← Book details Abinda Ke Cikin Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 96 OF 108

Sashe 96

Abinda Ke Cikin Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"La'ila!" Tayi maganar tana kunshe dariyar ta, kicin-kicin yayi da fuska, zai yi magana yaji tahowar Ummin tana maganar da wata mai aikinta. A zabure ya mike, ya sakko ya tsaya daga chan gefe kamar munafiki, turo kofar tayi hannun ta dauke da madara me zafi, kallon sa tayi, yadda yayi firit da fuska , dariya ya bata ta shiga yi tana matsawa wajen Amrah da take tayata a hankali tana satar kallon me bakin maganar kamar an saka abu an rufe bakin kuma, har wata nutsuwa ya kara a gaban Ummin yana sunne kai.

"Zo Sultan." Ta yafito shi bayan ta zauna a gefen gadon, yazo ya zauna ta dora kansa a saman kafadarta, ta rufe idon ta kwalla na taruwa sosai a idon ta.
Sun dade a haka, sannan ta fita ta barsu a dakin tana jin wani iri, tunanin yan uwanta da garin su da komai nata ya dawo mata sabo fil.

Ummi na fita ya janye bargon, ta shiga ja yana ja

"Yarinya kin zata ke kad'ai take so?"

Bata ce komai ba don taga take taken sa.. .

***Pls wadda tasan ingantaccen maganin ciwon ido irin wanda mura ke sawa, da mura irin me kama makogaro da saka kaikayin makogoron pls tayi min magana pc. Note banda maganin asibiti pls 😭😭😭 irin remedies haka na gida pls nagodeAbinda Ke Cikin Zuciya

Page 51

ZAFAFA BIYAR NA KUDI NE!!!

Tana kwance a dakin da yafi mata kama da aljannar duniya, ta kudundune a cikin bargo saboda sanyin da take ji, tafiyar Gimbiya kenan daga wajen ta sun dade suna hira itace ma gyara mata kai da kanta suka kuma ci abinci tare. Ita ta kwanta ita kuma ta fita domin kawo mata wata madara daga dakin ta.
   Kansa ya fara lekowa ya tabbatar bata ciki, dan idan yazo kora shi Gimbiyar keyi wadda a yanzu Amrah ta saka mata suna Ummi.
  Da karfin sa ya shigo ganin bata nan, ya lallaba ya shiga bargon, da sauri ta zabura zata mike, ya saka dukkan hannun sa ya danne ta,

"Wa na kama?" Yayi maganar yana bata fuska.

"Ka daga ni."

"Anki, wai ni kike ma wannan shan kamshin don kinzo wajen Ummi ko?"

"Ni fa ba shan kamshi nake ma ba."

"Menene Toh? Kinsan yadda na shirya ma zuwa kasar nan kuwa?"

"Please ka daga ni wallahi kayi nauyi."

"Anki din, sai Ummi tazo."

"Ummin?" Ta rufe baki cike da mamaki

"Eh ai ba kunyar ta nake ji ba."

"Tab lallai, babu ruwana wallahi."

"Ni da ruwana, an maida mutum marayan karfi da yaji."

"La'ila!" Tayi maganar tana kunshe dariyar ta, kicin-kicin yayi da fuska, zai yi magana yaji tahowar Ummin tana maganar da wata mai aikinta. A zabure ya mike, ya sakko ya tsaya daga chan gefe kamar munafiki, turo kofar tayi hannun ta dauke da madara me zafi, kallon sa tayi, yadda yayi firit da fuska , dariya ya bata ta shiga yi tana matsawa wajen Amrah da take tayata a hankali tana satar kallon me bakin maganar kamar an saka abu an rufe bakin kuma, har wata nutsuwa ya kara a gaban Ummin yana sunne kai.

