← Book details Abinda Ke Cikin Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 65 OF 108

Sashe 65

Abinda Ke Cikin Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Musa ya rada masa a kunne sannan yayi gaba shi kuma Sultan ya bishi suka nufi Babbar kofar da zata sada ka da cikin Masarautar. Kamar mutum mutumi haka Sultan ya shiga binsa yana jin kamar jinin jikinsa na tsittsinkewa yana bin hanyar da ba ita aka tanada masa domin bi ba, wani irin sakayau yake jin sa, irin abinda be taba ji ba sai sau biyu, na farko a asibiti watarana da MD ya kirashi, sai kuma a Canada. Sai kuma yau da yake jin kamar ma har wani sanyi sanyi yake ji na ratsa shi, ko kuma ace a dauko kankara a dora masa a jiki a kuma zo a rufe ta da babban mayafi. Har suka karasa inda zasu din be iya sake fahimtar komai ba, yana jin sanda Musa yake magana da wani dake chan gefe shi kad'ai, sai kuma yaga ya taso sun sake bin sa har zuwa wajen wasu su uku suma, sannan suka je wajen wasu, anan suka dan bata lokaci sai kawai yaga an bud'e musu kofar ance su shiga, kallon Musa yayi yaga baya kallon sa sai ma saka kansa da yayi suka shiga takawa cikin Masarautar wanda yake jin duk wani takun da zai yana amsawa a dukkan gabobin sa. Tafiya suka shiga yi da dan sauri duk da haka be bari abu daya na daga Masarautar ya tsere masa ba, ya bi komai yadda ya kamata ya kuma karance wani abu kad'an daga cikin yadda mutanen Masarautar suke al'amuran su, wanda kallo daya zakayi musu ka gane basu da maraba da bayi, wanda tsantsar wahala da rashin walwala yayi ma katutu.
A wata kofar katako suka tsaya, wani da Sultan ya lura da yanayin yadda yake abubuwan da sauri sauri yayi saurin bud'e musu, suka kutsa kai ciki sannan yaja kofar ya rufe yana sauke nauyayyar ajiyar zuciya kana ya bar wajen bayan ya tabbatar da babu wanda ya gansu.

***Hannun sa a goye a bayan sa yana kaiwa da komowa tsakanin dakin, daga chan gefe wasu ne a durkushe kansu a k'asa , dakin yayi shiru dukkanin su suna jiran suji abinda Sarkin zai ce, tsawon lokaci be ce komai ba sai dan siririn tsaki da yake ta ja a hankali a hankali. Sun cire rai da zai ce wani abu sai kuma ya koma da baya ya hau kan karagar sa, sannan yace cikin kaushin murya.

"Idan har abinda muke tunani zai shigo cikin Masarautar nan a gobe, ya zama dole mu tabbatar da zuwan sa hannu, duk da bamu da Ikon ganin ko menene ko waye, sai dai jikina na bani wani gagarumin abu ne ke tunkaro mu, dan haka ba zamuyi kasa a guiwa ba wajen ganin mun kare martabar abinda muka dad'e kafin mu same shi, ya zama dole ne, kowa a cikin ku ya zama a shirye shiri bana wasa ba, dan bamu san wanne shiri sukayi a kanmu ba."

"An gama ranka ya dad'e." Suka had'a baki wajen fad'a, wani daga ciki ya duka kad'an sannan yace

"A duban da nayi dazu, sai naga abun na kusa damu sosai, kusan da nake jin tsoron kar mu sakankance su shammace mu, ina ganin ya kamata a sake dubawa."

Babban yayi karaf da sauri yace

"Kana nufin abinda na gani akan zuwan nasu gobe ba daidai bane? Ko kana nufin bansan aikin da nake ba ne?" Ya karashe a dan hasale.

"Ba ina nufin hakan bane, sai dai..."

"Ya isa!" Sarki ya dakatar dasu

"Yanzu ba lokacin musu bane ko nuna wani yafi wani, lokaci ne na aiki babba, aikin da yafi wanda kukayi a baya, ruwan kune ku bar komai ya lalace."

"Tuba muke ranka ya dad'e."

Fuu ya tashi ya shige ciki ya barsu zaune, a hankali duk suka fice daya bayan daya cikin shigar su ta kowanne lokaci idan zasu zo ziyarar sarkin.

***Karewa dakin kallo Sulthan yayi, babu komai sai wata tabarma daga gefe, sai tarin wasu kaya daga dayan bangaren dakin, sai dai akwai bandaki karami a manne a ciki, da sauri ya sauke jakar sa, ya nufi kofar bayan ya tabbatar da hasashen shi, alwala ya dauro saboda ya samu yayi sallar data tsere masa, yana fitowa musa ma ya a shiga yayi alwalar shima, sultan ya jasu suka rama sallolin da suka tsere musu sannan suka yi Isha'i wadda ake yi a daidai lokacin.
Pad din sa ya ciro ya bud'e yana duba sakonnin da Amrah ta turo masa akan ta kira shi a kashe dan kashe ta yayi gaaba daya, murmushi yayi me kyau sannan ya tura mata reply,few lines masu ma'ana, kafin tayi reply ya maida wayar flight mood saboda baya son ta kira shi ta masa tambayar da bashi da amsar ta shima.
Suna nan zaune wanda ya rako su ya sake shigowa, ya ajiye musu kwanon abinci guda biyu kowa a gaban sa,ya rissina sosai wajen bawa Sultan wanda har yaso ya bawa Sultan din mamakin yadda suke girmamashi duk da be san dalili ba, be ma kuma san me Madaki da wannan amintaccen yaron nasa Musa suke shirya wa akansa ba, ya riga dai ya gama shirin sa shima lokaci yake jira ya aiwatar da komai amma kafin nan zai cigaba da bin su a yadda suka yi nasu tsarin.

