← Book details Abinda Ke Cikin Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 77 OF 108

Sashe 77

Abinda Ke Cikin Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

***Duk suka tsaya suna kallon hasken wanda yayi matukar daure musu kai, hasken yayi nasarar ankarar da mutanen nan suka juyo da sauri zuwa inda suka ji kamar motsi a wajen, hannun Amrah Sultan ya kama, suka soma tafiya da sauri Safwan da Muhammad na bayan su. Daga chan hanyar shigowa wanda Madaki ya bawa aikin bin Sultan din ne tsaye suna jiran fitowar sa, suna tsaye suka ji jiniyar yan sanda,

"Babah me nake ji kamar sheggun mutanen chan."

"Sune mana, amma kamar basu kusa karasowa ba ai."

"Kawai mu kutsa kai muyi abinda ya kawo mu, mu fece kafin su karaso."

"Kawai ba, hakan zamuyi."

Ciki suka shiga a kafa, lokacin jiniyar na kara matsowa sosai. Daga nesa suka hango mutane biyun nan dake bin su Sultan a bayan su, wanda su basu masan suna binsu ba, sauri kawai suke su isa wajen motar su.

"Ka gansu chan Baba, su biyu ne dama yace ko? Kawai mu bud'e musu wuta, mu koma muce yayi gardama mun sheke shi, sai mu cire zoben kawai kamar zai fi."

"Abinda kawai zamuyi kenan, karya bata mana lokaci har sheggun chan su karaso."

"Ah toh mu saita ta kawai."

Saitawa sukayi daidai lokacin su Sultan sun iso wajen mota, babu zato babu tsammani sai jin harbi sukayi wanda ya tafi direct ya sauka a akan Safwan da yake kokarin bude motar, ya kwalla k'ara da karfi ya zube a wajen, da gudu sukayi kansa Sultan na kwala kiran sunan sa a gigice,

"Safwan! Safwan." Rike shi Muhammad yayi yana kokarin saka hannun sa a daidai inda jini ke fitowa ta wajen da bullet din ya shiga. Jin harbin ya saka suma masu bin nasu suka shiga maida wuta a tunanin su yan sanda ne, sosai Amrah ta gigice ta fara neman hanyar guduwa wanda bata yi aune ba ta bugu da wata katuwar bishiya dake gabanta, zubewa tayi a take ta kwalla k'ara itama, karar da ta sake ruda Sultan yayi kanta da gudu yana kiranta.

Kuka Sultan yake wiwi, kukan da be taba yin irinsa a rayuwar sa ba, mutane biyun da suka fi kowa kusanci dashi, a sanadiyar sa yau gasu a cikin mawuyacin halin mutuwa ko rayuwa, yes shi likita ne kuma yadda yaga Safwan na fidda jini da yadda Amrah ma kanta ya bugu har ta sume yasan tabbas za'a iya rasa su, ko kuma ita ta samu wani internal ingury, amma for Safwan, bashi da tabbas.
   Zuwan su Adnan da yansanda wajen ya saka suka arce amma sunyi nasarar kama mutum daya acikin wandanda suka fara harbin da har ya samu Safwan.
    Daukar Safwan din sukayi aka sashi a mota wanda gaba daya hankalin su ya tashi ganin halin da yake ciki, karma Daddy da yayi matukar kaduwa da ganin d'an sa a halin rai ko mutuwa. Tun dazu yake neman wayar sa bata shiga ashe nan suka tawo shi da Sultan din, wanne irin so yake wa Amrah haka ne da har zai iya risking life dinsa, sannan sultan, yana masa son da ya zama wani abin dubawa, wanda baya iya ganin shi a damuwa ba tare da ya taimaka masa ba.
  Duk tsawon shekarun nan Safwan has been very good to Sultan, yana kin duk abinda Sultan din yaki ko da kuwa shi yana son abun,yana kuma zama cikin damuwa duk sanda Sulthan din ya shiga damuwa. Duk da shi ma Sultan din hakan ce a wajen sa, amma shi nasa da banbanci da na Safwan, shi yana yin komai ne domin rama halacci kamar yadda yake ganin anyi masa, ba kamar soyayyar da shi Safwan din yake masa ba wadda ta kasance daga Allah.
   Har suka karaso cikin gari suka kuma nufi asibiti Daddy be samu hanyar da zai sanar wa Mah-Mah abinda ya faru ba, be masan ta yadda zai fara ba, yace mata wajen cetar Amrah ne ko kuma yace mata wajen rakiyar SULTAN ne? Yasan ba zata saurari kowanne a ciki ba, saboda dukkan su biyun sune mutanen da Safwan yake so, kuma sune soyayyar su ke bashi wahalar da har take kaishi gadon asibiti, yanzu gashi nan ta kawo shi inda ko su kansu Sultan da Amrah basu da TABBACIN abinda zai faru. Duk da itama unconscious aka dauko ta amma ba kamar Safwan ba, da bullet ya ratsa ta jikin sa ya huda. Yadda yake zubar da jini kad'ai abin tsoro ne.
   Da gudu ma'aikatan suka iso suka karbe shi, aka nufi ICU dashi, wasu kuma suka karbi Amrah aka wuce da ita emergency room. Makalewa sultan yayi a jikin wani gini ya durkusa a wajen, zafin da yake ji yana fitowa daga chan k'asan zuciyar sa zuwa saman fatar shi ba abu bane me sauki. Me yasa duk be yi tunanin abinda zai faru ba yayi risking rayuwar Safwan wanda be san komai ba sai farin cikin sa, Safwan deserve something very very good tunda yana da heart me kyau, yana son kowa da zuciya tsarkakakkiya.
   Da sauri ya tashi kamar wanda aka tasa, ya girgiza kansa yana kara karfafa kansa

