← Book details Abinda Ke Cikin Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 108

Sashe 6

Abinda Ke Cikin Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

***
Da safe bayan Umma ta tashi su Amrah tasa su sunyi wanka sun shirya sai ta shiga gidan Mah-Mah kafin lokacin da Abba yace zasu tafi yayi. Gaisawa sukayi sai ta dauko mata maganar tafiyar tasu, sosai maganar ta daki Mah-Mah, dan batayi zato ko tsamammani ba, musamman yadda aka saba sosai rana daya mutum ya tafi wata uwa duniyar, dole abin zai taba ka, hakuri dai Umman ta bata da alkawarin zumuncin su ba zai yi komai ba, sannan ma sun yanke shawarar barin Adnan awajen su saboda ya karasa zuwa lokacin sai ya biyo su.
   Har gate ta rakota tana sake jaddada mata yadda tafiyar tasu ta zo mata a bazata, da yadda zasuji ita da yaran idan basa nan. Ita dai umma hakuri tayi ta bata sannan sukayi sallama ta tafi.
    Su Sultan na tsaye Umman ta fito, suka gaishe ta, ta wuce ciki. Tana shiga ta tarar da wayar ta Abba na kira, dagawa tayi yace su sameshi a chan immigration office din zai wuce daga nan dan kar a bata lokaci. Adnan tasa Afrah ta kirawo ya fitar da mota, lokacin Safwan ya shiga gida sai yace Sultan yazo suje.
   Suna zuwa basu wani dau lokaci ba  akayi musu komai saboda wani abokin Abban da yake aiki a wajen suka juyo gida.
   Da yamma Abba ya saka Adnan ya maida Amrah kafin Hajiya ta sake kira, tare suka tafi su dukka har da Afrah da tace itama sai tayi rakiya. Sultan ne yake driving din, Adnan a gefen sa sai su kuma a baya tare da Safwan da yake ta tsokanar Afrah tana biye masa, ita dai Amrah bata ce komai ba tana ta juya set din earing da Umma ta bata ta kai wa Hajiya har suka iso, kama kofar tayi zata bude ta kasa, da sauri Sultan ya balle murfin kofar sa ya bude mata, fitowa tayi tayi kicin kicin da fuska ta kalle shi, murmushi yayi mata ya mika hannu ta bashi dan kunnen, noke kafada tayi ta wuce shi, karar fadowar abu yaji, ya kalli inda ta bari, dan karamin bracelet ne golden and red me kyau yasa hannu ya dauka yana kallo, sai yayi murmushi ya zura shi a aljihun sa ya bi bayan su dan tuni duk sun shige ciki.
    Yana shiga ya ganta a tsaye gaban Hajiya ta rike kugu tana maida labarin abubuwan da suka faru, komai sai data fad'a mata bata rage komai ba, mamakin ta sukayi tayi ashe tana nad'e komai tana jira ta dawo ta amayar, dungure mata kai Adnan yayi ta hau bubbuga kafa Hajiya ta kai mishi bugu da muhucin hannun ta ya goce yana dariya.
    Har dare suna gidan, sai da Abbaya kirasu ya fara fad'a sannan suka tafi suka bar Afrah a chan dan tace ba zata tafi ba.
     A hanya duk suna ta hira Amma Sultan be sa musu baki ba, zuciyar sa ta lula a tunanin abinda ke nukurkusar ta, ya rasa dalilin da yasa yake jin irin feeling din da yake ji idan ya ganta. Yarinya ce karama just 9years amma yana jin wani irin shock duk sanda ya kalli kwayar idon ta, zai iya cewa idanun ta kadai ke sashi jin kamar yayi ta tafiya ba tare da ya tsaya ba, ya kan ji wani irin strong attachment idan kwayar idonta ta sauka a cikin tasa, gashi dai shi din ma nawa yake? He's not ready for any relationship dan karatun da yake shirin tunkara ba na raguwar zuciya bane, yana so ya zama cardiologist, cardiologist consultant saboda Safwan, saboda ya zama babu wani matsala tasa da zata taso har a rasa me tsaya masa, ya yarda ko da shi kadai karatun nasa zai amfana bashi da damuwa akai, bashi da matsala hakan kadai ya wadatar.

***
Shirye shiryen tafiya ya kankama, komai ya zama ready sai rana kawai ta rage musu, Hajiya da Amrah, Mah-Mah da yan samarin ta basa son tafiyar ko kadan, amma babu yadda zasuyi din sai fatan hakan ya zama alkhairi a garesu baki daya.
Daren ranar tafiyar mutane da yawa basu runtsa ba, ciki harda sultan da yake jin kamar some part of him is leaving him, juye juye yayi tayi kafin a soma kiraye- kirayen sallah ya tashi zuwa toilet.
   Jirgin karfe goma zasu bi saboda haka tun kafin lokacin yan uwa da abokan arziki suka cika gidan, aka dunguma aka tafi raka su airport. Bayan komai ya zama cleared jirgin su ya daga cike da kewar mutane dan da kyar aka raba Hajiya da Amrah dake ta faman kuka.

*Bayan shekara* *(6)*

***Abubuwa da yawa sun chanja rayuwa ta cigaba da garawa cikin hukuncin ubangiji, shigar Safwan, Adnan da Sultan jami'ah ya kara taimaka musu wajen sake sanin rayuwa. Bangaren da kowa ya zaba yake karanta, inda Safwan ya zabi bangaren law Sultan kuma medicine sai Adnan da yake karantar Criminology, da taimakon Abba kowa ya samu dream karatun sa.

