Sashe 47
Abinda Ke Cikin Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Mami kiri kiri tace ba za a soya komai ba dan tasan suma masu kawo kayan zasu kwallafa rai da cin kaji, dan haka tace yadda suka zo da tuwo a cikin su, nan d'in ma tuwon za a yi musu dan shi suka saba ci, harda cewa su kila na dawa da masara suke ci nan kuma na shinkafa za'a yi musu miyar taushe tasan sai sunyi murna a yau. Ni dai ban yi magana ba saboda ko a jikina idan ma tace tuwon karfe za ai musu bana jin zai dameni saboda nima ba san ganin su nake yi ba.
Shiryawa nayi tsab na bar gidan saboda nasan ko sun zo sai Mami ta wulakantani a gaban su, nasa Tukur ya kai ni gidan su Aisha, ina shiga ta fara murnar gani na muka shiga dakin ta, kamar jira ni kuma nake yi kawai na kwanta kan gadon ta na fara kuka mai taba zuciya.
“Ahh kawata menene haka da girmanki? Haba kuka sai kace wata yar karamar yarinya.”
Still na sake fashewa da kukan ta dinga shafa baya na cikin nuna kulawa. Tunda aka fara wannan maganar auran ban samu wannan gatan ba na lallashi sai yau kuma a yanzu da Aisha take ta tausar min da zuciya tun kafin ma taji abinda nake yiwa kukan. Sai da nayi mai isa ta sannan na sanar da ita abinda duk ya ke faruwa, ta tausaya min kwarai da gaske sannan ta bani shawara akan na daure na karbi zabin daddy koda kuwa ace mijin gurgu ne ko makaho na daure na zauna dashi kodan farin cikin kawu daddy.
Ya zan yi? Innalillahi wa'ina ilaihir rajiun dole na karbi wannan auran ko ta halin ya ya ne, gaskiyar Aisha ne ya yi min abinda ko iyayen da suka kawo ni duniya basu min ba. Ashe kuwa idan hakane ya cancanci fiye da wannan sadaukarwarma a gareni, dan idan nace zan bijire ni kaina bazan taɓa yafema kaina ba har randa numfashina zaibar gangar jikina. Haka na zauna a gidan su Aisha tana ta lallashi da ban hakuri tare da bani labarai makamanta irin wannan auran da za ai min, da kuma shawarwari masu ƙyau da amfani.
Jinai zuciyata ta rage nauyin datai min sosai, na kuma samu y'ar nutsuwa duk da banajin son auren har yanzu. Haka na shiga sauke ajiyar zuciya ina sake godema Allah akan k'addarorina da suke zuwa gareni daki-daki. Ina fata da addu'ar zama cikin mutane masu hak'uri da cin ribar hak'urin koda ba'anan gidan duniya ba.
*DR ISMA’ELA RESIDENCE....*
Saboda tsabar wulakanci irin na su Mami ko malmala bata sa an yiwa tuwon ba, haka tace su juye a kula wai sa dinga zabtara. Wajan ƙarfe hudu kuwa akai horn mai gadi ya bude motoci tsala-tsala suka shigo harabar gidan. Tasama su Ya Shukrah suke leken su, hakan yayi da-dai da fara fitowar mutanan motocin.
Abin daure kan ashe su uncle Hashim ne da iyalansa sai uncle Kabiru shima da nasa family d'in duk sun zo biki, nan da nan su Ya Waleedah suka sakko da gudu suna musu oyoyo cike da murnar ganinsu.
“Ya akai babu labari Meenal?”
“Eh cewa akai karmu fada idan muka gaya muku ba za a zo da mu ba.”
“Ina amaryar take?”
“Ku shiga ciki mana kun tsaya anan zai zance kuke yi." Cewar Uncle Kabiru yana rufe mota.
Duk sai suka runtuma ciki suna murnar ganin junan su. A parlorn kasa iyayen suka zauna inda Mami ta fito gurin su. Suna ta hira sai ga Alhaji Isma'il ya sanar dasu cewa an fasa kawo kayan lefe sai ranar daurin aure za a hado da su, Mami ranta ya baci dan taso wulakanta duk wanda ya yi kuskuren biyo masu kawowa sai aka samu aka si. Baki kuwa sai sabon abin ci aka yi musu dan duk cewa suka yi ba zasu ci tuwo ba, kawu Hashim ne kawai yaci saboda shi yana son tuwo sosai. Ni kuwa ban koma ba sai da aka yi isha'i sannan Aisha ta rako ni har mota Tukur ya dawo dani gidan gabana yana faduwa wani dum... Dum... Dum.. Na shiga cikin parlorn jiki na a sanyaye kamar wace ba ta da laka..
“Oyo yo ga amarya ta dawo.”
Naji sautin muryoyi daban daban, duk a zato na fa yan kawo lefe ne basu zo da wuri ba har suka kai wannan lokacin. Sai da na dago kai na sosai na kallesu sannan na fahimci ko su waye, cikin farin ciki nima na rungume su tare da sakin kuka dan na tabbatar suma daurin aure na suka zo. Na gaida su suna ta lallashi na sun dauka na dadewa ban gansu bane dan kawu Hashim har da cewa.
“Last month wallahi naso zuwa na dauke ki, muje kiyi mana ku sati daya ne Allah be yi ba sai yanzu. Kiyi hakuri Khadija ki bar kuka Allah ya ji kan iyayen ki da rahama.” A hankali na ce.
