Sashe 92
Abinda Ke Cikin Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
"Allah yasa." Zata mike yace ta zauna ta karasa breakfast din, hannu ta daga masa alamar bye bye ya fice ita kuma ta karasa cin abincin ta tattare wajen ta gyara ta zauna ta kunna tv.
***Yinin ranar be zauna ba sam ya kira Gimbiya sun yi magana ya kara kwantar mata da hankali sosai, tace masa Maimartaba ma ya motsa har yayi magana duk da ba'a ji me yace ba
Daga nan yayi asibiti daga asibiti ya wuce wajen da Madaki yake tsare inda yake samun labarin ashe Madakin bayan abubuwan da yayi,yana cikin manyan masu supplying bullets da ake amfani dasu wajen kai hare-haren dake damun kasar nan, yayi mamaki sosai yadda wai ace musulmi akan abun duniya xai iya salwantar da rayuwar wasu mutane da basu ji ba,basu gani ba. Dole case din ya sake zafi sosai sai ya zama kamar ma sun ajiye case din kidnapping Amrah da yayi an shiga wannan babban case din. La'asar likis ya gama ya nufi gidan su, ya samu Daddy a harabar gidan yana zaune yayi nisa a tunani, wanda sam be ji sallamar Sultan din ba sai da ya zauna a gefen sa.
"Sultan kaine."
"Nine Daddy, barka da gida ina wuni?"
"Lafiya lou Sultan."
"Kuna lafiya? Ya jikin Amrah?"
"Da sauki Alhamdulillah."
"Masha Allah, Allah ya kara sauki."
"Amin ya Allah."
"Safwan ma jiki yayi kyau, sai karashe kawai nace dai kar su sallame shi saboda ciwon nan."
"Ah jiki yayi kyau, wa ya dauka ma zai rayu?"
"Haka ne, Allah ya kara sauki."
"Amin ya Allah, Allah yayi muku albarka."
"Naje wajen Madaki dazu, abubuwan dai babu dad'i, suna kan bincike dai har yanzu."
"Allah ya rufa asiri, ya bada sa'a." Kawai Daddy yace yana girgiza kansa. Maganar tafiyar su yayi ma Daddy yayi musu addu'a sannan yayi sallama ya tafi. Maimakon ya wuce gida sai ya tsaya wajen Mubarak sukayi magana sosai sannan ya tafi.
Tun da ya tafi babu abinda tayi sai kallo da danna waya, sai bayan da tayi sallar la'asar ne ta tashi ta dora girki, hadadden girki irin wanda tasan Sultan din naso, dama ita a wannan bangaren ba baya bace. Cikin kwarewa tayi komai ta kammala a daidai lokacin da ya dace,ita din mutum ce me kazar kazar musamman a wajen girki da aikin gida saboda sune abubuwan da tafi so fiye da komai
Hannun ta ta wanke a gaban sink ta sa dan karamin towel ta tsane su tana sake duba komai, mutum ce ita me matukar tsafta da kyankyami, hakan yasa take aiwatar da komai cikin tsantsani da takantsantsan had'e da zallar kwarewa. A tsakiyar falon yanzu ma ta jera komai dan ta lura kamar yafi sakewa a kasan fiye da saman dining din. Sai data sake kallon komai ta tabbatar yayi, tayi murmushi ta yi saurin fad'awa tayi wanka a gurguje ganin lokacin ya ja. Light make-up tayi mara hayaniya ta saka wasu kayanta na cikin lefe riga da skirt ne masu kama da yan kanti, ta gyara kanta ta saka turaren gashi me dadin kamshi, sannan tabi ko ina da khumra da turarurruka masu sanyin kamshi. Sai data gama komai ta zauna sannan taji shigowar sa, yau babu wani tunani ta fita da sauri ta bud'e kofar, ta gama jira ya shigo da motar ya rufe gidan sannan ta fita ta karasa kafin ya karaso suka hadu a hanya,
"Tubrakallah!" Yace yana murmushi
"Welcome home."
"Thanks dear."
Hugging dinta yayi suka dunguma suka shiga ciki, duk yadda take sunnewa sai da ya saka ta saki jikinta dashi fiye da dazu, suka ci abincin yana ta santi sannan yace zai wanka, tashi tayi ta shiga ciki domin hada masa ruwan wankan sai gashi ya shigo daure da towel a kugun sa, ya saka kafa ya tura kofar toilet din ta rufe ya murda key yana kashe mata ido
"Let's bath." Yace yana matsawa kusa da ita, a matukar tsorace take tayi saurin cewa
"Wallahi nayi, ban ma dade dayi ba."
"Na sani, na gani ma ai, kawai karawa zakiyi."
"Wayyo Allah, ni wallahi nayi wanka."
"Bari muga." Ya matso ta sosai, ya saka hannun sa ya zagaye waist dinta, ya dora fuskar sa a saman kafadarta
"You look cute idan kina jin tsoro, ba wani abu fa nace ba, just wanka, ke kamar wata yar garin chan."