***Sallama suka yi a kusan tare suka shigo gidan, Daddy na zaune yana cike wasu takardu ya dago ya sauke idon sa akan yaran nasa, har suka karaso be dauke kansa daga kallon su ba, yana nazarin su sosai, Mah-Mah na lura da irin kallon da yake musu tasan bazai wuce na mamakin yadda suka girma suka zama manyan samari ba, Safwan ya gama law yana shirye shiryen tafiya law school inda Sultan yake level 500, Adnan kam har yayi service din sa ya bi su Abba chan da niyyar zai dan huta kafin ya dawo kuma a fara maganar aiki.
  Sai da suka zauna a gaban sa sannan ya sauke boyayyiyar ajiyar zuciya yana fad'ad'a fara'ar fuskar sa.

"Barka da gida Daddy."

Suka fad'a a tare

"Barka dai my boys, likita bokan turai ya karatun?"

Yace yana maida hankalin sa kan Sultan

"Alhamdulillah wallahi, muna ta fama kamar mutum ya zura da gudu."

"Ayi hakuri kar a zura din, wataran sai labari."

Dariya suka saka gaba daya, ya tambayi Safwan shirye shiryen da yake, ya amsa masa suka cigaba da hirar har sanda lokacin sallah yayi suka tashi.

****
G*idan shiru babu alamun akwai wanda ya tashi a cikin su kasancewar weekend ne, tsaye take a babban kitchen din dake daura da kofar fita daga shahen baki daya, wuka ce a hannun ta tana aikin ferayar dankali inda hankalin ta ya rabu gida wajen biyar cikin son ganin ta gama komai ta kammala kafin cikar lokacin data d'iba wa kanta, a k'aidar ta bata wuce karfe tara bata gama hada komai ma. Duk da aikin ba me yawa bane amma kasancewar sa kashi-kashi yasa yake ci mata lokaci.
  Hannun ta ta wanke a gaban sink ta sa dan karamin towel ta tsane su tana sake duba komai, mutum ce ita me matukar tsafta da kyankyami, hakan yasa take aiwatar da komai cikin tsantsani da takantsantsan had'e da zallar kwarewa. A saman dining ta jera musu komai bayan ta zuba nata ta wuce zuwa dakin su.
    Jan bargon da Afrah ta rufe kanta dashi tayi, ta kai mata duka a baya, a rikice ta tashi ta hau sosa wajen tana ware idon ta, ajiye plate din hannun ta tayi ta dauki towel ta wuce toilet tana jan siririn tsaki, Afrah tasan suna da islamiyya amma ta kwanta tana bacci dan wulakanci, bata son a komai a bata mata lokaci tafi son komai tayi shi cikin tsari, bata da hayaniya har yanzu koman ta a nutse take yin sa, zaka dauka yanka ce da ita sai dai ko kusa haka nature dinta.
   Ware gashin kanta tayi ya bi bayan ta ya kwanta har kusan rabin bayan nata, shampoo masu kamshi ta matsa ta wanke kan tas sanñan tayi wanka a gurguje ta fito, ganin Afrah nannade a bargon still yasa taje a fusace ta fizgeshi

"Amrahhhhg..." Taja sunan tana lumshe idon ta, duka ta sake kai mata da yasa ta mike da sauri.

"Allah kika bari na gama sai dai ki hakura dan bazan jira ki ba."

Tace cikin harshen turanci tana komawa gaban mirror, kunkuni Afrah tayi ta wuce toilet din ta barta tana shiryawa a nutse.
     Black abaya duk suka saka Amrah ta yane kanta da orange veil da zanen black ita kuma Afrah tasa yellow. Ashirye suka fito suka tarar da Ya Adnan a saman dining yana breakfast, zama Afrah tayi suka karasa tare suna dan taba hira, Amrah na gefe tana kallon su dan ita tayi nata, a tsarin ta bata son zama a saman dining shisa ko yaushe take cin nata daban.
Sun tashi zasu tafi Adnan ya tsaidasu ya dauke su hoto sannan suka tafi. Komawa daki yayi ya shirya sannan ya dauke wayar sa, misscalls din Safwan ya gani, yabi kiran yana zama a cikin cushion din falon.

"Hello..." Yace sanda akayi picking call din, sai dai baya jin komai alamun network din chan bashi da kyau, kashewa yayi ya hau whatsapp, ya ganshi online sai kawai ya masa magana. Hira sukayi sosai da zasuyi sallama yace ya tura masa hoton kannen su dan rabon sa dasu tun ranar da suka tafi. Gallery Adnan ya shiga ya tura masa wanda sukayi tare dazu sannan ya kashe datar ya sa wayar a aljihu ya fita walk.

Da wani irin sauri Safwan ya tashi zaune daga kwanciyar da yayi yana sake kallon hoton, zuciyar sa na wani irin bugawa da sauri da sauri. Sake kalla yake yana son gasgata abinda ya gani, haka yaran suka kara girma da kyau ko kuwa idon sa ne? Kamar wasu twins haka suka koma masa, bin su yayi tayi da kallo kafin ya tsaida kallon sa akan Amrah yana sake zooming sosai.

"Ya Rabb!" Yace yana fadawa baya

"Qurratul ayn." Ya furta yana shafa kansa, murmushi me kyau ya subuce daga bakin sa zuwa saman lips din sa.

A hankali ya sake furta

"Itace wallahi.!*_Abinda Ke Cikin Zuciya_*

©_Hafsat Rano_

Free page 5
Chapter 6 · 0% Book details