Sashe 43
Abinda Ke Cikin Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Bayan sun dawo daki suna zaune akayi sallama a waje, Muhammad ya tashi zai je, Ammi ta tsaida shi tace
"Ina zuwa."
Mayafinta ta yafa ta fita, wajen mintuna biyar suna zaune shiru bata dawo ba, Muhammad ya tashi ya fita dan yaga abinda ya tsaida ta, sai dai abin mamaki babu ko me kama da ita a layin, da sauri Muhammad ya dawo ciki yana kwala kiran Aysha, ta fito tana tambayar sa lafiya. Waje suka sake komawa suka hau duddubawa sai dai babu Ammi sama ko k'asa.
***
Karar ganguna da kalangu ne ke tashi a kowanne lungu na Masarautar, duk inda ka kalla zaka ga mutane na kaiwa da komowa, hakan ya nuna ana wani gagarumin taro ne ko kuma wani shagalin biki a Masarautar, sai dai a irin wannan ranar, a irin kwanan watan Sarkin na shirya musu wani shagali na musamman da babu wanda yasan dalilin shirya shi, kowa ya kan samu abinci me rai da lafiya yaci har ma yayi guzarin sa zuwa gida.
A wani babban Fili dake cikin masarautar anan ne ake gudanar da bikin. Daga chan saman wani tudu an shirya kujeru na alfarma, manyan yan fad'ar sarki ne a zazzaune kowannen su yasha nadi irin na sarakai, sarki be fito ba tukunna, mafiya yawan lokuta baya fitowaa ya kan dai dawo fad'ar sa dake kusa da filin ya zauna yana jin duk abinda ke faruwa.
Yau ma hakan ne ya faru, yana zaune akan karagar sa, mutane uku da ya aminta dasu kaf Masarautar, Magatakarda, Waziri da Madaki na zaune a k'asa suna tattaunawa, sakon ya iske su. Me sakon ne ya fadi k'asa yayi gaisuwa, suka amsa masa da sarki ya gaishe shi, sannan ya mika wata takarda, ya koma gefe ya durkusa, magatakarda ne ya karba ya warware ta sannan ya soma karantawa a fili bayan sarki ya bashi umarni.
Da wani irin yanayi dukka suke kallon shi har ya gama karantawa ya nannade ta ya mika ta ga Waziri, dubawa ya sake ki sannan ya kalli Sarki yana rissinawam
"Allah ya baka yawan rai."
Da hannu sarkin yayi masa alamar da tasa shi duban d'an aiken sannan yace
"Mahdi ya tabbatar da abinda yake fad'a? Ya sani babu Wasa tsakanin sa da Masarautar, idan har abinda ya rubuta a jikin wasikar nan gaskiya ne, muna bukatar ya bayyana a gaban fad'a gobe warhaka tare da ita."
"An gama ranka ya dad'e."Hafsat Rano
Page 21
www.instagram.com/zeeherbalsaphrodisiac.
_*ASSALAMU ALAIKUM SISTERS..!_*
_*INA MASU NEMAN INDA ZASU SAMU INGANTATTUN: _*
_*HERBALS APHRODISIAC MA’ANA NA GARGAJIYA BANA HADIN BATURE BA MAI SIDE EFFECT..?_*
_*TO KU MATSO, DOMIN NESA TAZO KUSA.._*
_*ZEE HERBALS APHRODISIAC_*
_*ZEE HERBALS APHRODISIAC_*
_*ZEE HERBALS APHRODISIAC_*
_*MUNZO MUKU DA INGATTTUN KAYAYYAKI WANDA ZASU GYARA KI CIKI DA WAJE_*
_*MUNADA SUPPLEMENT MASU GYARAN JIKI DANA FATA, WANDA ZASA SAKI KIYI SHEKI FATAR KI TAYI LAUSHI. TAYI LUWAI LUWAI TAMKAR TA JARIRAI_*
_*AKWAI SUPPLEMENT NA KAYAN MATA WANDA ZASU GYARA KI, KIJI KI TAMKAR BUDURWA, SUPPLEMENTS DINMU BASU DA SIDE EFFECT, DOMIN AN HADO SU NE DAGA INGATTATTUN ITATUWA, WATO NATURAL PRODUCTS NE ACIKI._*
