Sashe 60
Abinda Ke Cikin Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Tàshi mu je muyi alwala, mu yi wa Allah godiya."
Tashi tayi suka shiga bedroom, ita ta fara shiga tayi alwalar zuciyar ta na dukan uku uku ta fito, shima ya shiga yayi ya fito ya shinfida musu abin sallah, sukayi raka'a biyu sukayi addu'a sannan ya dafa kanta ya karanto addu'ar da tazo mana. Tashi yayi ya fita, sai gashi ya dawo da kayan da ya siyo. Ya ajiye sannan yazo ya kamata ya mikar da ita, ya janye mayafin da ta rufe jikinta dashi, ya ajiye a saman gadon. Ya jawo ta zuwa wajen da ya ajiye komai. Kasancewar dare ne gashi kuma lokaci yaja yasa suka dan ci komai kad'an, ta shiga tayi brush a lokacin ruwan da ake ya kara karfi sosai. Sanda ta fito baya dakin, kashe wutar tayi ta kwanta tana rufe idon ta. Shigowa yayi bayan ya sauya kayan sa zuwa kanana masu dan nauyi kad'an, ya hawo kadon yana kiran sunan ta. Shiru tayi masa sai yayi murmushi kawai dan yasan ba wai tayi bacci bane. Gefen ta ya samu ya kwanta yana sauke ajiyar zuciya da karfin. Matsawo yayi ya dawo daidai kusa da ita, yasa hannu ya juyota suna fuskantar juna, idon ta a rufe kam sai dai eyelashes dinta na ta rawa.
"Wannan idanun sun karyata ki, bud'e kiga."
A hankali ta dan bud'e idon kad'an, sai kuma tayi saurin rufe su ganin yadda ya matso so so so close to her.
Kissing saman kanta yayi in a passionate way, ya daga kanta dake saman pillow ya dora shi akan damtsen hannun sa, Sannan ya ture dankwallin kanta, gashin ta me matukar sulbi ya bayyana, hannun sa ya tura ciki ya shiga zagayawa dashi yana sakar kamshin hadaddun shampoo da conditioner din da tayi amfani dasu. A hankali yayi mata magana a kunne ,maganar da ta saka ta dunkulewa waje d'aya ta shiga kankame jikin ta.
"Please say yes." Ya sake rada mata yana cigaba da zagaya hannun sa a saman soft skin dinta.
"Please..." Ya sake k'asa sosai da voice dinsa. A hankali ta daga masa kanta hawaye na bin fuskar ta.
"I love you so much."
Sai ya kankame ta sosai yana jin kowanne lungu da sako na zuciyar sa na cikewa da tsantsar kaunar da yake mata. It's time da zai nuna mata yadda take a zuciyar sa.
Goodnight 😗😴😴
***Hasken wayar sa ne ya farkar dashi daga baccin da ya sake dauke su bayan sunyi sallar asubah, gefen sa ya kalla, ta makalkaleshi ta chusa kanta cikin jikin sa tana fitar da numfashi. Murmushi ne ya subce masa tuno abinda ya faru some hours da suka wuce. This is the best night ever a wajen sa. Alhamdulillah ya shiga jerawa dan shi ne kad'ai abi godia.
***Shiryawa yake tayi da sauri da sauri yana dubanta, cup din dake hannun ta take ta faman jujjuyawa ta kasa sha tun da ya fad'a mata tafiyar da zai yi bayan kawo ta da kwana daya tal, yasan dole zata damu, amma ba zai iya bari wannan damar ta wuce shi ba, yaji dadi da ya kira Abba yayi masa iya bayanin da zai fuskanta ya kuma amince xai turo mata Afrah, Hakan ya dan kwantar mishi da hankali.
Yana kama saka kayan yazo ya zauna yana jawo ta jikin shi, ya karbi cup din ya saka mata a baki.
"Kiyi hakuri, kiyi min addu'a kinji, in Sha Allah babu abinda zai faru, ki kula da kanki idan kuna bukatar wani abu ki fad'a ma Adnan."
"Kwana nawa zaka yi?"
"Bansani ba Amrah, bansani ba,Amma zan yi kokari naga na dawo da wuri, for you."
"Shikensn Allah ya bada sa'a ya dawo da kai lafiya."
"Amin matata."
Da hak ya samu ta dan saki jikin ta, ya sake taimaka mata ta sake gasa jikinta sosai ya bata pain reliever sannan yace ta kwanta kafin Afrah tazo. Sai da ta rakashi har gate, yana daga mata hannu tana daga masa ya fice daga gidan. Ciki ta koma tayi kuka sosai har sai da kanta ya soma ciwo.
***
Alhamdulillah, ina yiwa kowa fatan shiga Watan Ramadan lafiya, Allah ya sadamu da duk Alkhairan dake ciki, ya bamu ikon sauke nauyin ibadar yasa muga Daren lailatul Khadr yasa muna cikin bayin da za'a yanta.
Sai Allah ya kaimu Bayan Sallah da rai da lafiya. Ayi ibadah lafiya
[5/20, 9:05 AM] Maman Maryam: Abinda Ke Cikin Zuciya
Page 29
*Barka da sallah*
***Knocking ake sosai ta mike da k'yar cikin yanayin bacci me karfi ta nufi kofar, tun bayan tafiyar sa baccin ya dauke ta anan saman kujera, gajiya ce sosai a tattare da ita ga wani azababben ciwon kai dake damun ta plus gajiyar da oga kwata kwatan ya had'a mata jiya. Da k'yar ta isa gate din cikin dashashiyar murya tace
"Waye?"
"Ai nazata ko bin sa kikayi,wannan bugun da nayi tayi..."