“Amin.”
Daga nan suka bani kayan da aka dinko min daga can Lagos wanda zan yi fitar biki dasu, kawu daddy ya sanar min cewa an fasa kawo min lefe sai ranar daurin aure. Naji dadi sosai saboda har lokacin banji cewar zan auri wani ba Mas'oud ba, abin da kamar wahala duk da cewa bana daukar kiran da yake yi min dan gujewa fadawa fushin ubangiji. Zuwan su Meenal dasu Badiyya yaran uncle Kabiru da na uncle Hashim yasa na dan rage zaman yin kuka, dole suka sani a gaba da hira da kuma tursasani wajan cin abinci, wai kar naje gidan miji ina da ulcer a yi tunanin ba'a bani abinci a gidan mu.
A ranar kam alhamdulillahi na d'an yi bacci, sai dai duk na riga su farkawa, nayi sallah na zauna ina nemarwa kai na sauki a gurin Allah madaukakin sarki. Bani da buri yanzu irin naga wannan zakwakurin da yazo ya rushe min duk wani farin ciki na, yasa na tsani komai na rayuwa a lokaci daya. Su kuwa sun dade basu farka ba dan babu irin tashin da ban yi musu ba amman basu tashi ba sai da suka tashi da kan su. Wajan karfe takwas matar uncle Kabiru ta kira ni, naje take tambaya ta anyi min gyaran jiki kuwa? Na yi kasa da kai waye zai yi min bayan bani da uwa a duniya? Kawu daddy dai ya yana yi min iya abinda zai iya, Mami ita ya kamata ta yi min wannan amman ko a jikin ta, bata ki ma a kai ni ina cikin yanayin kazanta ba babu ruwan ta ita tunda basu Shukrah bane.
“Amman garin ya hakan ta faru?”
“Babu komai Aunty, kawai ni ce nace bana so.”
“Shine suka kaleki saboda kince bakya so? Toh maza ki tashi ki shirya yanzu kizo ni zan miki, Allah yaso nazo da komai na yi da kenan haka za a nannade ki a kai ki gidan mijin. Ai Khadija ko kana da kyau cewa akai ka kara yin wanka sai kafi haka kyau, musamman ke da zaki doshi gidan girma mai daraja kamar yanda muke fata.”
Na yi shiru zuciya ta kamar zata kone jin maganar gyaran jikin nan, sam bana so dan nasan zan gaya yin kyau kuma hakan zai sanyayawa mijin rai abinda ni kuma bana so wallahi. Na tashi kamar zan fadi sabo da sauri na bar gurin, ina ta kufce-kufce ta yadda na gujewa gyaran jikin amman sai da tasa aka nemo ni muka shiga dakin da ba za a dame mu ba ta yi min. Mami kam ko a jikin ta bama taso taji ance za a min wani abun na kulawa wanda ita ya dace tayi min amman ta shafawa idanunta kwallin rashin mutunci saboda hassada da bakin kyashi.
Subahanallahi ni kai na sai da naji canji a jiki na lokacin da aka gama yi min dilka da halawa na musamman, da yake yar asalin yerwa ce tasan ta kan kamshi mai zama a jikin ɗan adam. Naji wani dadi fiye da yadda nake tsammani, sai dai bana jin zan iya bari wanda ba Mas'oud ba ya kwashe wannan ni'imar.
Koda aka gama cewa tayi na tafi daki karna sake na fito waje, komai nake bukata nasa a kawo min nace mata to.
Abin da ya bani mamaki duk sunyi anko wai na bikin ne, lallai sun shiryawa auran nan mu duk bamu sani ba. Ganin kowa ya yi ne yasa Ya Waleedah da Ya Shukrah suka je kasuwa suma suka siyo irin material d'in sannan suka kai aka dinka musu saboda kar a yi musu surutu. Sai da naga abin da gaske ne sannan na tashi na dauki wayata na shiga toilet tare da kunna famfo yadda ko nayi wayar babu wanda zai iya jiyo ni. Bugu daya tamkar daman ni yake jira kawai naji ya daga murya shi a can kasa kasa.
“Yanzu ba zaka tsamo ni daga fadawa wannan auran ba daddyn Waleed? Kar kai min haka dan Allah. Da nace ba zan kuma kula ka ba sai randa ka samo mana mafita, amman na kasa gashi na kirawo ka da kai na.”
A hankali naji yana magana dan sai na kasa kunne sosai nake iya jiyo abinda yake fada.
“Ban san me zan iya ce miki ba Oum waleedah, yanzu haka ina kwance a asibiti tun shekaran jiya. Bana jin zan iya kuma numfashi daga lokacin da aka ce kin zama mallakin wani ba ni ba.”
“Ya Subahanallahi na shiga uku, Mas'oud yanzu kana asibiti? Da gaske ba kai zan aura ba? Wallahi nasan ina cikin tashin hankali, dan Allah karka guje min bazan iya rayuwa ba bu kai, ka tallafawa zuciya ta Mas'oud, idan ba hakaba wallahi nima gawata za'a kai gidan koma wanene.”
Kasa cewa komai ya yi, sai muryar wata mata da naji tana min magana cikin lallashi, da alama mahaifiyarsa ce. Cikin sanyin murya take min magana itama kamar zata yi kukan saboda naji yadda take rawar murya.