Sashe 31
Abinda Ke Cikin Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
“Ina neman afuwarki uwar daki na, sai dai wannan labarin da nazo miki dashi ban san yadda zaki dauke shi ba.”
“Ina jin ki Jakadiya.”
“Dama yanzu Gimbiya Shaheedah tasa nayi mata iso wajan maimartaba sarki, yanzu haka tana can gurin sa zasu yi ganawa ta musamman tsakanin su.”
A fusace Gimbiya Jaleela ta kalli Jakadiya tana hararata tace.
“Me nace miki game da cewa Salman sarki?”
“Ki gafarce ni Uwar daki na tuba nake Allah ya huci zuciyar ki, sha'afa nayi wallahi ki yafe min.”
“Shikenan amman ki kiyaye gaba. Ina so kuma ki binciko min abinda taje suka tattauna, bana kuma son kuskure kin sani dai.”
“Insha Allahu uwar daki na ba za a samu wani kuskure ba, Allah ya ja zamanin ki.”
Daga haka ta mike ta fita tana rawar jiki. Bata wuce ko'ina ba sai sashen Gimbiya Najwa wato kishiyar Gimbiya Jaleela, wace ita ce matar marigayi sarki Aliyu Salman ta uku, yar Galadima ce. Ita kuwa tana kishingide a tsakiyar katafaran parlorn ta, hadimanta suna ta faman yi mata fifita, wasu na matsa mata kafafuwa yayin da wata ke gefe tana yanka mata kayan marmari d'aya bayan d'aya tana sha. Gimbiya Najwa na ganin Jakadiya ta yi saurin sallamar hadiman nata, dan tasan tabbas labari ne ta kawo mata game da Sarki Salman ko Gimbiya Shaheedah ko kuma mahaifiyar sarki Salman d'in wato Gimbiya Sa'adatu.
Jakadiya daman tasan halayen ko wacce mata dake gidan, saboda duk itace munafukar su, wajan kai gulmar ko wacce a gurin d'aya. Tasan daman Gimbiya Najwa ba zata tambaye ta komai ba har sai idan ita ce ta fara yin magana, wani lokacin Jakadiya takan jinjinawa irin girman kanta da takamarta saboda kawai tana yar Galadima, da ace a yar gidan sarkin kacokam Allah ya yi ta bata san me zata yi ba, duk da cewa a wannan lokacin su Waziri da shi Galadiman sune suke jan ragamar sarautar Sarki Salman, sai abin da suka ce shi za'a yi.
“Na gaisheki ta gaban goshin marigayi sarki Aliyu... Jinjina da ban girma gareki shalelen Baba Galadima, uwa ga magajin sarki wato yarima Ilyas(junior). Nazo miki da wani labari.”
Kamar ba zata amsa ba tsawon lokaci, sai da ta mulu ta mulmule sannan ta kalli Jakadiya karo na biyu tace.
“Idan kin san maganar ba ingantacciya bace karki sanar dani, ki bari idan kin tabbatar da ingancinta, sai kizo ki gaya min.”
“Na kuma gaisheki ta gaban goshi, tabbas bani da gamsashiyar magana akan abin da nazo miki dashi. Kamar yadda kika ce, zan koma idan na gama tabbatar da ko menene zan dawo. Na barki lafiya, farin cikin yarima kuma sarkin gobe, shalele Ilyas.”
Tufa d'in dake hannunta taci gaba da ci ba tare da ta sake bi ta kan Jakadiya ba, saboda ita Gimbiya Najwa tana da wasu munafukan bayan Jakadiya, dan ita a cewar ta idan wata taga wani abun, wata be zama lalle ta gani ba. Hakan yasa ta rarraba kafa ta baza masu gano mata sirrikan duk wata mata dake cikin gidan. Shi yasa Galadima yafi waziri sanin duk wani abu da ya shafi Gimbiya Shaheeda da kuma sirrin mahaifiyar sarki Salman.
