← Book details Abinda Ke Cikin Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 46 OF 108

Sashe 46

Abinda Ke Cikin Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Numfashi marar amfani ba, ta iya yiwuwa kai a gurin ka kana yin mai amfani, sabanin ni da zan shiga gidan mutumin da ban san ko waye ba, ta ya za kai kace ni ina numfashi? Ka wahalar dani Mas'oud, ka koyar dani darasi mai matukar wahalar da zuciya. Bana tunanin zan san meye jin dadi da yanci a cikin rayuwa ta, zanje na rayu da wani ba kai ba Mas'oud, kana ji kana gani za'a kai ni inda bana so. Dan Allah Mas'oud ka rufa min asiri kar na rasaka please ka ceci rayuwa ta saboda da kai ta fara soyayya....”

Cak numfashin sa ya tsaya na dan wani lokaci, baki bude yake kallo na cikin zare ido da alama yaji maganar ne cikin tsakiyar kansa. Ya matso dap dani har ina iya jiyo bugun da zuciyar shi take yi da karfi sannan kuma cikin sauri. Kamar zai rike ni haka ya soma yi yana magana a daddaburce hankali a tashe.

“Dan Allah idan mafarki nake yi wanda yake kusa dani ta yi gaggawar tayar dani. Wallahi tunda nake ban taba yin mummunan mafarki ba irin wannan.” Cikin kuka murya a dashe nace dashi.

“Ba mafarki kake yi ba da gaske ne wannan maganar da nake maka. Sai dai nima ina fatan kawu daddy ya dawo yace min da wasa yake yi a yau din nan.”

“Innalillahi wa'ina ilaihir rajiun na shiga uku ni Mas'oud wannan wace irin mummunar kaddara ce? Oum Waleed dan Allah karki bari a rabu mu, wallahi ina sonki. Gobe zan turo uncle's d'ina ayi maganar koda basu taho da kudin ba, su san da zaman mu ni dake kar su rabu mu dan girman Allah.”

Yadda yake magana a gigice shine ya sake tayar min da hankali na tabbatar da idan bamu yi da gaske ba komai zai iya faruwa. Kamar na juya na tafi saboda naga shima ya fara zubar da hawaye, sai dai na juyo ba tare da na bari mun had'a ido ba nace masa.

“A wannan gabar bani da ta cewa Mas'oud, sai dai ina fatan zaka yi duk yadda zakai wajan karkato da zuciyar kawu daddy har ya amince da auran mu. A shirye nake tsab da idan ya kuma tuntuba ta da maganar ka zan amsa dan kar na cuci kai na, amman fa ni bazan iya zuwa yanzu nace dashi ba zan auri wanda ya bani ba, saboda yadda baka cancanci wulakanci a guri na ba, haka ma kawu daddy be cancanci tozarci daga gare ni ba. Dama tuntuni damar tana hannunka, yanzu ma tana hannunka sai ka nema mana mafita.”

Ina gama magana na ruga gida da gudu ina wani sabon kukan wanda yafi na farko zafi da radadi. Ban san yadda ya kare ba a compound, sai dai wajan karfe goma naji kawu daddy ya shigo yana yiwa Mami magana.

“Ikon Allah, yaran zamani sai addu'a kawai.”

“Alhaji me kuma aka yi maka? Ko samari ne ka hadu da su akan titi marasa kunya.” Yana kokarin zana ne yake cewa.

“A a babu ko d'aya daga ciki. Yaron nan ne Mas'oud abokin aikin Khadija. Ina jin ko labarin auran ta yaji yanzu shine ya kawo kanshi wai shi da ita sun dade suna soyayya tare da burin yin aure, wai yana ta shirin turo manyan sa sai yaki ance an bayar da ita. Shine nace da me ya hana shi bayyanawa tuntuni sai yanzu?”

Jin maganar aure na ne yasa Mami sauya fuska, can kuma sai ta ce tana zuba mishi juice a glass cup.

“Kaima Alhaji har yanzu ka ki gaya mana waye wanda zaka aura mata. Ni ban taba ganin inda aka yi wannan abin ba, ko dan bani na haifi Dijen ba shi yasa ake ta boye min shi?”

“Ko daya wallahi Hajiya, abin da yasa ban fada ba shi angon ne ya roki arzikin dan Allah karna fada sai ranar auran. Kinji dalilin da yasa ko ita Khadijan ban gaya mata waye ba.”

