Sashe 59
Abinda Ke Cikin Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
***Shiryawa yake tayi da sauri da sauri yana dubanta, cup din dake hannun ta take ta faman jujjuyawa ta kasa sha tun da ya fad'a mata tafiyar da zai yi bayan kawo ta da kwana daya tal, yasan dole zata damu, amma ba zai iya bari wannan damar ta wuce shi ba, yaji dadi da ya kira Abba yayi masa iya bayanin da zai fuskanta ya kuma amince xai turo mata Afrah, Hakan ya dan kwantar mishi da hankali.
Yana kama saka kayan yazo ya zauna yana jawo ta jikin shi, ya karbi cup din ya saka mata a baki.
"Kiyi hakuri, kiyi min addu'a kinji, in Sha Allah babu abinda zai faru, ki kula da kanki idan kuna bukatar wani abu ki fad'a ma Adnan."
"Kwana nawa zaka yi?"
"Bansani ba Amrah, bansani ba,Amma zan yi kokari naga na dawo da wuri, for you."
"Shikensn Allah ya bada sa'a ya dawo da kai lafiya."
"Amin matata."
Da hak ya samu ta dan saki jikin ta, ya sake taimaka mata ta sake gasa jikinta sosai ya bata pain reliever sannan yace ta kwanta kafin Afrah tazo. Sai da ta rakashi har gate, yana daga mata hannu tana daga masa ya fice daga gidan. Ciki ta koma tayi kuka sosai har sai da kanta ya soma ciwo.
***
Alhamdulillah, ina yiwa kowa fatan shiga Watan Ramadan lafiya, Allah ya sadamu da duk Alkhairan dake ciki, ya bamu ikon sauke nauyin ibadar yasa muga Daren lailatul Khadr yasa muna cikin bayin da za'a yanta.
Sai Allah ya kaimu Bayan Sallah da rai da lafiya. Ayi ibadah lafiya[5/20, 9:05 AM] Maman Maryam: Hafsat Rano
28
***Ciro wayar sa yayi ya kira, ganin an bud'e kofar gate din yasa ya fito ya rufe kofar ya nufi cikin gidan, gaisawa sukayi da Baba Maigadi ya wuce kai tsaye inda suka hadu ranar, kafin ya karasa isa sukayi kichibis dashi,
"Laaa."
"Kana lafiya Ameer?"
"Lafiya Lou Wallahi."
"Masha Allah, Alhaji na ciki?"
"Eh bismillah." Yayi gaba ya bishi a baya.
Su biyu ne a falon suna magana k'asa kasa, suna ganin shi suka mike tsaye, wanda suke taren ya kafe shi da ido babu ko kiftawa
"Shigo mana Sultan."
"Barka da rana."
"Barka dai, kana lafiya?"
"Lafiya Lou."
Sai suka zauna a kusan tare
"Me za'a kawo maka?"
"Babu komai."
"Ok, abinda yasa na kiraka,akan tafiyar nan ce, sun riga sun san da zuwan ka, saboda haka zamu chanja rana, ko alamis ko asabar, sannan tafiyar ka kai kad'ai ba zata yiwu ba, duba da baka da sani akan hanyoyin shiga Masarautar, saboda haka ga Musa, shine wanda zai jagorance ka a tafiyar."
"Akwai wani abu bayan nan?"
"Akwai, kurkuku me lamba 108 akwai mutane biyu masu matukar muhimmanci a tafiyar nan taka, ka tabbata ka samu ganin su,kayi magana dasu ko da na wssu mintuna ne."
"Sai me?"
"Shikenan ina tunanin, sauran abubuwan idan kaje chan zaka gane."
"Alhamis zamu tafi, ka zama cikin shiri."
"Na barku lafiya."
Yana fita suna shigowa, mace ne da namiji, kallon su yayi çikin wani yanayi, sai kuma ya wuce su da sauri ya fice ganin yadda suma suke kallon sa.
