← Book details Abinda Ke Cikin Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 108

Sashe 28

Abinda Ke Cikin Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Bayan sati in fama da jinyar kaina da zuciya ta, saboda yadda nake ji a duk lokacin da nayi kokarin yi masa magana akan abinda ke ciki na, amsar sa daya ce be san me nake magana akai ba, nakan had'a kaina nayi kuka na share, har Yaya Muhsina ta tattara ta koma bayan na roke ta akan karta sanar da iyayenmu halin da nake ciki.
   Ina kwance bayan na dan samu saukin jikina, hankali na yakai kan wata takarda dake ninke a k'asan kujerar dake fuskantar gadon da nake kai, na tashi da sauri na tsuguna na dauka, na bude ta ina bin rubutun da kallo, da Hausa akayi rubutun sai dai kafin ka fuskanci yadda rubutun yake a harhade sai ka sake karantawa,

_"Hakika Allah baya son zalunci, saboda haka addu'ar wanda aka zalunta bata da hijabi, an zalunce ki ta hanyar cire abinda ke cikin ki saboda wani kuduri nasu, aka koma so a halaka shi, sai dai Allah ba Azzalumim Sarki bane,Yayi ikon Sa akan Abinda kika haifa ba tare da sun iya aikata komai ba, Ina fatan watarana, zai zamar musu ciwon idanu, hakan zai yi sanadiyyar bayyanar Abinda Ke Cikin ZUCIYA, komai zai bayyana sannan kofofin zalunci zasu rufu ruf, watarana, ranar da komai zai bude, ban san yaushe ba, amma nasan akwai ranar, zata zo komai daren dadewa!"_

"Na maimaita karatun takardar nan har sai da na dinga jin kalaman na amsa kuwwa a kaina, har sai da na koma ina rayuwa akan abinda takardar nan ta kunsa, zan iya cewa har yau ina rayuwa ne da burin bayyanar Abinda Ke Cikin Zuciyar mutanen da suka wargaza min rayuwa, suka raba uwa da d'an ta, suka kuma ingizata ta aikata abinda har yanzu nake cikin dana sani,nake tsoron haduwa ta da Allah. Ina burin ganin ta, ina so na tabbatar mata da duk abinda ya faru ya faru ne bisa kuskure, rami me matukar zurfi suka hak'a mana suka kuma tabbatar mun fad'a ciki chan k'asa, suka kuma saka k'asa suka rufe mu a ciki ba tare da sun bar wata shaida da zata nuna gaskiyar mu ba. Ta ina zan fara neman ta Muhammad? Ta yaya? Bayan tun ranar babu wanda yace mana ko me kama da ita. Tabbas mutum mugun icce ne, mutum abin tsoro ne Muhammad."

"Wacece ita?" Ya tambaya tausayin ta na ratsa shi, sai yake jin kamar yana da wata gudummawa me girma da zai iya bata, amma ta yaya?

"Ka shirya jin zalunci mafi girma da muka aikatawa marainiyar Allah, zaluncin da ya kawo mu inda muke yanzu ya ajiye mu ba tare da wani ya sake waiwayen mu ba."

"Muhammad kai likita ne, kasan abinda ake nufi da Surrogacy, kasan illar sa, haka kasan hukuncin sa a addinin mu. Idon mu ya rufe, haihuwa kawai muke nema bayan da likita ya tabbatar da mahaifata ta lalace, lalacewar da ba zata iya daukar ciki ba har abadah, tun bayan dana samu labarin na shiga kunci, na daina walwala na kuma chanja komai ya daina min d'adi, na daina farin ciki na zama mafad'aciyar karfi da yaji, ana haka sai maimartaba yazo da shawarar da ta ruguza dukkan komai, bansan wanda ya bashi shawarar ba, idona ya rufe ban iya tsayawa bin diddigi ba na amince da Abinda na san ba daidai bane, haramun ne Allah ya hana, muka shirya da babban likitan da ya kware a aikin wanda shine likita na farko da ya fara irin wannan aikin na dashe a kasar mu, muka kuma samo yarinya bayan dogon bincike da nazari akan yaran dake cikin masarautar da basu da wani galihu, muka kuma samo wadda muke ganin itace daidai,muka kuma aiwatar da kudurinmu akanta."

Hawayen take fitar wa sosai, hawayen dake rage mata rad'adin abinda take ji, samun kansa yayi ta zaro handkerchief a aljihun sa,ya mika mata yana jin kukan na taba shi sosai, kallon agogo yayi be san lokaci ya ja sosai haka ba. Murmushi tayi masa bayan ta goge fuskar tace

"Na bata maka lokaci ko? Naji ni sakayau bayan dana amayar maka wani shashe na abinda ke cikin zuciya ta, yau zan yi baccin da ban taba yin irin sa ba, nagode da bani damar da ka bani."

Folding hannun sa yayi, yana jin at that instant matsalar ta, ta zama tasa, zai kuma yi iyakar kokarin sa ganin ya dawo mata da farin cikin da take cewa ta rasa, zai nuna mata cewa tana da damar da zata fara rayuwa afresh, ta manta da komai da kowa, sai dai yana bukatar yayi dogon tunani akan labarin ta , ya yi masa filla filla yadda zai gane inda matsalar take. Sallama yayi mata ya fito, ya dan yi turus ganin Baba a falon yana jan tasbah

"Nagode sosai Muhammad, ina saka ran Maryam zata manta da komai nan kusa ta dawo da rayuwar ta kamar yadda take, ka taimaka min wajen cikar buri na."

Ya tare shi da magana tun kafin ya karasa gaishe shin da yake

"Karka damu Baba, in Sha Allah zan yi kokari na akai."