“Ai shikenan, idan ta fashe ma gani ai.”

“Zaku gani kam insha Allahu. Yaron ma na bashi hakuri nace ya yi hakuri aure nan da rana ita yau za'a daura shi da ikon Allah.”

“Uhmm Alhaji kenan, kana bani mamaki tun zuwan yarinyar nan gidan nan, komai na ta baka nuna min shi kai tsaye sai ka yi kwana kwana. Amman ba komai lokaci ne tunda gashi ta kusa tafiya nata gidan.”

“Ki dena yi min fassara akan komai Hajiya. Yarinyar nan marainiya ce kin kuma san yadda Allah ya bayar da amanar rikon maraya. Dan Allah ki tayani faranta mata har zuwa ranar da ya rage mata a cikin gidan nan.”

Tamkar ya yi da gunki ta yi masa banza hakan ya kara tabbatar masa da cewa idan ya gaya mata wanda Dije zata aura akwai rashin hankali. Sai ya kuma jan bakinsa ya yi shiru be sake cewa komai ba har lokacin kwanciya ya yi ya tafi daki. Ni kuwa tunda naji yace ya bawa Mas'oud hakuri na koma gefe naci gaba da kuka na wanda babu mai lallashi.

*MASARAUTAR BASANNABAS*
(Sarki Salman Aliyu Salman SAS)

Kafin kace wani abu tuni sarki Salman ya kuma susucewa akan son auran Dije, sarautar ta kuma fita daga cikin zuciyar shi ta yadda ko sunan sarki baya son yaji an ambata masa. Duk da ya rage sauran sati daya a daura auran sa, ga kuma ta fiyar da aka ce zai yi zuwa Cyprus, kuma babu wanda za a fasa indai yana da rai da kuma lafiya a jikin shi. Komai dama da ya dace ango ya yiwa amarya, Sarki Salman ya bawa Alhaji Isma'il kudadenda za'a siya. Shi kuma ya kai wa wata mata kwangilar hadowa ba tare da ya sanar da ita ko na meye ba, daman ita aikin ta kenan, duk abinda mutum yake bukata a had'a masa na aure ko na gida tana yi a biya ta.

Yana zaune a cikin fada yama rasa abin yi saboda Sam baya cikin hayyacin shi, ya jiyo muryar Ciroma yana gyaran murya yana cewa.

“Allah ya taimake, rana ita yau shine ranar da zaka je taron nan, an shirya maka komai sai fatan zuwa da dawowarka kawai, Allah ya kara maka lafiya.”

.._Afuwan! Kunji shiru ko? Wallahi kwana biyu inata fama da chronic ulcer. Har takai na kwanta a asibiti na yan wasu kwanaki shysa kukaji shiru, Shekaran jia akai discharging. Ina fatan na same ku lpy? Nagode k’warai da addu’oin ku. KIBIYAR ajali zai cigaba da samuwa Insha Allah da zarar naji karfin jiki na sosai.. Na gaishe ku, Gaisuwa mai kima.._

ZAFAFA BIYAR
NA KUDI NE:::

Duka BIYAR 5 zaku samesu akan garabasar naira 700 kacal,

Guda hudu 4 Kuma 500,

Guda uku 3 Kuma 450,

Guda biyu 2 Kuma 400,

Guda daya akan 300.

Ma'ana
Each one is 300
2 is 400
3 is 450
4 is 500
5 is 700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO- *0812652655*
ACCOUNT NAME- *HAFSAT LAWAN GAMBO*
BANK NAME: *ACCESS BANK*

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

*+234 903 234 5899*

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

*09033181070*

Karku Bari ayi Babu ku domin wannnan salon na daban ne
SABUWAR SHEKARA
SABON SALO

TEAM#ZAFAFABIYAR🔥
[4/7, 6:44 AM] Maman Maryam: www.instagram.com/zeeherbalsaphrodisiac.

