← Book details Abinda Ke Cikin Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 103 OF 108

Sashe 103

Abinda Ke Cikin Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

"Tabbas abinda kaji shine gaskiya Safwan, mutanen da suka zo tare da Sultan a matsayin iyayen sa kai ma sune iyayenka, dole ne ka sani dan ranar wanka ba'a boyon cibi, duk da haka ku dukka yayanmu ne, ba wai hakan na nufin babu ku babu mu ba, amma suma suna bukatar sanin ku."

"Daddy...!?"

"Karka ce komai, idan kaji wani iri a zuciyar ka kayi addu'a, ka kuma godewa Allah da baiwar da yayi maka, su din iyaye ne da kowanne d'a zai yi burin kasancewa dasu."

"Alhamdulillah ya Allah." Kawai ya furta, ya runtse idon sa da karfi hawaye na cigaba da sauka a idon sa, hannun sa Sultan yaja suka fice ta kofar bayan sannan suka dangana da dakin su.

A durkushe suka tarar da ita tana kuka sosai, kamar zata shid'e, duk da kukan itama Mah-Mah take yi amma sai tayi saurin yin wajenta, ta rik'e ta ta tada ita tana kyautata zaton taji komai, kai tsaye daki suka nufa ta zauna da ita a gefen gadon dakin ita ma ta zauna dukkan su babu wanda yayi yinkurin tsaida hawayen da yake zubarwa babu kuma wanda ya tanka a cikin su.
   Zuwa wani lokaci zuciyar su ta fara sauka a hankali, Ummi ce ta zame ta sauka k'asa,

"Tabbas dani dake muna kan abu daya ne, sai dai ni nawa farin ciki ne, inda naki ya zama bakin ciki, nasan yadda kike ji saboda na shiga irinsa tsawon lokaci, sai yanzu Allah ya kawo karshen damuwa ta, ashe akwai ranar da zanyi farin ciki nima? Karki ga kamar bana tausaya miki halin da kike ciki, ina tausayin mu dukka amma kuma ina bukatar yaya na, ina bukatar su kwatankwacin yadda kike bukatar su, amma duk da haka bana nufin dauke miki su, har abada ke din kece uwar su, basu da kuma wata uku a bayan ke."

"Nagode Allah ya saka da alkhairi, ba abu bane me sauki rana daya kana tare da danka ace ba danka bane, kowacce uwa ce dole zata shiga tashin hankali balle ni da dukkan komai nawa ya tattara ne akan Safwan, ina yi masa son da ban san adadin sa ba, ina kuma tunanin dalilin shayarwa ita ta kara shakuwar mu, amma babu komai haka Allah ya kaddara min,nayi imani da kaddara mai kyau ko mara kyau."

"Na sani, nasan yadda kike ji... Kiyi hakuri Safwan dan ki ne,ke ya sani jiya, ke ya sani yau ke kuma zai cigaba da sani har gobe, ke din kece mahaifiyar sa."

"Nagode, nagode Nagode Allah ya saka da alkhairi."

"Amin ya Allah."

***Suna zaune suna hira Adnan ya shigo, dama tun tafiyar Sultan shine yake kula dasu yake musu komai bisa umarnin Sultan din, yanzu ma kiran da yayi masa yasa shi wutowa nan din kai tsaye bayan sun tashi daga wajen aiki. Gaisawa sukayi ya fad'a musu Sultan ne yace yazo ya tafi dasu, a shirye suke dama sai kawai suka rufe kawunan su suka bishi, daga nan suka wuce inda zasu dauki Muhammad da Aysha wanda dama tuni ya kira Muhammad din a waya tunda shi din ma da Sultan din zai yi tafiya ya had'a shi dashi sai ya zama komai zasuyi sai sun sanar da Adnan din. Haka ma case din Madaki Adnan din ne akai shi yake yin komai.
   Isar su kofar gida yayi daidai da fitowar Amrah da Afrah zasu shiga gidan Mah-Mah, ganin motar Adnan din ya saka suka fasa shiga suka tsaya suna kallon motar da mutanen dake cikin motar. Ganin su Maman Yara ne ya saka su saurin matsawa, suka gaisa sannan sukayi wa Amrah sannu da zuwa sannan suka dunguma suka shiga gidan inda Adnan ya wuce zuwa nasu gidan dan a gajiye yake tikis yana bukatar hutu.
   Kai tsaye falon Mah-Mah suka zarce, Muhammad ya tsaya daga harabar gidan be bisu ba. Lokacin Sultan suna zaune da Safwan yana warware masa yadda abubuwan suke, yayi shiru yana sauraron san yana kuma mamakin yadda akayi abubuwan suka zama haka.
   Kuka ba shine zai chanja komai ba, sbaoda haka ya tsaya kawai yana sauraren sa, tausayin Ummi da na Aminatu ya kamashi, yasan duk cikin su babu wanda be shiga damuwa ba ta dalilin su amma kuma sai yaji yafi tausayin matar da aka ce ta dauki cikin su tsawon watanni goma sha, ba mutum daya ba kuma har biyu, duk da cewa anyi amfani da komai daga wajen Maimartaba da Gimbiya akayi mata dashen dashi amma kuma dole ne a kirata da mahaifiyar su, ita tayi komai na dawainiya dasu a ciki ta kuma haife su duk kuwa da C's akayi mata aka cire yaran.
   Tunanin yadda zai gansu ya hau yi, yana tuna lokacin da suka hadu da Muhammad a wajen da suka je tafiya da Amrah, da yadda yaji wani abu game dashi a lokacin Amma sai ya bar hakan ba matsayin tausayin sa da kuma sadaukarwar da yayi ba tare da yasan wace Amrah ba.
   Zabura Ummi tayi ganin wadanda bata taba saka ran gani ba,

