← Book details Abinda Ke Cikin Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 42 OF 108

Sashe 42

Abinda Ke Cikin Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Waigawa yayi ya kalli me maganar, Malam Bako ne, sai ya fad'ad'a fara'ar fuskar sa ya juya wajensa

"Malam." Ya kira sunan sa sannan ya dora

"Barka da warhaka Malam."

"Barka dai Sultan, ina ciki aka zo aka cemin kazo, ashe dai kai din ne kuwa da gaske."

"Nine Malam." Yace yana murmushi

"Toh muje ko? Naji kana nema na." Yace yana kallon Malam bahaushe da yadda yake dubansu su dukka, sai yace

"Oga Sir wannan tsohon member ne na gidan nan kila ka manta shi kasan yaran da yawa."

"Ina wuni?" Sultan ya gaishe shi a gajarce ganin yadda yake kallon sa, be ji ya amsa ba har suka bar wajen suka nufi wata bishiya a chan k'asan gidan shi da Malam Bako.

"Karka ji nace kana nema na bayan nasan ba neman nawa kake ba, Aziza kake nema ko? Ita kake zo gani?"

"Aziza?" Ya ambata da sigar tambaya

"Maman Yara toh, da haka ka santa ko?"

"Eh malam, sai dai alamu sun nuna bata gidan kamar, yadda naga abubuwa da yawa."

"Ai ta dade da barin nan din, kuma dama tace min zaka zo nemanta wataran, ta kuma ce na baka wannan."

Sai ya ciro wata envelope a rufe ya mika masa yasa hannu ya karba yana jujjuyata a hannun sa.

"Amma mesa tabar gidan nan?"

"Toh ba zan ce kai tsaye ga dalilin barin nata ba, abun dai da alama daga sama ne, haka mu ma kawai muka tashi da maganar tafiyar ta, kuma bamu san ainihin abinda yasa tafiyar ba, sai dai mun san tafiyar ba ta dad'i bace duba da yadda tazo katsaham, a ranar kuma aka maye gurbi da Malam Bahaushe kamar yadda ka gani, amma ko shi baban naku (Daddy) ya san dalilin hakan, duk kuwa da har yanzu komai na gidan yana hannun sa ne."

"Toh nagode Malam, bari na tafi." Ya mike yana saka hannu a aljihu, ya ciro kud'i masu dan kauri ya mika masa, gashi Malam ko akwai abinda zaà yi wa yaran dasu."

"A yayi Albarka." Yace yana saka hannu ya karba, sannan sukayi sallama ya tafi.

Mubarak na ganin shi ya taso daga chan inda ya samu ya zauna yana jiran sa

"An dace?"

Girgixa masa kai yayi suna nufar motar

"Bata gidan, sai dai ta bar min sako."

"Ok." Yace sannan yayi ma motar key suka bar wajen.

    A asibiti ya ajiye shi ya shiga ciki shi kuma ya wuce domin shiryawa ya tafi wajen aiki. Takawa ya shiga yi har ya dangana da babban office din MD, yana zuwa shima yana isa kusan a tare ma suka je, hannun sa ya kama suka shiga office din yana amsa gaisuwar sa. Ya jima sosai a cikin office din sannan ya fito ya tafi.
State Library ya wuce daga nan, still takardar sa na makale a hannun sa, sai daya shiga ciki, chan inda babu hayaniyar komai ya zauna sannan ya soma bud'e takardar a hankali har ya gama warwareta baki d'aya.

_"A lokacin da zaka riski sakon nan nawa, na tabbata da nai maka nisa, bana so ka nemi ne dan ba zaka same ni ba,ban sani ba ko watarana, idan da rabon mu gana,akwai abubuwa da yawan gaske da nake son sanar dakai amma babu hali, sai dai sunayen mutanen nan zai taimaka maka k'warai wajen samun haske a abinda ka saka a gaba, inayi maka fatan alkhairi a koda yaushe."_
Sunaye ne a rubuce da babban baki, kowanne yana nuna arrow zuwa na gaba, sai dai dukkansu akwai tazara me yawa a tsakanin kowannen su. Sunan d'aya ne ya dauki hankalin sa sosai ganin shi har da address a rubuce a jiki.

