."

Dariya tayi, yayi kamar zai rik'e ta sanda zai shiga toilet din, ta zille da sauri tana dariya.

Sallah sukayi, ya dauke kayan shinfidar, ya ce ta koma kan gadon ta kwanta tunda ba wani bacci sukayi sosai ba, kwanciya tayi ya gyara mata komai sannan ya zauna zuwa sanda garin yayi haske, sannan ya koma gida. Yana zuwa ya shiga daki ya rage kayan jikin sa ya kwanta, nan da nan bacci ya dauke shi me karfin gaske.
Sai wajejen sha daya ya tashi, yayi wanka ya fito, ya shiga ya gaida su Maman Yara ya same su suna zaune suna hira, yayi mata ya jikin sannan yace zai tawo musu da kaya saboda su chanja dan tun wanda suka tawo dashi ne.
Mota ya hau, ya tunkari inda yake saka ran samun Daddy, yana tafe yana tunanin yadda komai ya tafi kamar yadda suka tsara.
Lokacin da Madaki yayi masa kiran nan, yayi recording komai, yana katse kiran ya nemo number wani abokin sa babba a DSS, ya bashi bayanin komai, number wayar sa ya bukata, a take suka yi tracking number suka gano location din da yake, da kuma komai akan gidan wanda ya kasance gidan wanda aka kama sun tare ne, hatta abinda sukeyi a gidan sai da suka gano suka kuma tashi mutum biyu cikin farin kaya suka isa gidan suka sake samun information akan komai. Ko da Madaki ya turo address din already su sun isa wajen wasu ma suna cikin gidan cikin badda kama. Babu abinda ba za'a iya yi ba idan ana son a dakile abubuwan da ake yi a k'asar nan tamu akan harkar rashin tsaro amma babu me yi. Allah ya kyauta.
Sanda ya shiga layin nasu,zuciyar sa sai da ta buga saboda tsoron abinda zai tarar, amma idan ya tuna hakan ce hanya kad'ai da zai iya cire wasiwasin da Madakin ya saka masa. Bama wannan ba kad'ai, atleast zai taiamaka masa wajen karasa sauran abubuwan da yake son karasawa da yake ta fadi tashi shi kad'ai, yasan zai bashi shawara a matsayin sa na mahaifi shawarar da zata taimaka masa.
Yana yin parking Afrah suka fito ita da Adnan, daga gani asibitin zasu,yayi saurin rufe baki yana girgiza kai

"Wai sai yanzu zaki koma?"

"Na zata wallahi kana chan." Tace tana rufe baki.

"Aiko sai anci ki tara, kika barta ita kad'ai."

"Ayi hakuri." Dariya yayi suka gaisa da Adnan,ya shiga ciki su kuma suka wuce. Kai tsaye falon ya wuce, ya tura kofar cikin rashin kuzari, gami da sallama. Yana tsaye da remote control a hannun sa, ya juya da sauri.

"Sultan."

"Barka da gida Daddy."

****
Banyi editing ba, I'm very very busy ne Wallahi. Afwan.

Wadanda sukayi min magana ta PC banyi reply ba, kuyi hakuri ba a nutse nake ba ban zauna ba.
"
©hansatu rano
Page 46
Zafafa biyar na kud'i ne!!!

***
Yana tsaye da remote control a hannun sa, ya juya da sauri.

"Sultan." Ya kira sunan shi yana takowa zuwa tsakiyar falon

"Barka da gida Daddy." Yayi maganar yana russunawa

"Ina kwana Daddy?"

"Lafiya lou Sultan, ya gajiya da dawainiya? Allah dai yayi muku albarka."

"Amin Daddy."

Dan jim yayi, har Daddy ya gama dube duben tashar sa, ya zauna yana dora hannun a saman kujerar da yake kai

"Akwai labari ne sultan?" Yayi maganar rabin hankalin sa na kan talabijin din.

"Dama wata magana nazo muyi Daddy, ina ban takura ba."

Juyowa yayi gaba d'aya ya kalle shi

"Ina sauraron ka, menene ya faru?"

Gyara zama Sultan din yayi, ya kalmashe kafar sa yadda zai ji dadin zaman sannan yace

"Dama Daddy akwai abubuwan da suka faru..."

Ya shiga bashi labarin komai cikin hikima ba tare da Daddy ya fuskanci takurawar Mah-Mah ce ta saka shi tunanin neman sanin waye shi din, tiryan tiryan yake bin komai har ya kai gabar da ya samu address din Madaki, sai a lokacin yaga Daddyn yayi sak kamar zai yi magana sai kuma ya cigaba da sauraren sa. Be rage komai ba, ya kwashe komai da ya faru, ya sanar dashi har zuwa haduwar su ta karshe da Madakin da kamashin da yasa akayi, sai dai be kai ga fad'awa Daddy abinda Madakin yace masa ba ya dakatar dashi bayan yayi kamar zai kware har sultan din yayi saurin tashi ya dauko masa ruwa ya bashi, be iya sha ba ya ajiye a gefe sannan yace

"Yanzu Sultan ace duk ka shiga irin wannan matsalolin amma sai yanzu zamuji, me yasa baka sanar dani ba tun farko, baka tsoron abinda zai je ya dawo? Kasan waye Madaki kuwa Sultan?... Mutumin da babu Imani a ransa babu..." Sai kuma yayi saurin yin kwana yace

"Mutumin da daga yadda ka bani labarin sa babu abinda ba zai iya ba domin ya cutar da kai, ko nace ma ya cutar da kai tunda ga dan uwan ka nan da matar ka badan Allah ya kiyaye ba waya san abinda zai faru!?"

"Dama Daddy..."
Chapter 87 · 0% Book details