_*KAI BA ANAN KADAI MUKA TSAYA BA, MUNA DA INGATTUN KAYAYYAKIN MATA WANDA KESA KISHIYA KWAFA, WANDA DUK INDA SARAUNIYA TAKAI KIN WUCE, WANDA ZASU TSATSO MIKI MARTABAR KI DA KIMAR KI_*
_*AKWAI INGATTATTUN MAGUNGUNA, NA CUTUTTUKAN DA SUKA SHAFI DAN ADAM DAMA JINNU.. KAI DAMA WANDA BAMU AMBATA BA.. ZEE HERBALS APHRODISIAC (MASARAUTAR INGATTATTUN MAGUNGUNA KENAN)_*
_*KYAU, ARHA, INGANCI, RAHUSA... SAI ZEE HERBALS APHRODISIAC_*
_*MANHAJOJIN MU NA SOCIAL MEDIA: KAMAR INSTAGRAM DA WHATSAPP DAMA NAMBAR TARHON MU: DOMIN SHIIGA KUGA IRIN KAYAYYAKIN MU TUNTUBE MU TA_*
_INSTAGRAM LINK DIN MU:_
www.instagram.com/zeeherbalsaphrodisiac
_WHATSAPP LINK DIN MU:_
https://Zeeherbalsaphrodisiac.whats.bz
_NAMBAR TARHON MU_
08169380189
_*DA A BAKA LABARI GWARA KA BAYAR.. KIZO A DAMA DAKE YAR UWA, KI ZAMO DAYA DAGA CIKIN KASAITATTUN MATA MASU AJI.. MUNA GARIN KATSINA, SANNAN KAYAN MU MUNA BADA SU AKAN FARASHIN SAYA ‘DAI DAI KO SARI.. MUNA TURA KAYAN MU A KO’INA A FADIN NAJERIYA._*
*****
***Duk inda suke tunanin zasu duba sun duba amma babu ko me kama da Ammi balle ita kanta, zuwa lokacin sun fara tsorata da lamarin, Aysha kuka take sosai, tausayin su ya darsu a zuciyar yan gidan, suka fito aka cigaba da neman Ammin tare dasu. Ana haka ne wata mota ta tsaya a daidai kofar gidan, suka tafi da sauri suna zuwa yana fitowa, driver Alhaji Safiyanu Madaki ne dan Aysha ta gane shi sanda suka je wajen. Da sauri suka isa wajen sa, har suna hada bakin tambayar ina Ammi? Kai tsaye yace musu be ganta ba, zuwan sa kenan Alhaji ya aiko ya tafi dasu. Hankalin su ya kara tashi akan na da, dan da sunyi tunanin ko chan wajen nasa ta koma ko kuma dai shine ya aiko a dauke ta. Gefe Muhammad yaja hannun ta, suka matsa yana kafe ta da idon sa da yayi mugun kad'awa.
"Me ya faru da kuka je wajen sa?"
"Da muka je..." Ta soma bashi labarin abinda ya faru har karshen maganar da sukayi yace zai turo a dauke su,da wayar da ya fita yayi da kuma sunan da Ammi ta ambata (Mahdi) wanda yasa Alhajin fita yayi wayar, komai ta fad'a masa, yayi shiru yana son gane me hakan ke nufi, sai dai duk iya kokarin sa na son dora abinda ya faru a ma'aunin da zai gane komai ya k'asa, idan ya kamo nan sai ya kwance ta chan, it doesn't make sense to him gaba daya. Ammi taje wajen sa, tace taga wani, ya fita yayi waya, ya dawo sunyi magana again sannan yace zai turo a dauke su, daga nan kuma aka zo aka ce ana sallama, Ammin ta fita, shiru shi kuma yanzu ya aiko din a dauke sun, dukkan wannan abin be bashi ma'ana guda d'aya da zai nuna abinda yake faruwa ba. Ya tabbata dai tafiya akayi da Ammin tasu, wadda tun bayan tasowar su bata taba nuna musu wani ko wata a matsayin wanda ta sani ba, sai yau katsaham tazo wa da kanwar tasa da yake gani a matsayin kanwar sa uwa d'aya uba daya sabon labarin da ya sashi a shakkun, shi waye kenan idan har mutumin da suka je suka gani shine mahaifin Aysha, toh shi waye nasa mahaifin? Me ya faru ko kuma me yake shirin faruwa.?