*_Safiyanu Madaki_* yayi maimaita sunan ya sake maimaitawa kamar me son tuno wani abu, biro yasa ya zagaye sunan sannan ya nannade takardar ya tura ta a aljihun sa ya fito daga wajen.

***
Kallan jikin card din take tana kallon hanya, suna zuwa address din ta biya me adaidaita sahun kudin sa suka nufi building din, kan Aysha a daure yake da al'amarin Ammi ta kasa gane abinda suke nema wajen mutumin da kallo d'aya zaka yi ma gidan sa ka san ba karamin mutum bane, yau rana ta uku kenan suna sintirin zuwa amma yaki ganin su, amma basu daina zuwa ba, gashi gaba daya Ammi ko sana'ar ta ta, ta daina a kwana ukun nan haka suke fama da kansu sai dai ko k'ad'an bata nuna damuwar hakan ba, damuwar ta, tafi ga yadda zasu yi suga mutumin nan wanda yau kafin su fito Aysha ta sanar ma Muhammad abinda ke faruwa dan shi be san komai ba kuma Ammin taki sanar dashi.
Da kallo me gadin ya bisu dan ya gane su sarai a kwana biyun da suka zo, sai dai yau ba kamar wadanchan ranakun biyu bane, yau suna zuwa ya taso ya bude musu kofa sannan ya basu wajen zama, ya shiga ciki. Jim kad'an sai gashi ya fito ya koma wajen zaman sa yana kad'a kafarsa, suna zaune basu ce masa komai ba har zuwa sanda wayar sa tayi k'ara, ya d'aga da sauri sannan ya taho wajen su.

"Ku taho." Yace

Da sauri suka bi bayan sa, har zuwa wani katafaren fargajiya wadda ke cike da shuke shuke, ba zaka taba zata akwai mutum a wajen ba, yana zaune bayan sa na fuskantar su, suka zagaya suka zauna a wasu kujeru guda biyu da aka ajiye a gabansa. Waya yake k'asa k'asa be dago ba balle ya amsa sallamar da Ammin sukayi masa, sai da ya kashe mintuna masu yawa yana wayar sannan ya dago yana duban ta, duba irin na tsanaki me tattare da ma'anoni masu yawa.

"Safiya?" Yace yana kad'a kansa.

"Kina da naci da yawa, kwana uku kina sintirin zuwa, na dauka da kika zo sau biyu zaki hakura, ashe zaki dawo, kina nan da halin ki na juriya da naci a komai."

"Naga Mahdi, na ganshi a kasuwa kuma ya ganni, kuma kasan hakan me yake nufi ko?"

Sai ya kafe ta da ido kamar me nazari, sai kuma ya mike da sauri ya na danna wayar sa

"Da yaushe kika ganshi, a wanne irin yanayi da kuma lokaci, sannan kin tabbata be bi ki yaga inda kike ba?"

"Wacce tambaya zan amsa a ciki, bayan tsawon lokacin nan rashin amsa daga gareka ya hanani cika burin Maimartaba."

"Hello Musa." Yace yana fita daga wajen da sauri. Ajiyar zuciya Ammi ta sauke taki yarda su hada ido da Aysha.

"Ammi... Wai me yake faruwa?"

"Yanzu ba muhallin tambaya bane Aysha, ki nutsu."

Shiru sukayi dukka, sai gashi ya dawo ya zauna yana ajiye wayar

"Karki damu komai zan san yadda zan yi."

"Ina yake?" Tace masa kai tsaye

"Baki yarda da cewa zan yi abinda ya dace ba? Baki yarda dani ba?"

