Sashe 20
Abinda Ke Cikin Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tun yana hanya yake ta kiran wayar sa amma ba answer,yana zuwa kai tsaye bangaren su ya wuce dan yana da yakinin zai same shi a chan, sai dai yana bude kofar ya ganshi a yashe a k'asa, da sauri ya karasa ya hau jijjigashi, yana kiran sunan sa da karfi, ganin zai bata lokaci yasa ya fita da sauri ya kira wani yaro dake musu aiki ya taimaka masa ya shashi a mota, sannan suka wuce asibiti, suna zuwa aka karbe shi, aka shiga bashi taimakon gaggawa.Mah-Mah bata san me yake faruwa ba, tana chan family house dinsu ana bikin yar cousin dinta, Mubarak ya kirata da wayar Safwan, matsawa tayi daga wajen hayaniya sannan ta d'aga, bata iya karasa jin abinda yake cewa ba ta kashe kiran, tayi saurin kiran Daddy tana jin kwalla na taruwa a idonta, yadda Mubarak ya fad'a mata haka ta fad'a masa sannan tayi sallama da yan bikin bayan ta fad'a musu Safwan ne babu lafiya, addu'a akayi ta masa sannan wata sister dinta ta karbi driving din suka nufi asibitin da wasu daga cikin yanuwan ta, suna tafe tana kuka dan tasan yadda yake jin jiki idan ciwon nasa ya tashi, ya jima rabon sa da ya samu irin attack haka shiyasa ma suka shiga tashin hankalin jin a sume ma aka kaishi asibitin, wajen lokaci daya suka isa ita da Daddy, suka dunguma zuwa dakin da aka bashi hankalin su a tashe, lokacin an samu numfashin sa ya dawo daidai sai dai he's still unconscious, kukan Mah-Mah ne ya karu ganin yadda lokaci daya ya zabge kamar ba shi ba, yana kwance sambal oxygen a makale a saman hancin sa, yanayin yadda girjin sa ke kaiwa da komowa zaka gane ba daidai yake ba, gefen gadonta zauna ta kama hannun sa cike da tausayawa, ko me ya sa shi shiga wannan yanayin ba karamin abu bane.
***Har ya gota su sai ya dawo da baya ganin hausawa ne tun daga yanayin shigar su, daga dan nesa dasu ya tsaya yana kallon babban mutumin dake zaune yana magana da wani, da dukkan alamun yadda yake magana yasan baya jin daidai, wata mace ce babba a gefen sa, tasa doguwar riga ta yane kanta da mayafi sai dai kanta a duke yake a k'asa baka ganin fuskarta, wani abu me kama da mayen karfe yaji yana fizgar sa wajen su, takawa ya shiga yi da d'an sauri ganin suna kokarin barin wajen.
"Babah..." Ya samu kansa da kiran mutumin, chak suka tsaya a tare, suka juyo, matar ta kura masa ido tana jin wani abu na zagaya wa a saman kanta, sunan da yayi amfani dashi yasa fuskar dattijon tayi fadi, ta haska da wani irin murmushi, sai ya dan rissina yace
"Barka da rana Babah, ya jikin?"
Hannun sa dattijon ya kama, ya saka cikin nasa sannan ya girgiza kansa
"Ya akayi ka kirani da Babah? Ko kana neman wani ne?"
Girgiza kai Sultan yayi alamar a'ah, sannan yace
"Zan wuce ne na ganku a zaune, na kuma ji ina son sanin halin da kake ciki, saboda ganin da nayi kuma hausawa ne kamar ni, a kasar da ba tamu ba, nasan watakila akwai abinda zan iya taimaka wa dashi, Babah kuma sunan duk wani babba ne, nasan idan na fadi haka zaku gane saboda ba a kasar da ake amfani da sunan bane."
"Allah yayi maka albarka, lallai iyayenka sun yi kokarin baka tarbiyya, jiki alhamdulillah kasan idan abu ya hada da girma."
"Haka ne, Allah ya sauwake ya kara lafiya, nima ina karatu ne anan bansani ba ko akwai abinda zan iya yi."