***Mah-Mah bata taba tunanin Sultan zai yi kunnen uwar shegu da maganar ta ba, sai da taji shiru be ce komai ba, be kuma dawo gidan ba balle ta turke shi da maganar, duk da jikin Safwan din da sauki sai dai tasan dauriya kawai yake yana son nuna babu komai bayan ita kuma tasan ba haka bane.
Shiryawa tayi ta shiga gidan su Amrah ranar ta samu Umma ita kad'ai, Amrah na daki Afrah kuma taje gidan Hajiya. Bayan sun gaisa sukayi ma juna Allah sanya alkhairi da yadda al'umaran suka chanja lokaci daya. Bata nuna ma Umman komai ba, abinda taso taji akan Sultan ne amma sai taji Umman bata ce mata komai ba. Suna zaune sai ga Hajiya ta shigo, ranta a bace Afrah na biye da ita tana mata magana. Tashi Umma tayi da sauri tana mata sannu da zuwa ta amsa sannan ta amsawa Mah-Mah gaisuwar da take.
"Kira min Amrah maza." Tace wa Afrah tana samun wajen zama. Tare suka dawo sai a lokacin Amrah ta gaida Mah-Mahn ta zauna a gefen Hajiyar tana tsokanar ta, sai dai ganin kamar ba a mood din wasan take yau ba yasa tasha jinin jikinta.
"Maza kira Mijin ki yanzu yanzu, kice nace yazo ya dauke ki ku tafi, ba zai yiwu ba, a daura miki aure ki cigaba da zama a gida ba, ban yarda da wannan iskancin ba kuma ba za'a yi shi dani ba, kirashi maza."
Sai ta juya wajen Ummah
"Duk laifin ku ne da har kuka yarda,yaran yanzu masu shegen wayon tsiya, sai su auri yarinya su barta a gida sai sun samu abinda suke so sai suce sun saketa, anyi ba daya ba ba biyu ba, nan nan nan wata yarinyar makocin mu akayi mata wannan rashin albarkar, yanzu tana nan ya maida ita karamar bazawara yayi tafiyar sa k'asar waje."
"Gaskiya be kyauta ba."
"Amma Hajiya nace tunda ga ita Maman sultan din, sai kawai ta kirashi idan ya dawo gida ta fad'a masa yazo su tafi, ba wai a kirashi yanzu haka katsaham ba ko?"
"Tace miki itace babar tashi, ko tace miki ta isa dashi ne? Nasan da ita a wajen ai, na ganta kuma amma ba haka nake so ayi ba, ke Amrah, kira shi maza ki bani wayar nan."
"Na tura masa text message zai gani." Tace tana kumbura baki
"Ba zaki kira shi ba kenan?"
"Gashi ma yana kira."
"Bani shi nan."
"Haba Hajiya, haba Hajiya."
"Rufe min baki ba dake ake magana ba uwar iya, ki tsaya auren naki yazo tukunna."
"Salamu alaikum, kana ji, kazo yau ba sai gobe ba, ka tattara matar ka, ka tafi da ita, ba haka ake mu a garin mu ba., Yawwa toh."
Ta sa hannu ta kashe kiran sannan ta ajiye wayar ta tashi.
"Shi kuma idan ya dawo sai ki turo min shi." Tayi gaba suna mata Allah ya kiyaye bata bi ta kai ba tayi tafiyar ta tana sababi.
"Sai ki tayata ku hada kayan." Umma tace tana sauke ajiyar zuciya
"Amma da an bari Abban nasu ya dawo ko?" Mah-Mah tayi saurin fad'a
"Babu abinda zai ce akan maganar mahaifiyar sa."
"Toh ajira Sultan din, yazo tukunna, kila ma akwai abinda zai ce."
"Gwara dai su shirya komai bana son abin magana."
"Bari toh na koma, Allah ya sanya alkhairi ya basu zaman lafiya."
"Amin ya Allah, angode sosai."