"Na yadda da kai a dah amma banda yanzu, na yarda da kai har na baka amanar abinda yafi komai muhimmanci a gare mu baki daya, amma me kayi? Ka ha'ince ni ka kuma barni da kaina bayan kasan bani da kowa."

"Safiya!?" Yace yana kallon Aysha

"Safiyanu Madaki!" Ta ambata muryar ta ras, da wani irin mamaki yake duban ta, kai tsaye babu ko sakayawa? Lallai Safiyya ta shirya tunkarar sa.

"Me kike so nace miki? Baki yarda da abinda nace miki shekarun baya ba? Da kafafuwansa zai kai kansa, ranar da dukkan abinda ke lullube a cikin zuciya zai bayyana, ranar na zuwa, nan kusa."

Mikewa tayi tana girgixa kanta

"Ka bamu sabon wajen zama, sannan ga yarka nan na kawo maka." Ta nuna masa Aysha tana kauda kanta. Da sauri ya mike har yana ture kujerar da yake kai.

"Kina nufin?"

"Yarka ce, cikin da ka barni dashi kenan, ban sanar dakai ba sai dan sanar dakai din bashi da Amfani, sai dan sanin kai din waye da yadda ka dauke ni."

Sai ta juya wajen Aysha da ta sandare tana duban wanda aka kira da mahaifin ta

"Kiyi hakuri Aysha, wannan shine mahaifin ki da kike son gani, bayan auren mu da watanni uku ya sakeni."

Duban sa tayi, babban mutum me ji da kudi da aji, sai ta kalli Ammin, bata sani ba ko wahala ce ta maida ta haka, amma sai taga sam babu gamin hadi ita da mutumin da ta kira da mahaifin ta,ya ninka ta a komai nesa ba kusa ba, toh kenan idan har sunyi aure akwai dalilin da yasa sukayi auren kenan? Har da zai sake ta a wata uku kachal?"

"Aysha...?" Ya kirata da muryar sa da ta ji tana mata amsa kuwwa a kunnen ta.

"Aysha... Kiyi hakuri ki yafe min " Yace yana matsawa daf da ita,

"Mahaifiyar ki ita ta hana ni sanin ki balle har nayi miki abinda uba ya kamata yayi, saboda wani laifi da take ganin nayi mata wanda sai nan gaba kad'an zata gane."

Shiru tayi tana sauraron sa har ya gama maganganun sa da bata gane komai a ciki ba, ita Ammi na gefe bata tanka musu ba har ya gama sannan ya dauki waya yayi magana, yana gamawa yace

"Ku je ku shirya dan Allah Safiyya, sabon gida zaku koma."

Bata ce komai ba taja hannun Aysha dake ta faman waigen mutumin da aka kira da mahaifin ta, har suka gama ficewa daga wajen sannan suka fito bakin titi suka hau abin hawa.

"Ammi dan Allah?" Tace tana marairace murya ganin sun kusa zuwa gida

"Ki bari muje gida."

"Tohm." Tace taja bakin ta tayi shiru.

Suna zuwa suka hau had'a kayansu waje d'aya, duk abinda Ammi take sauri sauri take yi,suna cikin hadawa Muhammad ya dawo, ya tsaya yana kallon su.

"Ammi?"

"Muhammad babu lokacin doguwar magana, barin gidan nan zamuyi idan muka koma inda zamu koma zan fad'a muku komai, har ma da abinda nake boye muku, kafin lokaci ya kure min."

Bece komai ba, shima sai yasa hannu ya taya suka karasa hadawa, sannan suka zauna zaman jiran wanda zai zo su tafin kamar yadda Safiyanu Madaki yace. Sauran yan gidan Ammi tasa suka je sukayi wa sallama, sai duk suka nuna rashin jin dadin tafiyar da zasuyi haka da wuri haka.
Chapter 42 · 0% Book details