Sashe 70
Abinda Ke Cikin Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Me kike har yanzu bakiyi bacci ba? Are you thinking about me?"
"A ah ni sallah nayi."
"Sai kika kwanta kina tunani na ko? Gani na dawo kin bani warm hug irin na ranar nan ko?"
"Laaa Allah ba haka bane.."
"Toh yaya ne? Uhm?"
"Kawai nazo nan ne Afrah ta tsare wajen kwanciyar, shine na dawo nan dakin, zan kwanta ma kenan ka kira."
"Wow, magana ta, ta fito dai kina missing dina shine kika zo nan, Kinsan akwai unforgettable memories a dakin..."
"La'ilah..." Tace tana danne fuskar ta. Dariya ya saka da dan karfi sai kuma ya rage murya
"That night was one of the best night in my life baby."
Da sauri ta toshe kunnenta, ta kifa wayar tana dariya k'asa k'asa. Sultan zai kashe ta da kunya. Tana jin sa yayi ta kiran sunan ta,taki magana har sai da ya gaji ya kashe wayar bayan yayi mata sai da safe. Tashi tayi tana dan zagaya dakin wani shauki ma kamata,hannun ta, ta harde waje daya tana rufe idon ta na ganin komai, duk da ba zata dorar da komai ba a ranar,amma itama tasan shine best night dinta.
Jona wayar ta, tayi jikin socket bayan ta gama zagayen ta kwanta tana kankame pillow sosai a jikinta. Wani irin bacci me dadin gaske ya dauke ta ba tare da ta shirya masa ba.
***Da yawan su suka zagaye katangar gidan, babban cikin su da wasu su biyu sai matar nan ta dazu data shigo gidan suka saka kai a cikin gidan suna yi suna bud'e kowacce kofa suka tarar har suka dangana da falon gidan. Afrah ce ta tashi firgigit ta waiwaya gefen ta, babu Amrah sai wajen ta, da sauri ta diro daga saman gadon tayi hanyar toilet, ta bud'e da sauri jin motsin na karuwa, bata ciki, da sauri tayi wajen kofa ta saka key sanda taji ana kokarin taba kofar dakin. Kafarta karkarwa kawai take jikinta na wani irin kad'awa da matukar tsoro sanda taji muryar mutane radau a falon suna magana k'asa k'asa. Kuka ne yazo mata tayi saurin saka hannu ta toshe bakin ta tana tunanin ina Amrah taje bayan a dakin ta barta har tayi bacci.
Jin maganganun na cigaba da tashi ta lallaba da sauri ta dauko wayar ta dake k'asan pillow ta shiga kiran Abba,no answer ta koma Kiran Ya Adnan, haka ta dinga bin numbobin kowa tana kira amma babu wanda ya daga. Toilet tayi saurin shigewa ta saka key ta tsugunna a wajen tana kuka da sauri da sauri tana sake kiran numbers din, tun tana kiran number close family har ta koma Kiran na nesa amma babu wanda ya daga.
Ita ko Amrah tayi nisa sosai a baccin ta, baccin da take jin dadin sa sosai suka bud'e dakin, suka shiga, matar nan ta dazu ta matsa gaban gadon bayan daya daga ciki ya haske fuskar amrahn da touchlight me haske sosai.
"Itace?" Ogan ya tambaya
"Eh itace." Ta amsa, gefen gadon ya buga da kafa, hakan ya farkar da Amrah a firgice ta tashi, sai dai hasken da ya haske mata ido yasa ta koma da sauri tana saka hannun ta tana kare wa.
"Who are you?" Tace da karfi tsoro na shigar ta
"Tashi..." Taki tashi
"Tashi!!!" Ya daka mata tsawa,da sauri ta tashi tana saka kuka. Hannu yasa ya finciko ta da karfi, kanta ya bugu da saman gadon ta kwalla wata irin kara saboda zafin da taji.
"Oga maigida fa yace karmu dora mata yatsa fa."
Wani daga bayan sa ya tuna masa deal din.
"Na sani, bana son taurin kai ne."
Ya amsa a dakile,kafin yace
"Wuce muje."
Da sauri ta tashi tana matse jikin ta,tana kuka, har sun fara tafiya ya juyo da sauri
"Hadiye kukan nan stupid!"
Tsit tayi tana jan numfashi, kofar dakin da Afrah take ce ta bud'e ta fito da sauri, tayi wajen Amrah tana kuka sosai, rike junan su sukayi suna kuka Afrah ta shiga basu hakuri
"Dan Allah karku tafi da ita, dan Allah kuyi hakuri."
"Shissh!" Ya dora hannun sa a saman lips din sa.
"Shegiya idan kema baki mana shiru ba sai mun had'a dake, kuma wallahi muka tafi dake sai na yi tasting wallahi."
"Dan Allah ku taimaka mana."
Amrah ta fad'a tana jan numfashi, wani kallon banza ya bita dashi sannan suka kwashe da wata mahaukaciyar dariya.
"Ku ma daina bata bakin ku, kuna hada mu da Allah dan wallahi babu abinda zamu fasa, tafiya zamuyi dake idan kinga kin dawo sai wannan mijin naki yayi mana abinda muke so."
"Wuce muje dallah kuna bata mana lokaci."
Rike ta Afrah tayi, yasa hannu ya fincike ta, ya shiga jan hannun Amrah tana turjewa har harabar gidan inda suka ajiye motar su, yawan su da Afrah ta gani ya kara tsorata kowanne su dauke da zungureriyar AK 47. Tana kallo suka saka Amrah a motar suka tafi da ita. Kamar zata zare haka ta dinga gudu a harabar gidan tana ihu, wanda ya jawo hankalin makota kowa da yayi luf sai da aka tabbatar sun tafi sannan aka shisshigo, wasu mata suka taimaka suka rike Afrah dan ko aina na jikin ta rawa yake kamar mazari.