"Azizah, Aminatu?" Ta kira sunan su tana mikewa da sauri, jikin ta na wani irin rawa kamar mazari, durkusawa sukayi a gabanta, lokacin har Aminatu ta fara kuka, kukan da ya tuna mata da abun da ya faru. A gefen su Ummin itama ta durkusa, tana jin burin ta da addu'ar ta, ta gama cika a yanzu, duk addu'ar ta da ta dad'e tanayi akan wannan ranar ce, akan wadannan mutanenn sai gashi Allah ya had'e mata su a lokaci daya.
    Babu wanda ya yi yinkurin bawa wani hakuri, suka sha kukan su suka more, sannan ne suka dawo hayyacin su, aka shiga tambayar bayan rabuwa, da kalar rayuwar da suka fuskanta.
   Daddy ne yayi kiran Mah-Mah a waya yace duk suzo falon sa gaba d'aya, tashi sukayi suka dunguma chan kowa ya zauna aka sake sabuwar gaisuwa sannan Sultan da ya zama kamar shine mahadar kowa ya fara magana a nutse.
   A wannan zaman, kowa ya fahimci yadda abubuwan suke, labarin Aminatu ya taba kowa dan kusan kowa sai da ya zubar da kwalla da tana fad'an kalar azabar da tasha a hannun azzaluman mutenan.
   Anan aka gabatar da Safwan da Muhammad a matsayin yan biyun da akayi mata dashen su, inda Muhammad ya rayu tare da Safiyya shi kuma Safwan Madaki ya bada shi a wajen su Daddy. Sosai maganar ta daki Muhammad, dan har yaso yafi Safwan shiga cikin yanayi akan maganar ko kuma dan shi ba a lokacin yaji maganar ba?
   Kallon su Aminatu ke yi hawaye masu zafi na fita daga idon ta, su dinma ita suke kallo, kowa da abinda yake tunani akan Al'amarin. Ummi kam ba'a cewa komai, fasalta yanayin da take ciki na farin ciki ma bata baki ne, sai ta kalli wannan ta kalli wannan ta rasa ina zata saka kanta don murna, samari ne dukkansu masu jini a jiki, masu kyawu da cikar kamala,duk kuwa da nakasun ilimin dake tare da Muhammad amma shi din ma bashi da aibu, ya kuma samu ilimin sa na addini daidai da yanayin sa da yanayin rayuwar da suka taso a ciki.
   Sai bayan komai ya lafa ne, Maimartaba yayi gyaran murya, sannan yayi bayani cikin jawabin sa wanda ya saka kowa a cikin farin ciki. Suka kuma daura aniyar yin komai domin kaman ya kasance kamar yadda yake a tsare.
   Da haka taron ya kare bayan dogon lokacin da suka dauka ana yin sa.

*Two weeks later*

[7/6, 10:02 PM] Maman Maryam: ©®Hafsat Rano

Page 56

RanoNet
www.ranonet.com.ng
Register for your amazing data at a very cheap price.
Mtn 1gb @300 naira only

****
Motocine guda Biyar dukkansu rufe suke ruf da bakin glass, motar farko Muhammad  ne yake tuka ta, Sultan a gefen sa sai Daddy da Maimartaba a baya, ta biyu kuwa Ummi ce a ciki da Amrah da Maman Yara, Safwan ne yake jan motar, sai ta uku Mah-Mah ce da Aminatu, sai Aysha Adnan na tukawa,in da motocin karshe guda biyu suka kasance kaya ne cike a ciki sai driver kawai. A kofar Masarautar suka ja suka tsaya, masu tsaron kofar duk suka zuba musu ido, cike da mamakin zuwan nasu duk kuwa da gagarumin taron da ke gudana acikin Masarautar, babban cikin su ne ya taso ya iso wajen motar ya kwankwasa glass din, Sultan ya juya baya ya kalli Maimartaba, yayi masa izini ya bud'e, ya bud'e a hankali, da sauri me tsaron kofar ya daga hannun sa sama ganin Sultan din cikin shigar kayan sarauta hadda rawani irin na manyan Masarautu dauke da kunnuwa biyu.

"Allah ya baku yawan rai, Barkan ku da zuwa Babbar Masarautar irin Masarautar Saji."
Chapter 103 · 0% Book details