_*ASSALAMU ALAIKUM SISTERS..!_*

_*INA MASU NEMAN INDA ZASU SAMU INGANTATTUN: _*
_*HERBALS APHRODISIAC MA’ANA NA GARGAJIYA BANA HADIN BATURE BA MAI SIDE EFFECT..?_*

_*TO KU MATSO, DOMIN NESA TAZO KUSA.._*

_*ZEE HERBALS APHRODISIAC_*
_*ZEE HERBALS APHRODISIAC_*
_*ZEE HERBALS APHRODISIAC_*

_*MUNZO MUKU DA INGATTTUN KAYAYYAKI WANDA ZASU GYARA KI CIKI DA WAJE_*

_*MUNADA SUPPLEMENT MASU GYARAN JIKI DANA FATA, WANDA ZASA SAKI KIYI SHEKI FATAR KI TAYI LAUSHI. TAYI LUWAI LUWAI TAMKAR TA JARIRAI_*

_*AKWAI SUPPLEMENT NA KAYAN MATA WANDA ZASU GYARA KI, KIJI KI TAMKAR BUDURWA, SUPPLEMENTS DINMU BASU DA SIDE EFFECT, DOMIN AN HADO SU NE DAGA INGATTATTUN ITATUWA, WATO NATURAL PRODUCTS NE ACIKI._*

_*KAI BA ANAN KADAI MUKA TSAYA BA, MUNA DA INGATTUN KAYAYYAKIN MATA WANDA KESA KISHIYA KWAFA, WANDA DUK INDA SARAUNIYA TAKAI KIN WUCE, WANDA ZASU TSATSO MIKI MARTABAR KI DA KIMAR KI_*

_*AKWAI INGATTATTUN MAGUNGUNA, NA CUTUTTUKAN DA SUKA SHAFI DAN ADAM DAMA JINNU.. KAI DAMA WANDA BAMU AMBATA BA.. ZEE HERBALS APHRODISIAC (MASARAUTAR INGATTATTUN MAGUNGUNA KENAN)_*

_*KYAU, ARHA, INGANCI, RAHUSA... SAI ZEE HERBALS APHRODISIAC_*

_*MANHAJOJIN MU NA SOCIAL MEDIA: KAMAR INSTAGRAM DA WHATSAPP DAMA NAMBAR TARHON MU: DOMIN SHIIGA KUGA IRIN KAYAYYAKIN MU TUNTUBE MU TA_*

_INSTAGRAM LINK DIN MU:_

www.instagram.com/zeeherbalsaphrodisiac

_WHATSAPP LINK DIN MU:_
https://Zeeherbalsaphrodisiac.whats.bz

_NAMBAR TARHON MU_
08169380189

_*DA A BAKA LABARI GWARA KA BAYAR.. KIZO A DAMA DAKE YAR UWA, KI ZAMO DAYA DAGA CIKIN KASAITATTUN MATA MASU AJI.. MUNA GARIN KATSINA, SANNAN KAYAN MU MUNA BADA SU AKAN FARASHIN SAYA ‘DAI DAI KO SARI.. MUNA TURA KAYAN MU A KO’INA A FADIN NAJERIYA._*

_*BE YOUR OWN BOSS, BUILD YOUR OWN EMPIRE, BE THE WHOLE WORLD OF HIS MAJESTY( YOUR HUBBY) BE THE ONLY CENTER OF ATTRACTION WITH ZEE HERBALS APHRODISIAC. OUR PRODUCTS LASTS LONGER AND VERY EFFECTIVE. NO SIDE EFFECTS. AVAILABLE N WHOLESALE/ RETAILS.. DELIVERY IS NATIONWIDE. 100% TESTED AND TRUSTED_*

*2___1*

Samun kansa ya yi da jinjina kai alamar yaji sai dai tunanin sa yana ga yadda za'a daura aure baya garin sai kace na asiri. Amman kwarin gwiwar da jarumar zuciyar shi take bashi shine ya sanya shi jingine fargabar tashi da take neman ruguza masa lissafi.

*KHADIJA (DIJE)....*

Tun daga ranar da kawu daddy ya sanar dani ranar aure na ban sake fita ko nan da compound ba, ma'ana tun ranar da Mas'oud yazo naje gurin shi. Shi kuwa tun yana kira na ina kin dagawa har ya hakura sai dai ya kira Shukrah da ya karbi lambar ta dan ya dinga jin bayani game da ni. Hankali na be sake tashi ba sai ana sauran kwanaki uku kawu daddy ya kira ni wai za a kawo kayan lefe, a gabansa nace to, amman a raina fata nake Allah yasa motar masu kawowar tayi hatsari duk su mutu kowa ma ya huta.
Chapter 46 · 0% Book details