"Babu abinda zai same su, babu abinda zai same su." Ya cigaba da fad'a yana tafiya, a tsaye ya tarar da Abba, Adnan da Daddy hankalin su a tashe, duk suka bishi da kallon tausayi. Durkusawa yayi a gaban Daddy yana sauke kansa kasa ya kasa cewa komai

"Sultan, tashi kaji? Addu'a kawai suke bukata a yanzu, muyi musu addu'a." Gid'a kansa yayi da sauri yana tunawa da addu'a. Tabbas addu'a suka fi bukata fiye da komai yanxu, zaije yayi musu addu'a yanzu. Masallacin cikin asibitin ya nufa, yana jan kafar sa har ya isa, ya daura alwala a gaban fanfon wajen ya shiga ciki ya dukufa kai kukan sa wajen ALLAH. Be san iya kar adadin da ya dauka a wajen ba, sai da yaji an dafa kafad'ar sa, ya juyo sukayi ido da Adnan da idon sa ya chanja sosai kamar gauta, ya tashi da sauri

"Adnan ya ake ciki?" Ya rik'e shi

"Amrah ta farka, tana son ganin ka."

"Safwan fa? Karka cemin he's still unconscious dan Allah, ba zan iya dauka ba."

"Mu cigaba da addu'a."

"Ya Allah!" Ya kama kansa dasauri, yayi baya kamar zai fad'i, Adnan ya rike shi da sauri.

"Zai samu sauki in Sha Allah, mu cigaba da addu'a."

***Daga kai yayi ya kalli abinda aka rubuta a saman dakin kafin ya tura ya shiga, a kwance take an nannade mata kanta da farin bandeji inda ta bugu, drip ne a daure a hannun ta wanda yake shiga a hankali. Babu kowa a dakin, kasa karasawa yayi yana jin kamar ba zai iya karasawa ba, kamar ma ba zai iya takawa ba yake ji, ganin ta motsa yasa shi ya isa wajen ya tsaya a gaban gadon, fuskar ta tayi fari sosai ta fad'a, hannu ya kai ya shafi gefen fuskar ta, ya kama hannun ta guda d'aya ya rik'e a cikin nasa, yana jin zafin jikinta da nashi na haduwa waje d'aya. Kansa ya dora a saman gadon daidai inda kanta yake yana jin kamar ya cire ciwon ta dana Safwan ya dora akan sa, basu chanchanci kasancewa a wannan state din ba saboda shi.

"Sultan..." Ta kira sunan sa a hankali, dagowa yayi idon sa ya sauka a cikin nata, yayi mata murmushi da sauri, ta mayar masa tana daga hannun ta dayan.

"Karki motsa,I'm here, me kike so? Kina son wani abu?"

Girgiza kanta tayi hawaye na gangarowa daga idon ta

"Karka sake tafiya ka barni."

"Ba zan sake ba, I promise you, duk inda zanje tare zamuje."