Shiru tayi bata tanka ba, dan tasan tunda yayi niyyar sai yayi, sai kawai ta rufe idon ta, tana jin shi yana kidan sa da rawarsa shi kad'ai.
Daren ranar ya sake zama memorable a wajen sa, kusan ma fiye da na farkon amma banda wajen Amrah, ga yadda garin ya saki babu zafi sai iska dake kad'awa me dadin gaske. Jawo tayi gaba daya jikin sa yayi hugging nata so tight kamar wani zai kwace ta. Da haka barci me karfi ya kwashe su
***
Ana gobe zasu tafi, ya kaita gida tun safe, ya wuce asibiti, yaji dadin ganin jikin Safwan ya sake yi, suka dade suna hira dan a chan ya cinye fiye da rabin lokacin, daga nan suka fita tare da Adnan suka siyo abubuwa sannan suka wuce gida.
Tare suka shiga gidan da Adnan, suna zaune da umma suna hira suka yi sallama suka shiga, sai ga Sultan ya k'asa daga kai ya kalli Umma, yayi ta sunne kai Afrah da Adnan na tsokanar sa, be kula su ba, sai umma ce ta hanasu sannan ta tashi ta basu waje, abinci aka kawo musu suka ci, sannan suka tafi inda suka wuce gidan Hajiya bayan sun jira Abba yazo sun masa sallama. Babu wani karba da Hajiyan tayi wa Sultan din, dan har yanzu ba wai ta huce bane, ba kuma ta gamsu da Sultan din ba kamar wanda shine ya zaba wa kansa rayuwar a haka. Basu wani dad'e ba sukayi mata sallama suka tafi, suna zuwa karasa hada abinda zasu hada kawai sukayi suka kwanta saboda su tashi da wuri.
***Jirgin karfe sha daya na safe zasu hau, saboda haka kafin lokacin sun gama shirya komai, Adnan da zai kaisu airport shida Afrah tuni sunzo, har da Umaimah da Mah-Mah da tun jiya dama ita a asibiti yayi mata sallamar sa, sai gata tare dasu Adnan din babu wanda yayi tunani a cikin su.
Basu wani bata lokaci ba suka wuce airport din, suna zuwa basu dade sosai ba aka kirasu, sukayi sallama da kowa idon umàima akan Sultan yana sallama da mutane, kuka ne taji yazo mata tayi saurin maida su tana karfafa kanta, tafi karfin haka tunda ta riga ta gama shirya abinda kawai zatayi dan ba zata zauna son sa ya kashe ta a banza ba, shi yana chan yana watayawar sa, taso da ita akayi tafiyar nan Amma babu komai rai dai.
***Manage manage. Yan tafiya Canada su o'o da o'o ina fatan kun gama had'a jaka ko?😂😭😭🔆🔆Abinda Ke Cikin Zuciya
Page 49
ZAFAFA BIYAR NA KUDI NE!!!
***Hannun ta ya kama ganin yadda idon ta ya cicciko, ya mintsine ta kad'an tayi saurin kallon sa, ya girgiza mata kai yana murmushi.
Har suka gama duk abinda ya kamata su yi hannun sa na sarke a cikin nata, ta rasa dalilin da yasa yake son rike hannun ta ko da yaushe, ko hakan na cikin abinda yake so ne? Bata sani ba. Sai da suka dangana da wajen zaman su a cikin jirgin sannan ya sake ta, ta zauna shima ya zauna kusa da ita, ya cije bakin sa kad'an a lokacin da yayi tunanin halin da Maimartaba yake ciki, idan ya tuna sai yaji kaso me yawa na murnar da yake ta ragu, musamman da yake jin kamar wannan din shine ganin sa dasu na farko. Tana lura dashi yadda yanayin sa ya chanja, duk sai taji babu dad'i, tasan kuma abinda yake damun sa duk kuwa da yadda yake kokarin daurewa, fuskarsa kad'ai ta isa ta fallasa asirin zuciyar sa, amma karfin zuciya irin tasa, ta gaza nuna gajiyawa ko kuma sarewa akan abubuwan da suka faru dashi a dan kankanin lokaci, sai ma kokari da yake wajen ganin ya faranta wa duk wanda yake tare dashi. Tasan da gaske yana cike da damuwa, amma bata san ta yadda zata fara taimaka masan ba, rufe idon ta tayi, ta jingina da saman kujerar tana sauke ajiyar zuciya.
Tayi nisa a tunani har bata san sanda akayi sanarwar jirgi zai tashi ba, jin sa kawai tayi daf da ita, yana kokarin daura mata belt din, bata yi motsi ba har ya gama, ta bud'e idon ta daidai lokacin da yake kokarin daga kansa, idonta ya hadu cikin nasa, wanda taga ya sake chanja kala sosai.
"Ya Sultan...!!"
"In Sha Allah komai zai dawo daidai."