Afrah ce ta taimaka ta had'a duk abinda tasan zata bukata waje d'aya, saman gado tayi hayewar ta, ta kwanta tana jin wani yanayi me kama da tsoro tsoro tun bayan da Hajiya ta kirashi, ya kuma yi mata text zai xo idan anyi sallar isha'i. Har akayi magriba ta kasa katubus, ba abu ne me sauki ba barin gida, ka bar iyayenka da yan uwanka ka tafi ka fara sabuwar rayuwa , rayuwar da baka san yadda zata zo maka ba sai ka shigeta, duk kuwa da yadda kaso ka hasaso ta ta wuce nan.
Kamar yadda yace ana idar ta sallar sai gashi, lokacin Abba ya dawo. Kai tsaye falon Abban ya wuce. Tare suka shigo da Umma ta samu gefe ta makale tana jin kamar ace mata k'et ta zura da gudu.
Nasiha me ratsa jiki Abba yayi musu, ya kuma tunasar dasu akan hakkokin kowannen su akan dayan su, ya kuma jaddada musu kalmar nan ta hakuri a zaman aure wanda Idan babu ita, da yawa yawan mutane da basu zauna lafiya ba, daga karshe ya karkare da yi musu addu'a da fatan samun kwanciyar hankali da zaman lafiya a gidan aurensu. Umma ma tayi nata fad'an daidai gwargwado. Kuka sosai Amrah take, kukan rabuwa da iyayenta, fita sultan yayi ya basu waje don su samu damar magana da ita sosai.
Yana tsaye a jikin mota ya jingina bayan sa yana kallon layin nasu da yayi tsit saboda tasowar hadari kasancewar lokaci ne na damuna. Jin an bud'e kofar yasa ya waiga, yana kallon yadda take tahowa hannun ta a cikin na Afrah kanta a lullube da mayafi.
Da sauri ya bud'e mata gidan gaba, ta saka kafarta bakin ta dauke da addu'a,
"Sai da safe Ya Sulthan."
"Sai da safe Afrah."
Sai ta sunkuya daidai kunnen Amrah
"Sai da safe." Bata sa ran xata amsa ba dama. Tana tsaye har suka fita daga layin, taji wasu hawaye sun biyo kunci ta,zata yi missing Amrah sosai.
A hankali yake tukin, zuwa lokacin har an fara yayyafi kad'an kad'an, sanyin AC da sanyin garin suka hadu suka cika ko ina, kankame jikinta tayi, ta lafe a jikin kofar motar. Hannun sa ya zuro cikin mayafin ta data dunkunkune kanta dashi ya kama hannayen ta yasa a cikin nasa ya cigaba da tukin sa hankalin na rarrabuwa. Parking yayi a gefen hanya ya fita da dan gudu ya shiga wani shop, be dad'e a ciki ba ya fito ya zo ya bude baya ya zuba kayan ya ja motar suka tafi.
Suna isa gida ya kashe motar, yana kallon ta, ta dan hasken da ya hasko cikin motar.
"We are home." Yace yana smilling.
Kama murfin motar tayi ta fito, ya zagayo da sauri ya rike hannun ta.
"Kar ruwa ya jik'a min ke."
"Bismillah." Suka nufi kofar shiga main gidan. Mukulli ya ciro ya bud'e sannan ya ja baya ya bata hanya. Da bismillah ta shiga ya biyo bayan ta bayan ya koma ya debo ledojin da yazo dasu. A takure ya sameta a kan kujera, ya ajiye kayan ya zauna a kusa da ita.
"Kinga yadda abubuwan suka kasance ko? Ba da wani dalili nace ki zauna a gidan ba, sai dan abinda zan fuskanta bana son ina chan kuma ina tunanin halin da kike ciki, atlease idan kina gida zan samu peace of mind, Amma bansan hakan zai bata ran Hajiya ba."
"Hajiya abu kad'an ke bata mata rai ai."
"Tana da gaskia, kuma banga laifin ta akan abinda tayi ba, sai ma murna da nayi dan dama ina ta dana sanin zaman da nace ki yi, God I need my wife a kusa dani."
"Umm."