Murmushi tayi, shi kuma yayi kissing din saman idon ta tayi saurin runtse idonta tana jin wani irin feeling.

ZAFAFA BIYAR
NA KUDI NE:::

Duka BIYAR 5 zaku samesu akan garabasar naira 700 kacal,

Guda hudu 4 Kuma 500,

Guda uku 3 Kuma 450,

Guda biyu 2 Kuma 400,

Guda daya akan 300.

Ma'ana
Each one is 300
2 is 400
3 is 450
4 is 500
5 is 700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO- *0812652655*
ACCOUNT NAME- *HAFSAT LAWAN GAMBO*
BANK NAME: *ACCESS BANK*

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

*+234 903 234 5899*

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

*09033181070*

Karku Bari ayi Babu ku domin wannnan salon na daban ne
SABUWAR SHEKARA
SABON SALO

TEAM#ZAFAFABIYAR🔥© Hafsat Rano
Page 37

Zafafa biyar na kud'i ne!!!

_*INA MASU NEMAN MAGANIN INFECTION SADIDAN? MAGANIN NI’IMAH, MAGANIN GYARAN HIPS AND BOOBS? MAGANIN BASIR....NA HAUSA BANA BATURE ME KWANTAR DA CIWO BA? TO KU MARMATSO KUSA, DOMIN YAU MUNA TAFE DA ALBISHIR WANDA ZAI FADADA MURMISHIN FUSKOKIN KU.. YA KUMA KAWATA ZUKATAN KU. MUN GWADA MUN GANI, MAGUNGUNANTA SUNADA KYAU KUMA SUNA DA AIKI.. BABU SIDE EFFECT, ANYI SU NE DAGA TSAFTATTUN KAYAN ITATUWA, DA SIRRIN CHADIAN HERBALS.. KARNA CIKAKU DA SURUTU;_

_*AISHA S BAYERO TRADITIONAL MEDICINE AND HERBAL RESEARCH CENTER..._*

_KUNJI SUNAN KO? CENTER CE TA MAGUNGUNAN GARGAJIA, WANDA DUK WANI DAMUWA DAKE DAMUNKA IDAN HAR KAZO WAJEN S BAYERO TA KARE DA YARDAR ALLAH.._

_KADAN DAGA MAGUNGUNANTA SUN KUNSHI:_

_MAGANIN SANYI _
_MAGANIN NIIMA SET_
_MAGANIN NANKARWA _
_MAGANIN KIBA BABBA DA _KARAMI _
_MAGANIN HIPS _
_MAGANIN GYARAN NONO _
_MAGANIN RAGE KIBA _
_MAGANIN SAKA FEELING _
_MAGANIN CIDA KWAI _
_ZUMA YAR ASALI_
_MAGANIN BASIR KOWANNE IRI _
_HODAR NI’IMA _
_MAGANIN MALLAKA _
_GUMBAR NONON RAK’UMI _
_GUMBAR MADARA _
_TURAREN FARIN JINI _
_KAZA MARA KWAI _
_TURAREN MALLAKA 3 STEP _
_HAD’IN MATAR MINISTER 1_
_KAZA ME KWAI_

_STEP 2:_

_TURAREN MALLAKA ME KWALBA _
_ME KUNAMA DAN MATSI _
_TURAREN GOSHI _
_TURAREN QIRJI _
_TAUWADAR MATA _
_MEMORY _
_KAHON MALLAKA_
_YAJIN MAZA_
_TEA DIN MAZA _
_DAMBUN MATSI_
_MAN AYU_
_MAN DAMO PURE _
_KWALLIN IDONKA IDONA _
_GARIN SHA DAKA ME KYAU _
_KUBEWAR MATA_

_DUKA WADANNAN INGATTUN MAGUNGUNA NA GARGAJIYA HAJ AISHA NA DASU GANGARIYA.. HERBAL MAGUNGUNA NE MASU KYAU DA INGANCI.. TAFIYAYYU NA KASAR CHAD. CHADIAN HERBAL MEDICINE AND RESEARCH CENTER.. KYAU, INGANCI.. RAHUSA... SAI MAGUNGUNAN *AISHA S BAYERO TRADITIONAL MED AND HERBAL RESEARCH CENTER...._

_NUMBER WAYAR WHATSAPP: 08121491609 KO KIRA TA NUMBER 08145873617._
Chapter 77 · 0% Book details