Sashe 44
Abinda Ke Cikin Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Ok ba damuwa." Yace sannan ya karanto masa numbers din ya saka a wayar sa, ya kira back shima ya gani yayi saving da Ameer Madaki, shi kuma ya tambaye shi da me zai saving yace masa Sultan. Da haka suka rabu sai da Ameer ya ga fitar motar sa daga layin su sannan ya ja tasa ya shiga gida. For the first time a rayuwar sa yau ya hadu da wanda yaji yana so ya zama role model dinsa, tun be kai ga sanin sa ba amma yaji yayi masa, shigar sa, nutsuwar sa, gayun sa, kai hatta tafiyar sa akwai wani strange abu a cikin ta ,uwa UBA maganar sa da tafiyi masa kama da ta sarakuna ko wasu manya manyan masu kud'i dai, shi dama a rayuwar sa yana son gayu da fame, yaso fara waka Daddy ya hanashi amma da tuni shima wani big time celebrity ne yanzu.
***
*Amrah*
***Babu abinda aka fasa na shirye shirye, musamman bangaren Mah-Mah da tafi kowa murnar auren, sosai take shiryawa ranar tana kuma gayyatar duk wani na kusa da ita har ma dana nesa. Kwana biyu da bata ga Sultan ba sai ta d'anji babu dad'i, kenan fushi yayi dan ta masa fad'a, ita a ganin ta ai ba laifi bane dan uwa ta nuna wa d'anta kuskuren sa, abinda tasan kawai taji babu dad'i da fad'an nata ya chanja salon da ba wai ta shirya da zuciyar ta akanta fadi hakan ba, sai dai bacin rai ne tasan ya kwashe ta, ta farfada masa abinda ta fad'a din duk da a ganin ta shine yayi abinda ya tunzura ta.
Har daki ta samu Safwan da tambayar ko ina Sultan din, yace mata yana asibiti ne, hankalin ta ya kwanta suka cigaba da shirye shirye hankali kwance.
A bangaren Amarya Amrah ma shirye-shiryen na tafiya daidai a wajen kowa amma banda ita da umma, har ga Allah umma bata son auren sai dai Abba yaki bata hadin kan da zai taimaka wajen ganin an fasa, maganar sa daya ce Hajiya tafi komai da kowa a wajen sa, dole taja bakin ta tayi shiru kuma ta cigaba da kokarin kwantar wa da Amrah din hankali tana nusar da ita muhimmancin biyayya ga iyaye.
A haka aka shiga satin biki, idan kaga Amrah zaka dauka ciwo ta kwanta ta tashi saboda yadda ta lalace, duk da gyaran jikin da take samu amma be boye damuwar da take ciki ba, auren wanda baka so masifa ne sai wanda ya taba shiga irin yanayin sannan ne zai fad'a maka yadda yake. Sukuku takeyi komai, yawancin abubuwan ma sai dai tabi Afrah da kallo idan tana yi, dama ita ba kawa ce da ita ba, sai cousins su ne akan komai.
Tun ranar da abin ya faru bata sake saka both Sultan da Safwan din a idon ta ba, babu wanda itama kuma tayi yunkurin nema, ta kan ji wani lokacin suna magana da Afrah ko a waya akan abinda zasu bukata.
Ranar laraba me kunshi tazo tayi musu rantsattsen hadadden kunshi, sosai kunshi yayi kyau a hannun Amrah, sai dai ita ko k'ad'an bata ga hakan ba, da an bi ta ta ma babu wani kunshi da zatayi, dan dai anfi karfin ta ne kuma Umma tace ta bar komai a hannun Allah ta cigaba da addu'a zai kawo mata mafita, idan Safwan mijinta ne dole ne ayi auren idan ko ba mijin ta bane ko da duk duniya sun taru akan son suyi aure ba zai aureta ba. Hakan yasa ta dan kwantar da hankalin ta amma ba wai dan ta hakura ko tana son shi ba.