Can kuma bangaran Sarki Salman da uwar gidan sa wato Gimbiya Shaheeda, tana shiga ta zauna gefen shi tana tsotsar alawar da take cikin bakin ta tace dashi.
“Wani lokacin kakan yi min abin da sam be dace ba a gaban kaskantattun mutane, wato hadimai. Ya za'ai kamar ni nace ina son yin magana da kai kace a ce min bacci kake yi? Karka manta ban da ni babu wacce zata iya zama da kai bayan kowa yasan cewar ba da kwan haihuwa, ba zaka iya bawa Basannabas magaji ba kamar yadda marigayi ya bar maka gadon mulkin sa wanda kake a kai yanzu.”
Jin kalamanta yasa ransa fara tafarfasa saboda zafin su da yaji, bata da wani abu da take yawan yi masa gori irin rashin haihuwar sa. Amman saboda tsabar shakkarta da yake yi sai bai ce mata komai ba har ta kuma yin magana.
“Ni wallahi kasan ba da ban soyayyar da nake yi maka ba, da tuni nasa ka sauwake min naje nayi wani auran na haihuwa. Amman saboda na san babu matar da zata iya auran ka yasa nake daurewa ina lallashi zuciya ta akan ta hakura ta zauna tare da kai.”
Ta yi shiru na dan wani lokaci, shi kuma wata irin tsanarta ce take sake zama sabowa a zuciyar shi. Shi be ki ta ce ya sauwake mata ba indai har tana da bukatar yin haka, baya jin komai a game da ita sai zallar shakka da son bin duk wani abu da take so. Kansa a kasa dan ko da ta shigo be dago ya kalleta ba sai ji ya yi tace.
“Honey dago ka kalle ni.”
Ta na rufa baki kuwa ya daga yana kallanta, ta yatsina fuska tare da mika hannu ta zare bakin glasses d'in idan shi yadda zata ganshi sosai.
“Haba Honey, ba na hanaka kallo na da wannan glasses d'in naka ba? Na yi na yi da kai ma ka dena saka baki amman ka kasa bari, idan ka sashi kamar wani tsohon makaho wanda bashi da d'an jagora.”
Da yasan wannan maganar ce zata kawo ta da duk yadda zai yi sai ya hana su hadu, sai dai ance rashin sani yafi dare duhu. Kuma idan da sabo yaci ace ya saba da duk wasu abubuwa da ake yi masa a masarautar. Ita kuwa kallon shi kawai take yi tana jin wata zazzafar kaunar shi, hakan ne yasa bata son taji ana cewa ya kara aure shi yasa take kuma rike shi ta hanyar da zuciyarta ta aminta.
“Sannan kullum nice nake nema ka kai babu wani abu da yake damunka. Ina tunanin rashin haihuwar nan taka tana da nasaba da rashin sha'awa da baka da ita. Ko kai kayi zaton sarakuna basa mu'amala da matan su?”
Salman ya yi shiru dan shi sam ba wani farin ciki yake ji ba idan suna yi. Shi kawai yana yi ne ko Allah zai sanya ya samu rahama, ya kuma fita a hakkin ta na aure. Ganin ba zai yi magana ba yasan yata tashi tana murmushi ta wani jujjuya ya masa kugu ya kawar da kai, ba burgeshi take yi ba, hasalima ji yake tamkar ya fashe da kuka dan haushi da takaicin abin da take yi. Tana fita ya sauke ajiyar zuciya tare da rintsa ido kawai ya hangi Dije tana ta yi masa murmushi a wajan fuskar shi. Sai ya samu kansa da kin bude idon yana jin wani dadi a yadda yake ganin ta. Kiran sallar magariba shine ya tayar dashi daga gurin, ya shiga toilet ya daura alwala daga nan ya shirya ya fito zuwa masallaci dan kagabar da sallah.