******
Assalamu alaikum
Barkanmu da Sallah ya iyali? Masu complain na ki dawowa kuyi hakuri, abubuwa ne suka sha min kai plus bana gari. Hankali na gaba daya yana kan rubutun nan tunda duk abinda ka fara burin ka kawai ka gama shi ka sauke nauyi.
Nayi typing da yawa yana Wattpad sai dai ntwrk sam ya hanani logging, complain din da naji ne ciki hadda maganganu marasa dad'i yasa na rubuta wannan din yanzu. NagodeAbinda ke cikin zuciya
Hafsat Rano
Page 30

****
Tashi yayi maimakon ya ci abincin da aka ajiye masa sai ya bud'e jakar sa ya dauko cake da fresh milk yasha kad'an. Abincin Musa ya dauka yaci sosai yana kallon sa, da yaga ya cinye tas sai ya tura masa nasan gaban sa yace

"Ba ci zanyi ba."

Murmushi Musa yayi ya ja kwanon gabansa kara cin kusan rabi sannan ya kora da ruwa, sannan yayi hamdala. Duk Sultan na hankalce dashi sai da ya ga ya gama ya maida komai gefe ya gyara zama yace

"Musa, inaso zan tambaya kà."

"Allah yasa na sani." Ya amsa da sauri yana tattara hankalin sa gaba daya wajen sa.

"Wanne shiri kukayi kai da Madaki? Me kuka tsara akan abinda ya kawo mu.?"

"Allah ya taimake ka, da farko dai zamu cigaba da zama anan ne kwana uku zuwa sati, zuwa dai sanda Maimartaba zai yi wata tafiya da aka tabbatar mana da cikin satin nan ce, idan yaso daga nan sai muyi abinda ya kawo mu, mu fice."

"Idan har haka ne, me yasa kai ba zaka iya dauko masa abinda yake so din ba? Sai ni dole."

"Saboda kai kad'ai ne zaka iya." Musa ya amsa masa kai tsaye.

Shiru Sultan yayi yana tattare maganar waje d'aya, sai kawai ya tashi ya shiga zagaye dakin yana jin lallai akwai wani kulli da Madaki ya shirya masa, amfani zai yi dashi ya cimma wani burin sa, ba zai taba bari suyi wasa da rayuwar sa ba, zai kuma nuna masu shi ma namijin duniya ne, zai basu mamaki idan har ya gama binciken da yake akan komai ya gano akasanin yadda suka zo masa.
   Zai fara da kurkukun nan da daga nan kuma zai dauko abinda yace masan ya dauko sai dai ba zai bashi kai tsaye ba, shima zai buga nasa wasan ne daidai da yadda ya dace.
   Daren ranar be wani yi baccin kirki ba, a kusan zaune ya karasa kwanan ya saka wannan ya kwance wannan, ganin lokacin yaja sosai yasa kawai ya karasa raya daren yana addu'ar Allah ya yanke masa wahalar neman iyayensa da yake ya kawo masa komai a cikin sauki.

***Dakin Mah-Mah ta kwankwasa, yana kwance da wani littafi a hannun sa, jikin sa ya dan yi karfi sai abinda ba za'a rasa ba, tashi yayi ya dora jallabiya akan gajeran wandon sa sannan ya bud'e.
   Tray ne a hannun ta, da sauri ya mika hannu zai karba

"Mah-Mah bakya gajiya."

"Ya jikin naka?" Tace bayan ta ratsa ta gefen sa ta wuce ciki, bin bayan ta yayi ya zauna a gefen ta.

"Na samu sauki ai."

"Masha Allah, Allah ya karo saukin."

"Amin Mah-Mahn mu."

"Kai da wa?"

"Nida Sultan."

"Karbi, maza cinye." Ta mika masa plate din tana share zancen.  Hannu yasa ya karba ya ajiye a gefe yace

"Mah-Mah..."

"Na'am."

"Dan Allah ki daina ganin laifin Sultan akan abinda ya faru, Sultan yayi iya kokarin sa wajen boye min halin da suke ciki, da yake Allah ya kaddaro ita din matar sa ce, sai yasa naji komai da kunne na, kuma nayi alkawarin cika masa burin sa kamar yadda yayi kokarin cika min nawa."

"Toh baban yan tsari, ni bana son maganar nan ma, kaci abincin kar yayi sanyi."

Sai ta tashi tayi hanyar fita tana sababi

"Ka bi ka damu kanka akan wanda be damu da kai ba,kana ganin tun da yasa kafa ya fice daga gidan nan ranar da aka daura auren ka sake ganin sa? Ko ya kiraka yaji halin da kake ciki?"

"Mah-Mah...!"

"Please Safwan, bana son zancen nan."

"Shikenan Mah-Mah, Allah ya baki hakuri."

"Yafi, kaci abincin ka gyara jikinka, Mubarak ma yazo neman ka dazu kana bacci."

"Zan fito idan na gama."

"Yawwa." Tace sannan ya ja masa kofar. Girgiza kansa yayi ya soma cin abincin a hankali

***Su wajen uku ne a zaune a gaban sa,kansa a k'asa yana duba wata takarda, murmushi yayi bayan ya gama ya dago yana mikawa daya daga cikin su.

"Yaro be san wuta ba sai ya taka."

Yace yana tuntsurewa da dariya.
Chapter 65 · 0% Book details