"Zo Sultan." Ta yafito shi bayan ta zauna a gefen gadon, yazo ya zauna ta dora kansa a saman kafadarta, ta rufe idon ta kwalla na taruwa sosai a idon ta.
  Sun dade a haka, sannan ta fita ta barsu a dakin tana jin wani iri, tunanin yan uwanta da garin su da komai nata ya dawo mata sabo fil.

Ummi na fita ya janye bargon, ta shiga ja yana ja

"Yarinya kin zata ke kad'ai take so?"

Bata ce komai ba don taga take taken sa, ta mike zata bar dakin ya saka mata kafa ta fado kansa,

"Ouch." Tace tana mulmula goshin ta

"Raguwa, kin gama shan kamshin?"

"Um um."

"Oya fad'a min, me Ummi take baki? Mene wannan?"

Ya nuna cup din madarar

"Madara ce."

"And?"

"Ba komai, just milk."

"Ban yarda ba, lemme check."

Zaunar da ita yayi, ya dauki cup din ya kai bakin sa ya sha, ya lumshe idon sa gardin madarar na ratsa shi.

"No wonder kika makale anan, ashe kayan dadi kike kwasa kika bar ni ina chan ina chan ina shan wuya."

"Wuya?"

"Eh mana, can't you see how badly I'm missing you? Ban taba ganin ango iri na ba, Allah sarki ni."

Dariya tayi, ta karbe madarar ganin sai sha yake, ta sha dan ba karamin dadi madarar tayi mata ba. Tallafe kansa yayi da hannun sa, ya lula a duniyar tunanin maganganun da Maimartaba yayi masa dazu, har ta gama ta tashi ta wanko bakin ta, ta dawo be sani ba, sai da ta zauna sosai ajikin sa sannan ya dube ta, yayi mata murmushi me kyau, ya kwanta akan bayan sa, ta dora kanta a saman chest dinsa.

"Na damu sosai, ina tsoron yadda Safwan zai karbi maganar nan Amrah."

"In sha Allah abinda kake tunani ba zai faru ba, in Sha Allah."

"I hope so, amma gaba daya hankali na a tashe yake, ko Daddy ya sanar wa Mah-Mah?"

"Komai zai zo da sauki, in Sha Allah."

"In sha Allah."

A tare suka fito, bayan Ummi ta aiko an kirasu, tare suka ci abincin daren, duk yadda Amrah take cike da matsananciyar kunya amma haka ta daure suka yi suka gama sannan suka zauna akayi hira wadda bata iya saka baki sai murmushi kawai.
Maimartaba ne ya fara yi musu sallama ya tafi ya kwanta saboda yana bukatar hutu,chan Amrah ma tayi musu sallama saboda taga hirar akan rayuwar Sultan din ce da Ummin ke ta yi masa tambayoyi yana bata amsa, tasan suna bukatar kasancewa su biyu shiyasa kawai ta tafi, ta dauki wayar ta tayi logging whatsapp suka shiga hira da Afrah tana bata labarin abubuwan da suka faru. Jin an taba kofar ne ya saka ta saurin kifa wayar ta rufe idonta pretending kamar bacci take, tana jin sa ya shigo, ya wuce kai tsaye toilet ya watso ruwa ya fito, ta bud'e idon ta kad'an ta kalle shi, yana tsaye daure da towel iya kugu, yana goge kansa, da sauri ta maida idon ta rufe zuciyar ta na bugawa da sauri. Tana jin sa ya hawo gadon, tayi tunanin sai matso kusa da ita ya kwanta sai taji ya kwanta a gefe ya dora kansa a saman sangalalin hannun sa, ya kurawa saman dakin ido, ji tayi babu dad'i, tasan tunani yake tayi bacci shiyasa, bata so taga yana tunani haka, duk sai taji babu dadi da gaske. Suna kwance a haka kowannensu ba bacci yake ba sai dai shi Sultan be san idon ta biyu ba. Motsi tayi kad'an ya kalli wajen da take, idon ta a bud'e take kallon sa ta dan hasken da yake shigowa dakin.Kafin yayi magana ta mirgino ta dora kanta a saman hannun nasa itama, yayi mata murmushi ta mayar masa.