°°°°°°°° °°°°°°°°° °°°°°°°°°°°
Tun da ta idar da sallah ta mayar da goshinta kasa bata sake dagowa ba, addu'a kawai take yi tana zubar da hawaye. Cikin kaskantar da kai take gayawa Allah muradanta duk kuwa da cewa tasan yasan tana cikin halin bukatar taimakonsa. Sannu a hankali ta dago fuskarta sharkaf da hawaye, tasa bayan hannunta tana sharewa. Gimbiya Sa'adatu kenan wato mahaifiyar sarki Salman, mace mai tsantsar hakuri da juriya tare da kawar da kai.
D'an ta ne, amman ba ta da wani iko akan shi, daga nesa kawai suke hango junan su amman basa haduwa face to face saboda an riga an janye mata shi daga gareta.
°°°°°°° °°°°°°°° °°°°°°°
Kishingid’e gimbiya shaheeda take a doguwar kujera dake tafkeken parlorn ta na alfarma. Wanda komai na cikin parlorn kirar samfarin kayan sarauta ne wanda turawa kewa laqabi da ‘Royal design’. Kai hatta salular da ke saqale ajikin da bango itama ta Royal ce.
Bayinta biyu ne a zaune kowanne yana mata tausa a kafa d’aya d’aya. Sai lumshe idanu take ahankali tana mai cigaba da taunar tufar dake hannunta, Wanda take gutsira ahankali cikin k’asaita.
Wayar tace dake kusa da ita tayi haske alamar saqo ya shigo, Sai data mula tasha iska tukun sannan ta daga wayar ta duba. Ta jima kafin ta daga musu hannu alamar su dakata, Sannan ta mike ta gyara zaman wani hadadden mayafin jikin ta mai beza. Bayin guda biyu suka bi bayanta kowacce kanta a kasa.
Sashen su ta nufa, Dake dare ne, Tarwar masarautar take da hasken lantar ki. Tsuntsaye nata kuka. Shiga tayi cikin wani babban parlor. Duk sun hallara aciki, Kowacce tana hakimce a kujera tana jin kanta. Kallo d’aya zakai musu kasan manyan mata ne masu aji, Wanda ke watayawa a duniyar masu kudi.
Gaishe su tayi. Ta samu waje ta hakimce itama. Bayin dake wajen duk suka basu wuri. Babbar matar ta tsakiya dake hakimce ta mike kafafun ta akan center table itace tafara magana,
“Shin ya sanar muku da halin da ake ciki kuwa....?”
“Hmm! Ki bari kawai.. Mun fara sanya fa. Yacemin kwana biyu ya kasa gane kansa.”
Cewar Haj Huwaila ta bawa Haj Jaleelah amsa tana tana jijjiga kafafu.
“Shin Gimbiya Shaheeda kin fara ganin alamun canji kuwa?”
Haj Najwa ta tambayi Gimbiya Shaheeda dake kallon su baki d’aya. Gimbiya Shaheeda taja majina tana jujjuya zobunan daham din hannun ta.
“Toh.. Gashi nan dai.... Ba wani matsala gaskia. Yanzu ma wanka nakeso nayi ayimin iso wajen sa.”
“Karki sakaci da maganin nan Gimbiya. Wallahi Malam ya rantse da abinda zai kashe shi wannan maganin babu na biyun sa..”
Haj Jaleela tace da Gimbiya Shaheeda data mike lokaci guda tana Yatsina fuska,
“Duk yadda ake ciki...”
Sallama ta musu ta dauki hanyar sashen ta. Kallo d’aya tayi wa sashen mai babban daki tayi gaba tana sake daure fuskar ta.
Su kuwa ko bayan fitar ta sa zancen ta suka yi a gaba. Sunata shewa suna tafawa. Tamkar ba kishiyoyi ba ada. Aminan juna ne na qut da qut.
Gimbiya Jaleela ce ta gyara zama tana faman jujjuya ido tace.
“Ni wallahi so nake a fara bawa mata sarauta a kasar nan. Ina ji a jiki na zan iya duk wani abu da ake yi a cikin sarauta. Kuma nayi mafarki nan gaba kadan mata zasu dawo sune suke jan ragamar mulkin masarautar Basannabas.”