"Allah yayi maka Albarka." Yace yana gyad'a kansa kamar komai ya kare.

***A kafa yake takawa yana tuna komai daki-daki, yana kuma so ya fitar da daidai da akasin haka a cikin labarin nata, wayar sa dake hannun sa tayi kara kad'an, ya duba da sauri sai yaga kiran Mah-Mah ne ya shigo ya yanke, da sauri ya bi kiran yana tunanin ko Safwan ne ba lafiya, sai dai tun kafin ya gama daidaita wayar a kunnensa abinda be taba tunani ko hasashe ba.
   Da sauri ya karasa gidan, dan tsananin tashin hankali be san inda yake wurga kafarsa ba, ba damuwar sa bace abubuwan da zasu je su dawo, damuwar sa daya abinda mutanen da ya dauke su rayuwar sa zasu shiga idan komai ya kwabe.

"Ya Aallah!" Yake ta ambata sanda ya tura kofar da yaji ta a bud'e ba tare da ya danna door bell ba, suna zaune su uku, ta dora kanta akan kafar Umma tana kuka sosai, sai yaji ya k'asa garasawa ciki, ya jingina da kofar ya jin wani iri, rana ta farko da ya ji bashi da confidence din fuskantar mutane, be san me zasu ce masa ba, haka be san amsar da zai basu ba a yanzu da shi kansa be san waye shi ba.

KUNA BUƘATAR A TALLATA MUKU KAYAN SANA'ARKU A PAGES ƊIN BOOKS ƊIN ZAFAFA BIYAR 2021?.

To kuzo ga dama ta samu💃🏻💃🏻.

        Ina ma'abota son a tallata musu hajojinsu a kafafen yanar gizo suke?.

Tofa kuzo dama ta samu, dan jerin gwanon haziƙan marubanku ƴan biyar sun fiddo muku da hanyar da kuma kasuwancinku zai zagaya lungu da saƙo ta dalilin shafukan littatafai.

Ga duk mai buƙatar a saka masa tallan kayan sana'arsa a shafin littatafan mu na zafafa biyar zai iya tuntuɓar waɗan nan Numbers 0903 234 5899 or 09033181070 ta WhatsApp, idan har agama buks ɗin kana buƙata a sakamaka talla zamu saka maka akan farashi mai sauƙi. Idan kuma wasu adadin pages kake buƙata koda ɗaya ne duk zamu saka maka akan farashi mai sauƙin gaske🤓.

Kuyi maza ku kawo, mai haja shike talla, mai saya kuwa shike neman sauƙi😻😻😄🤗.

______________________

_ZAFAFA BIYAR 2021_*🔥

_*SUKAR BAYA*_💚
_BILLYN ABDUL_
( _kwai cikin qaya_ )
( _raina kama_)
( _wutsiyar raqumi_ )

*_SIRADIN RAYUWA_*💛
_SAFIYYA HUGUMA_
( _alqawarin Allah_ )
( _daurin boye_ )
( _Dangantakar zuci_ )

💙

_*KIBIYAR AJALI..*_💜
_MISS XOXO_
(Sulke baya tsare ta sai ta wuce)
( _Igiyar zato_)
( _Kaimin halacci_ )
( _Naufal_ )

*_ABIN DAKE CIKIN ZICIYA_*🧡
_HAFSAT RANO_
( _ruhi daya_ )
( _Sauyin qaddara_ )
( _Daurin goro_ )

*_MIN QALB_*❤️
_MAMUHGEE_
( _buri daya_ )
( _tarayya_ )
( _eznah_ )

Duka BIYAR 5 zaku samesu akan garabasar naira 700 kacal,

Guda hudu 4 Kuma 500,

Guda uku 3 Kuma 450,

Guda biyu 2 Kuma 400,

Guda daya akan 300.

Ma'ana
Each one is 300
2 is 400
3 is 450
4 is 500
5 is 700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO- *0812652655*
ACCOUNT NAME- *HAFSAT LAWAN GAMBO*
BANK NAME: *ACCESS BANK*

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

09033181070

Karku Bari ayi Babu ku domin wannnan salon na daban ne
SABUWAR SHEKARA
SABON SALO

TEAM#ZAFAFABIYAR🔥Onar Tasfah
15💓

***Ajiye wayar tayi tana kallon Hajiya Ummah

"Abinda nayi kuwa ya dace?" Mah-Mah tace tana zama a kusa da ita

"Kinga matsalar ki ai, kun dauko yaro kun ajiye shi a gidanku wai ku tausayi, gashi nan kina kallo idan baki yi wasa ba zaki rasa d'an naki k'waya d'aya tal a duniya, ke kin samu dayan ma mu kuwa fa? Idan nice da Safwan sai in da karfi na ya kare wajen ganin na masa abinda yake so, bare yaron nan bashi da kowacce matsala zuciyar sa fes take yana kaunar duk wanda ya rabe shi, amma ni dama sam Sultan be min ba, kawai kar kayi magana ne ace dan baka haihu bane baka san zafin d'a ba, amma ni kallo daya nayi masa nasan a karshe shine zai zamar muku matsala."

"Amma Ya Ummah Sultan bashi da wata matsala tun tasowar su, ina jin kamar ban kyauta ba abinda na gaya masa."

"Sai kiyi ta ganin rashin kyautawar kinji, ita fa wannan rayuwar kowa kansa fa ya sani, ina laifi ma abinda kukayi masa, gata dai daidai gwargwado ai kun masa, wanda nasan ba dan ku ba toh da har ya bar duniya ba zai taka inda ya taka a yanzu ba."

"Haka ne." Tace tana son d'ora zancen Hajiya Umman a mazaunin da take kokarin dora mata shi
Chapter 28 · 0% Book details