Kamu kawai sukayi washegari dan yadda ta kafe babu abinda zaà yi, yan uwan umma suka ce dole ne ayi kamu al'adace dangin ango zasu zo. Amma kuwa har aka gama kowa ya watse bata bar kukan da take ba wanda mutane da yawa sun zata ire iren kukan da Amare sukeyi ne, akayi ta bata baki, wanda kuma suka san dalilin kukan nata basu ce komai ba har aka gama.
Daki ta shiga ta kulle ta hau cire komai tana wurgi dasu, kafin ta dire akan guiwar ta tana jin wani irin zafi,shikenan daga gobe komai ya kare, tasan ita da rayuwar farin ciki har abadah. Babu abinda zuciyar ta bata sak'a mata ba, har sai da taji kamar ta had'a kayan ta, ta gudu ta shiga duniya amma ba zata iya ba, she's still young and naive bata san takamaimai ma me zatayi ba, haka ta zauna tayi ta kuka har sai data ji idonta na mata yaji yaji, sannan ta shiga toilet tayi alwala taxo tayi sallolin da suka tsere mata dan lokacin wajen karfe sha biyun dare, ta kwanta lamo tana tausayin kanta.
***Matsanancin ciwon kai ke damun sa har baya gani sosai, ya matsa ma kansa sosai da tunanin abubuwa da yawa, gashi ya kasa samun ganin Safiyanu Madaki har yanzu idan ya kira maigadi sai yace be dawo ba, dole ya hakura ya jira dan be san ta inda zai fara ba bayan shi. Yana kwance yaji alarm din da yasa ya kad'a, ya tuna da wayar da sukayi da Daddy jiya akan lallai ya ganshi a wajen daurin auren,ko dai Daddy be fad'a ba ai ya zama dole ya je ko da baya cikin garin ne balle, dan ma Allah ya taimake shi Safwan ya rufa mishi asiri yace ma Daddy din abu ne ya rike shi a asibiti da sai ya kawo wani abu wanda baya fatan hakan.
Da k'yar yasa hannun sa ya dafa ya tashi, ya shiga toilet yayi wanka ya fito ya shirya cikin normal kayan sa ya nufi gida.
Wajen dukka abokan su sun hallara, har da ma wanda suka zo tun jiya aka sauke su a wani gidan Daddy, anan angwayen suke saboda haka kai tsaye chan ya nufa, suna ganin sa sukayi masa cha kowa na fad'an abinda yake son fad'a. Wani ya kalle shi yace
"Amma wallahi ban taba ganin d'an rainin wayo irin ka ba, auren ma sai ka yi masa yanga?"
Karaf Safwan yace
"Babu ruwanku da shi,daga zuwan sa kun sashi a gaba, haba dan Allah."
"Muje ciki kaga kayan da na zaba mana." Yace yana jan sa suka shiga ciki suka bar sauran kowa na fad'ar albarkacin bakin sa.
Kaya ne iri daya, farar shadda da akayi ma dan ubansun aiki a jiki da wani bakin zare me kauri, sai takalma sau ciki bakake masu kyau da suka haska fatar su dukka, dinkin manyan riguna ne, kuma dama tun da dadewa sukayi wa kansu alkawarin duk ranar auren su idan ya zama ba tare za'a yi ba toh kaya iri daya zasu sa.
"Sunyi kyau sosai." Yace yana dagawa.
"Yauwa ka shirya bari naje waje, kayi sauri amma kaga lokaci."