Da asubah bayan sun tashi sallah Abba ya dawo ya dan kishingid'a a falo yana jin BBC hausa, ya jawo wayar sa zai duba date kawai yaga misscalls din Afrah da mugun yawa, tashi yayi zaune yana ji a ransa ba lafiya ba, yabi kiran zuciyar sa na karyewa. A lokacin Afrah na kwance a gidan makotansu na baya, wayar ta na kan ruwan cikin ta, tana ta kuka kiran ya shigo, ta tashi a zabure ta dauka tana fashewa da kuka.
"Lafiya Afrah?"
"Amma barayi sun shigo sun tafi da Amrah cikin dare."
"Innalillahi wa Inna ilaihi rajiun." Ya mike tsaye jiri na daukar sa. Umma da ta fito da waya a hannun ta tana kallon kiran da Afrah tayi mata, tayi saurin karasowa jin Abba ya rafka Innalillahi.
"Yanzu ke kina Ina?"
"Toh gamu nan." Yace yana ajiye wayar da sauri
"Prof Lafiya kuwa?"
"Babu lafiya Aisha, Innalillahi wa Inna ilaihi rajiun, barayi sun shiga sun tafi da uwata Aisha."
"Innalillahi wa Inna ilaihi rajiun." Umman ta fashe da kuka,
"Na shiga uku, wannan wanne irin tashin hankali ne..."
"Karmu bata lokaci, muje dan Allah."
Da sauri suka fita, lokacin Adnan sun gama waya da Afrah shima ya tawo da sauri suka hadu a hanya, suka dunguma suka tafi unguwar umma na kuka sosai.
ZAFAFA BIYAR
NA KUDI NE:::
Duka BIYAR 5 zaku samesu akan garabasar naira 700 kacal,
Guda hudu 4 Kuma 500,
Guda uku 3 Kuma 450,
Guda biyu 2 Kuma 400,
Guda daya akan 300.
Ma'ana
Each one is 300
2 is 400
3 is 450
4 is 500
5 is 700
Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇
ACCOUNT NO- *0812652655*
ACCOUNT NAME- *HAFSAT LAWAN GAMBO*
BANK NAME: *ACCESS BANK*
saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇
*+234 903 234 5899*
IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇
*09033181070*
Karku Bari ayi Babu ku domin wannnan salon na daban ne
SABUWAR SHEKARA
SABON SALO
TEAM#ZAFAFABIYAR🔥©Hafsat Rano
_Page 33_
***Fitowa yayi jin kamar motsi a falon,hannu yasa da sauri ya toshe hancin sa ganin kwalaben giya baja-baja a tsakiyar falon, idon sa ya sauke akan doguwar kujerar da yake kwance, a matukar buge yake yana magana ciki-ciki alamun baccin ya soma daukar sa. K'asa karasawa Sulthan yayi yadda mamaki ya kamashi, dama dai tun ganin da yayi ma Yariman yasan ba kansa kalou ba yadda yake magana ma, amma beyi tunanin haukar tasa ta kai haka ba. Komawa yayi ya rufe kofar ya kwanta. Be wani yi baccin sosai ma yaji ana kira a masallacin cikin Masarautar, toilet ya shiga yayi alwala ya fara yin Raka'atanul Fajr, ya zauna yana karatun alkurani a hankali, har sai da yaji ana kokarin tada ikama sannan ya tashi yayi Fajr.
Turo kofar akayi, ya tsaya a kofar yana rik'e da kugun sa yana kallon Sultan dake daure igiyar takalmin sa, murmushi ne dauke a fuskar sa yana kallon Sultan din da irin karfin halin sa na shigowa har shashen sa yayi wa kansa masauki. Ya yarda da gayen ba da wasa ya zo ba Amma zai nuna masa ya fishi sanin sarauta da ma bariki gaba daya.
"Ka sauya shawara kenan?" Yace yana sauke hannayen nasa. D'aga kafad'a Sultan yayi sannan yace
"As you can see..."
"Madallah kayi kyaun kai."
"Me kake bukata a wajena?" Sultan yace yana masa kallon cikin ido sosai.
"Bana bukatar komai kamar yadda kai kake bukata a wajena."
"Kamar me kenan?"
"Kana tunanin shiga turakar Maimartaba abu ne me sauki ko?"
"A tunani ba."
"Toh Ba Abu bane me sauki kamar yadda kake tunani, amma zan iya taimaka maka, ka dauki abinda zaka dauka ka bar Masarautar nan idan ka yarda."
Shiru Sultan yayi kamar ba zai ce komai ba, sai kuma ya dubi Yariman yana takowa zuwa gaban sa,
"Inaso na shiga yau da daddare, idan ka shirya sai ka taimaka, ni kuma zan fita kamar yadda ka nema."
"Shikenan, za'a shigo da kayan karin kumallo, sai kaci ya huta zuwa daren, na barka lafiya."
Be jira ta cewar Sultan ba ya ja masa kofar yana wata irin tafiya cike da kasaita. Hannu Sultan ya saka a cikin gashin kansa da ya soma taruwa ya birgita shi yana jin kamar yayi ihu, baya jin dadin jikinsa tun da ya tashi amma zai kokarin karfafa kansa, yaki ne babba a gaban sa da dole sai ya jajirce ya tsaya a kan digadigansa sannan zai yi nasarar sauke mulkin zaluncin da ake a wannan Masarautar.