Jinjina kai yayi ya sake damke hannun sa, sannan yace
"Zakayi alfarma,ka zo gida?"
"Zanzo Baba, zanzo in Sha Allah." Yace yana murmushi
Sai ya kalli matar cikin tsananin farin ciki yace
"Gimbiya Allah ya bamu d'a."
Sai yaga fuskar ta tana washewa a karon farko tun dawowar su kasar, ta matso sosai sannan ta kama hannun Sultan tace
"Bless you my child."
Murmushin da tayi masa ya tsaya sosai a ransa, ya kasa barin tunanin sa, he feel so attached, yana jin kamar akwai wani abu me karfin gaske tsakanin shi da wadannan bayin Allah, sosai yaga farin ciki a fuskar su da ya nuna sun jima rabon su dashi, address suka bashi, tare da rokon shi akan ya cika alkawari kamar yadda yace zai zo.
Wunin ranar baki dayan ta a tunanin mutanen yayi, daya tsaya da abinda yake fuskokin su zasu fado masa, sai ya bar hakan a matsayin yadda suka yi masa da kuma kasancewar su yan uwansa hausawa kuma yan k'asa daya, shiyasa yake jin kamar dama chan ya sansu. Da haka ya bar tunanin ya cigaba da abinda yake ganin shine daidai.
Yana hanya a cikin mota kiran Daddy ya shigo, ya kalli wayar sai tunanin maganar da Abba yayi masa ta fado masa, ko dai Abba ya kira Daddyn ya fad'a masa abinda yake tsakaninshi da Amrah ne shiyasa ma yake kiran sa yanzu? Sai yaji kunya ta kamashi yayi murmushi yana fatan hakan ya zama gaskiya. Da sallama ya daga wayar, sai dai muryar Daddyn kadai ta sanar dashi akwai matsala.
"Sultan kana ji na? Safwan ne ya samu attack...
"Subhanallahi... Me ya same shi? Garin yaya?" Yace a rude, yadda yayi maganar kad'ai zaka san ya rude iya kar rudewa
"Bamu san me ya faru ba Mubarak ne ya ganshi a sume, kuma Likita yace zuciyar sa ta fara kumbura, komai zai iya faruwa dashi, gashi munyi munyi ya fad'a mana abinda yake damun sa yaki, kayi kokari ka kirashi kaji dan Allah." Ya karashe muryar sa na karaya
"In Sha Allah Daddy, zan kirashi yanzu, ku kwantar da hankalin ku babu abinda zai faru."
"Shikenan Sulthan, Allah sa muji alkhairi."
Da sauri Sultan ya shiga neman Layin Safwan hannun sa har rawa yake, yana dagawa ya rude ya fara masa fad'a ya manta ma lallabashi ya kamata yayi
"Me kake so kayi? Kana so ka kashe rayuka hudu hadda aka? Akan mace? Akan mace? Me yasa Safwan? Me yasa? Na dauka mun gama maganar nan tuntuni, kasan halin da kake jefa zuciyar ka duk sanda irin wannan abun ya faru? Kana rage mata karfin tane."
"Ya zanyi Sultan? A kunnena take fad'a min bata son na, tace ta tsaneni, bata so na ko kasan, bayan bani na sawa zuciya ta son ta ba, da nasan yadda zanyi dana cire son ta daga zuciya ta da nayi tun ranar,i just can't, I love her so much da ni kaina bansan wanne irin so bane."
"Then dolen ta ne ta soka, ko tana so ko bata so sai ta soka Safwan, I can't risk loosing you akan mace, ko wacece yau zan kirata, zan mata magana zan fad'a mata condition dinka."
"Nasan zata amince, karka damu zan yi kokari na kaji, just stay calm ka kwantar da hankalin ka please komai yazo karshe, ka bani number ta da sunan ta yanzu zan kirata ba sai anjima ba."
"Number ta baida amfani ina ganin gwara kuyi magana face to face zaifi."
"Ta yaya zan iya magana da ita face to face Safwan? Ka manta bana nan ne?"
"Kuna tare ai..."