Daga masa kai Sultan yayi yana jin dadin yadda yaga Safwan din, da alama yana murna da wannan ranar, kuma alamu sun nuna ya samu sauki sosai bayan da ya tafi. Kayan ya dauka ya hau sawa yana kokarin kore tunanin dake neman kutso masa a daidai lokacin wanda sam be kamata yayi ba. Ita din yanzu ta zama matar dan uwa kuma amininsa, babu wani abu da ya rage tsakanin su sai matsayin ta na matar Safwan dinsa. Yaso ya kara ganin ta bayan ranar ko sau daya ne suyi magana ya yi kokarin sake fahimtar da ita, amma yadda abin ya kasance ne ya hanashi dan baya son Safwan yayi tunani irin wanda Mah-Mah tayi, ko kuma mutane suyi masa wani kallo na daban ko maci Amana ko wanda be san alkhairi ba.
"Ina miki fatan alkhairi da zaman lafiya me dorewa."
Ya furta a hankali sannan ya fito suka dunguma zuwa masallacin dake kusa da farkon shigowa layin nasu.
*** Yadda wajen ya cika sosai zaka tabbatar da ba karamiin tara mutane daurin auren yayi ba, waje waje suka dinga bi suna gaisawa da mutane, suna ji aka fara gabatar da abinda ya tara mutane.
Gefe Sultan ya koma da sauri ya ciro wayar sa dake ta faman ringing be ji ba, Madaki's Gateman ya gani a rubuce, da sauri yabi kiran yana dagawa yace
"Lafiya Babah? Ya dawo?"
"Ya dawo jiya da daddare, kuma yau ina ganin ya sauko na isar da sakon ka, sai naga har ya fika son haduwa da kai dan cewa ma yayi na kiraka a lokacin ka fadi inda kake shi zaizo sai kuma aka yi rashin sa'a kiran be shigo ba, sai yanzu ya saka na sake kira da baka daga bane ya bar wajen nan ya koma ciki."
"Alhamdulillah, bari na tawo yanzu." Yace yana jin wani irin karfi, karfin tunkarar komai da zaizo masa. Kallon wajen yayi yaga hankalin Safwan na chan, yayi saurin fita daga wajen da sauri ya fad'a motar sa yayi reverse ya bar wajen.
A daidai lokacin,limamin masallacin ya sanar da dauruwar auren Muhammad Sultan Da amaryar sa Amrah.
_ZAFAFA BIYAR 2021_*🔥
_*SUKAR BAYA*_💚
_BILLYN ABDUL_
( _kwai cikin qaya_ )
( _raina kama_)
( _wutsiyar raqumi_ )
*_SIRADIN RAYUWA_*💛
_SAFIYYA HUGUMA_
( _alqawarin Allah_ )
( _daurin boye_ )
( _Dangantakar zuci_ )
💙
_*KIBIYAR AJALI..*_💜
_MISS XOXO_
(Sulke baya tsare ta sai ta wuce)
( _Igiyar zato_)
( _Kaimin halacci_ )
( _Naufal_ )
*_ABIN DAKE CIKIN ZICIYA_*🧡
_HAFSAT RANO_
( _ruhi daya_ )
( _Sauyin qaddara_ )
( _Daurin goro_ )
*_MIN QALB_*❤️
_MAMUHGEE_
( _buri daya_ )
( _tarayya_ )
( _eznah_ )
Duka BIYAR 5 zaku samesu akan garabasar naira 700 kacal,
Guda hudu 4 Kuma 500,
Guda uku 3 Kuma 450,
Guda biyu 2 Kuma 400,
Guda daya akan 300.
Ma'ana
Each one is 300
2 is 400
3 is 450
4 is 500
5 is 700
Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇
ACCOUNT NO- *0812652655*
ACCOUNT NAME- *HAFSAT LAWAN GAMBO*
BANK NAME: *ACCESS BANK*
saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇
0903 234 5899
IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇
09033181070
Karku Bari ayi Babu ku domin wannnan salon na daban ne
SABUWAR SHEKARA
SABON SALO
TEAM#ZAFAFABIYAR🔥[4/7, 6:44 AM] Maman Maryam: www.instagram.com/zeeherbalsaphrodisiac.
_*ASSALAMU ALAIKUM SISTERS..!_*