"Na zata bacci kike ai."

"Um um, ido na biyu."

"Me kike? Tunani?"

"A ah, chatting muke da Afrah."

"Don't tell me idon ki biyu sanda na shigo, you pretend kamar kina bacci amma?"

"Na zata ka gane ni ai."

"Um um, da gaske na dauka bacci kike, ashe wayo kikayi min."

"Toh ba kaine ba."

"Ni kuma? Ya Allahu, me nayi dis time Kuma?"

"Ba komai."

"Sai kin fad'a min, or else?"

Yayi maganar yana juyowa suna facing juna

"Me?" Ta tambaya tana dan matsawa

"I'll hug you, I'll kiss you and..."

"I'm sorry." Tayi saurin cewa tana kokarin tashi. Dariya yayi sosai yana maida ita

"Allah kin cika tsoro."

"Na daina."

"Toh naji, muyi bacci, let pray sai kowa ya rufe idonsa and we sleep, shikenan?"

Daga kanta tayi, suka karanto addu'ar kwanciya bacci a tare, suka tofa a ko ina sannan suka kwanta.
Da safe suka tashi suka shirya sannan tace ya fara fita dan ita bazata iya jerawa tare dashi ba, dariya yayi mata ya fita, sai da ya dade da fita sannan tayi shahada ta fita, babu kowa a falon alamun ma masu gidan basu tashi ba, shi kad'ai ne a falon yana waya, bata zauna ba sai kawai ta koma daki ta zauna, chan ta sake dawowa ta tambaye shi Kitchen lokacin ya gama waya, ya nuna mata ta tarar da masu aiki ne a ciki suna ta kokarin had'a breakfast, ita ta karba ta tsaya akai suka had'a hadadden breakfast wanda tasan zai farantawa in-laws din nata rai.
Sai chan Ummin ta fito, Sultan lokacin yana dakin Baban, tayi ta shiwa Amrah albarka bayan masu aikin sun fad'a mata abinda tayi, amma tace karta sake ta bar su suyi aikin su ne, bayan haka ma idan suka koma Masarautar dole ta hakura da komai.
Ita dai Amrah taji ne kawai, girki passion dinta ne saboda haka ko ina ta samu kanta zatayi shi da farin ciki dan yana cikin abinda yake sata nishadi.
Tare suka fito Baban ya shirya tsaf, yayi shigar manyan kaya, sosai ya fito a ainihin waye shi, duk suka tashi sai da ya zauna sannan suka zauna. Yanzu ma kamar jiya tare sukayi breakfast din, bayan sun gama Sulthan suka fita tare da Baban, su kuma suka zauna a wajen suna hira.
A daidai lokacin Daddy ya gama shiryawa, Mah-Mah ta gabatar masa da abincin sa, sai dai bashi da appetite din da zai iya ma cin abincin, yasan sultan ba wani dadewa zai ba, ya kuma san idan suka dira a k'asar nan komai zai bud'e, baya so ta fara ji a wajen wani shiyasa ya yanke hukuncin fad'a mata kawai, idan yaso sai ya nemi alfarmar Maimartaban akan su bar masa Safwan din dan shi dai za iya cewa ba Mah-Mah kad'ai ba, hatta shi baya iya jin zai dau rashin Safwan din.
A shirye take taci kwalliya sosai, kasancewar ta mace yar kwalisa gashi tana cike da farin cikin samuwar lafiyar Safwan, saurin zuwa asibitin take dan yace mata yana so yaci tuwo shiyasa ta dawo gida tayi masa lafiyayye ta sake shiryawa zata tafi wajen nasa.

"Daddy ga abincin fa, mutumin ka ne tuwo miyar ganye."

"Zanci, amma nafi so muyi magana."

"Magana? Allah yasa lafiya."
Chapter 96 · 0% Book details