Da sauri ta zare lock din tana jin dadi, tayi saurin rungume ta kankam.
"Bacci ya dauke ni wallahi."
"Baccin gajiya ko?" Afrah tace tana kashe mata ido daya, duka ta kai mata sannan ta mika hannu
"Kinji da gulmar ki, bani jakar kayan naki dallah."
"Yawwa kamar kin san na gaji."
Ta fad'a tana sakar mata jakar, ciki suka juya da nufin shiga suna cigaba da hirar su kamar ba jiya jiya suka rabo ba, suna haura balcony din aka buga kofar gidan da karfin gaske, kallon juna sukayi a tare
"Kina da baki ne?"
"A'ah..."
Sake bugawa akayi, ta ajiye jakar ta nufin kofar tana tambayar waye, ba'a yi magana ba sai cigaba da bugun da akayi, tayi saurin isa ta sake cire lock din, ta dan bud'e kofar kad'an ta yadda ba za'a ganta daga waje ba tace
"Waye?"
"Bako ne, maigidan yananan?"
"Baya nan."
"Toh... Ko dai ba address din bane, ko ba gidan Dr Sultan bane?" Yace cike da tantama
"Nan ne, amma baya nan."
"Toh Toh... Madallah, idan ya dawo kyace masa nazo."
"Toh wa za'a ce masa?"
Shiru be amsa ba, ta sake tambaya shiru, sai ta dan leka kanta wajen kad'an sai taga ashe ma ya tafi, rufe kofar tayi tana komawa ciki dan tuni Afrah ta shige.
"Wai waye naji kin dad'e."
"Wani ne, bansan waye ba wai Sultan yazo nema."
"Ko sune na gansu a kofar gida suka bini da kallo, har ma na dan ji na tsargu domin yanayin su be min ba, kamar marasa gaskia wallahi."
"Toh..."
"Idan kunyi waya ki tambaye shi ko akwai bakon da yake expecting, dan yadda k'asar nan tamu ta lalace, gashi kiwon mutum ake ba dabba ba."
"Malama karki tsorata ni,babu abinda zai faru, tsarguwa kawai kikayi dallah."
"Toh Allah yasa." Tace tana dariya ganin yadda Amrah ta nuna alamun tsoro, sai ta kauda maganar suka shiga wata amma k'asan zuciyar ta sai taji ta kasa aminta da mutanen da ta gani dazun, addu'a tayi kawai ba tare da ta sake daga maganar ba dan yadda Amrah ta nuna ta tsorata karta kara tsoratata.
Ganin azahar ta tawo yasa suka shiga kitchen a tare, suka girka noodles suka ci a kitchen din sannan suka dawo falon suka cigaba da kallo suna hira, lokaci lokaci Amrah na kiran wayar Sultan amma switch off, da ta ga haka sai ta dinga tura masa message duk sanda ta kira tasan idan ya kunna dole zai gane. Addu'a ta bishi da shi suka cigaba da hira da Afrah Amma k'asan zuciyar ta babu dadi tana tunani da fatan Allah ya tsare shi ya kaishi lafiya ya kuma bashi nasara a abinda ya saka a gaba.
***Daga nesa ya hange shi tsaye ya na d'an dube dube, ya tsaida me napep din ya biya shi sannan ya fito yana gyara zaman jakar dake rataye a kafadar sa ya nufi inda yake. Tun kafin ya karasa ya ganshi yayi saurin tawowa suka hadu a hanya. Kallon tsanaki Sultan yayi masa kad'an sannan ya mika masa hannu suka gaisa yana karantar yanayin sa cike da nazarin abubuwa da dama a tattare dashi, na farko yanayin shigar sa sai kuma yanayin da fuskar sa take ciki wadda ta sake saka sultan din cikin wani yanayi na tunani.
"Muje ko?" Yace bayan ya dan kalli agogo samfurin apple dake hannun sa. Har ya fara tafiya sai ya tsaya
"Musa ko?
"Eh Musa ranka ya dad'e."
Jinjina kansa yayi kad'an
"Kai ne jagoran tafiyar bani ba, kai ya kamata ka shiga gaba."
"Haka ne, bismillah." Yace yana nufar wata bakar mota, dakatawa Sultan yayi da bin sa yace
"Bana tunanin zuwan mu a motar gida zai taimakawa abinda zamu je yi."
"Tabbas ba zai taimaka ba, dama iya kar mararrabar zamu idan yaso sai mu karasa daga chan."
Jinjina kai yayi kad'an sannan ya bi shi ya shiga motar,shi kuma yaja suka tafi.
Tafiya ce me matukar nisa wanda tun sultan na duba dukkannin bayanan daya tatatara har ya hakura ya dangana da kallon hanyar yana sake lafewa a jikin motar da babu abinda yake tashi a cikin ta sai karar na'urar sanyaya waje.
La'asar sakaliya suka isa inda musan yace, ya gangara gefen wata yar karamar hanya zuwa wani madaidaicin gida wanda ya zama kamar shi kad'ai ne a wajen. Shi dai Sultan be ce komai ba yana bin komai da ido.
"Yallaabai ina dan zuwa dan Allah."
Da ka ya amsa masa ya fita da sauri ya shiga gidan, jim kad'an suka fito da wasu mutane su uku, suna magana har suka karaso wajen motar, ganin haka yasa SULTAN bude kofar ya fito.
"Barka da zuwa." Suka fad'a a tare har suna dan russunawa.
"Ranka ya dad'e wannan shine zamu bashi ajiyar motar, wadannan kuma su zasu dauke mu har Masarautar Saji Idan Allah ya yarda."
"Allah ya kaimu lafiya." Kawai yace