Dam kirjinsa ya buga ya tsaya da tafiyar da yake yi, yace a d'an tsorace
"Muna tare?"
"Eh."
"Bangane ba Safwan,kana nufin itama tana kasar nan kenan?"
"Sultan Amrah ce fa, Amrah ce."
"Amrahhhhhh!" Ya ambata da d'an karfi, da sauri ya jingina da fence din wani gida yana jin hajijiya na neman kaishi k'asa, daga nan be sake fuskantar abinda Safwan yake fad'a masa ba, jin sa da ganin sa ne suka dauke da wani lokaci, komai ya zama baki kirin a gaban sa, da k'yar bayan jin sa ya fara dawowa kàdan kadan yace
"Shikenan zan kiraka." Yayi saurin kashe wayar, tafiya ya shiga yi ba tare da yasan inda yake sanya kafar sa ba, yasan dai ba hanyar gida ya dauka ba sai dai be san ina ya nufa ba, besan me zaiyi a lokacin dan komai ya tsaya masa ne chak, hatta bugun zuciyar sa ya daina bugawa daidai, gani yayi gidajen na koma masa upside down, ganin da gaske zai iya samun matsala idan ya cigaba da tafiya a haka yasa ya samu wajen wasu kujeru ya zauna sannan ya dafe kansa dake masa wani irin sarawa kamar zai rabe da gangar jikin sa..
KUNA BUƘATAR A TALLATA MUKU KAYAN SANA'ARKU A PAGES ƊIN BOOKS ƊIN ZAFAFA BIYAR 2021?.
To kuzo ga dama ta samu💃🏻💃🏻.
Ina ma'abota son a tallata musu hajojinsu a kafafen yanar gizo suke?.
Tofa kuzo dama ta samu, dan jerin gwanon haziƙan marubanku ƴan biyar sun fiddo muku da hanyar da kuma kasuwancinku zai zagaya lungu da saƙo ta dalilin shafukan littatafai.
Ga duk mai buƙatar a saka masa tallan kayan sana'arsa a shafin littatafan mu na zafafa biyar zai iya tuntuɓar waɗan nan Numbers 0903 234 5899 or 09033181070 ta WhatsApp, idan har agama buks ɗin kana buƙata a sakamaka talla zamu saka maka akan farashi mai sauƙi. Idan kuma wasu adadin pages kake buƙata koda ɗaya ne duk zamu saka maka akan farashi mai sauƙin gaske🤓.
Kuyi maza ku kawo, mai haja shike talla, mai saya kuwa shike neman sauƙi😻😻😄🤗.
______________________
_ZAFAFA BIYAR 2021_*🔥
_*SUKAR BAYA*_💚
_BILLYN ABDUL_
( _kwai cikin qaya_ )
( _raina kama_)
( _wutsiyar raqumi_ )
*_SIRADIN RAYUWA_*💛
_SAFIYYA HUGUMA_
( _alqawarin Allah_ )
( _daurin boye_ )
( _Dangantakar zuci_ )
💙
_*KIBIYAR AJALI..*_💜
_MISS XOXO_
(Sulke baya tsare ta sai ta wuce)
( _Igiyar zato_)
( _Kaimin halacci_ )
( _Naufal_ )
*_ABIN DAKE CIKIN ZICIYA_*🧡
_HAFSAT RANO_
( _ruhi daya_ )
( _Sauyin qaddara_ )
( _Daurin goro_ )
*_MIN QALB_*❤️
_MAMUHGEE_
( _buri daya_ )
( _tarayya_ )
( _eznah_ )
Duka BIYAR 5 zaku samesu akan garabasar naira 700 kacal,
Guda hudu 4 Kuma 500,
Guda uku 3 Kuma 450,
Guda biyu 2 Kuma 400,
Guda daya akan 300.
Ma'ana
Each one is 300
2 is 400
3 is 450
4 is 500
5 is 700
Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇
ACCOUNT NO- *0812652655*
ACCOUNT NAME- *HAFSAT LAWAN GAMBO*
BANK NAME: *ACCESS BANK*