Wajen driver suka koma, yace Aisha ta shiga motar shi kuma ya koma ya fiffito da kayan su, ya tayashi suka saka a cikin motar, ya nemi alfarma wajen Malam Tsalha makocin su akan idan Ammi ta dawo kafin shi ya dawo ya fad'a mata sun je wajen Alhaji Madaki, amsa masa yayi da toh sannan suka tafi.
*Sultan*
***Gida ya koma ya dauki motar sa, ya sake duba address din gidan sannan ya dauki hanya. Yadda unguwar take Babbar unguwa dake dauke da gidaje a tsare, kowanne gida na dauke da number a jiki ya taimaka masa k'warai wajen saurin gane gidan, daga gefe chan yayi parking, ya tsaya yana kallon gidan. Menene hadin sa da maigidan da har ya fito a cikin sunayen mutanen da zai nema. Bud'e murfin motar yayi ya sauko, ya nufi gidan kai tsaye, a tsaye ya tsaya ya kwankwasa gate d'in, maigadi ya leko ta yar kofar, sai kuma ya zare sakatar ya fito gaba daya, hannu Sultan ya bashi suka gaisa sannan ya tambaye shi ko Alhaji Safiyanu Madaki yana nan, d'an jim yayi yana nazari, kwana biyun nan ana yawan zuwa neman uban gidan nasa, ya kuma jaddada masa kar ya kuskura ya sake barin ko waye yazo in dai ba har shine ya fad'a masa ba. Amma sai kuma ya dubi Sultan, be yi kama da irin mutanen da Alhajin yake nufi da kar ya barsu ba, shi gaba daya ma kwarjini Sultan din ya cika masa ido da ma filin wajen gaba daya.
"Yana nan kuwa?"
Sai yayi firgigit ya k'asa duban sa yace
"Alhaji baya nan yayi wata yar tafiya, amma me zai hana ka nemi shi a waya ko kuma dai ka fad'a min abinda idan ya dawo zan fad'a masa, kaga zai fi sauki idan ka dawo kawai ganin sa zakayi."
"Ko zaka taimaka ka bani number ka, idan yazo sai ka fada masa Azizah ce ta turo wani bawan Allah, idan ya yarda zai ganni sai kayi min ko da flashing ne idan yaso sai na dawo."
"Toh hakan ma yayi yallabai." Ya fada yana washe baki, ciki ya shiga da niyyar dauko wayar sa ya bawa Sulthan din ya saka tasa number a ciki yayi flashing sai yaga tasan dan ba wai sanin ta yayi da kah ba, yana dauko wayar yaji mahaukacin horn din da ko ba'a fada masa ba yasan waye, da gudu ya kwasa yayi gate din, ya hau kokarin budewa a rikice, ji yayi gate din ya yi saukin turawa, sai da ya kai karshe ya juyo yaga Sultan tsaye hannun sa a jikin gate din alamar tare suka bude. Maimakon wanda aka bude kofar domin shi ya shiga, sai ya tsaya idon sa akan Sultan fuskar sa dauke da mamakin waye shi?
Karbar wayar Sultan yayi ya saka number shi, sannan ya kira ya ga number yayi saving, ya mika masa yayi masa godiya ya juya da nufin barin wajen. Da sauri Ameer ya balle murfin motar ya fito
"Minti daya Dan Allah." Yace yana tsayawa a gabansa, hannu Sultan ya bashi sukayi musabiha.
"Sunana AmeeR."
"SULTAN." Yace yana murmushi
"Kazo wajen Daddy ne?"
"Eh wallahi, nazo ganin sa amma ban same shi ba, amma zan dawo."
"Ok..." Sai yayi shiru.
"Sai anjima?" Sultan yace
Dafa kansa wanda ya kira kansa da Ameer yayi, yace
"Kamar na san fuskar ka waallahi, a zahiri ko a mafarki? Ban sani ba, kawai inaji kamar ace na hadu da wani celebrity da na dade ina fatan haduwa dashi, something like that, wani irin strange feeling na kamar kasan wani kuma ka manta aina."
Murmushi Sultan ya sake yi
"Kasan hakan na faruwa, may be mun taba haduwa din kuma, ko kuma me kama dani ka sani."
"Umm... Probably, toh amma dan Allah ka bani number ka, idan na tuna inda na sanka, I ll give you a call."