Sashe 85
Abinda Ke Cikin Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
"Saboda kazo mu karasa abinda muka fara, ban dauka zaka saba alkawari ba tun farko, idan ba haka ba, me yasa ka chanja shawara akan bani zoben?"
Kure shi da ido Sultan yayi, sai kuma yayi murmushi ya murza zoben sannan yace
"Na zata mun wuce wannan wajen, idan ma maganar saba alkawari ne toh kaine ka fara, saboda me yasa zaka saka iyali na a ciki?"
"Saboda alamun da ka nuna ba zaka bayar da zoben ba, tun bayan da ka dawo da Musa gida na tabbatar da haka."
"Menene amfanin zoben ne wai har haka?"
"Kana nufin baka sani ba?" Dayan yayi maganar
"Um um, ban sani ba, na dai ga kawai zobe ne kamar kowanne zobe ma, me yasa kuka damu dashi har haka? Ko ance musu shine tikitin shiga aljanna ne?"
Kallon juna sukayi, suka yi magana da juna ta yadda Sulthan din ba zai gane ba.
"Ka gane? Shi wannan zoben kamar wani sign ne na family din mu, tun farko a gidanmu ya kamata ya zama, toh sai akayi mana fin karfi har ya bar hannun mu, shine muke so ya dawo wajenmu, babu wani amfani da yake dashi bayan shaidar nan kawai."
"Madallah, kace idan nazo zaka fad'a min abinda zai bani mamaki, duk da dama kai din baka rabo da bada mamaki, tun da har ka iya gabatar min da bayin Allah nan a matsayin iyaye na, ina fatan ka sallame su ka biya su kudin aikin su har da kari, domin aikin su yayi kyau sosai, zasu mafi kyau da wasan hausa."
"Ba wannan maganar bace yanzu Sulthan, magana daya ce, akwai muhimman abubuwa da na sani game da kai, kuma nayi alkawarin ko da ban hada ka da su ba,zan fad'a maka inda zaka neme su, na farko iyayenka, na biyu kannenka da suka taso tare damu, na uku...."
"Ina ka kai ta?" Ya katse shi
"Wa?"
"Safiya!"
"Ina kyautata zaton tana cikin Masarautar, sai dai bani da tabbacin hakan saboda har yanzu ban tabbatar din ba."
"Ina jinka..."
"Idan har ka yarda zaka bani zoben nan, nayi maka alkawarin fad'a maka komai."
Zare zoben Sultan yayi, hasken ya kara tashi me karfi, duk suka zuba ido cike da mamaki, karfin zoben yayi yawan da zai dauki hannun Madaki ko mukarraban sa, dama a lokacin da yake ba a hade bane,duk da haka Madakin me karaya ba, ya matso ya mika hannu Sultan ya dora masa zoben a saman tafin hannun sa.
"Ina sauraren ka!"
Cikin tsantsar farin cikin da Madaki be taba samun kansa a ciki ba, yake kallon zoben yana kallon mutumin, tsawon lokaci abinda ya hana masa cikar burin sa kenan,
"Ina sauraren ka!" Sultan ya kara magana yana hard'e hannayen sa
"Kamar yadda nayi alkawari, yadda ka cika min buri na kaima zan cika maka, zan fara da baka tarihin zoben nan da abinda zai iya yi."
"Kasantuwar Zoben nan ya samo asali ne a wani lokaci, lokacin da Sarautar Saji ta samu matsala, alokacin da aka rasa sarkin da za'a nad'a a cikin yayan Sarki Abubakar Muhammad Moddibo Saji, Wanda ya kasance kaka a wajen Sarki Bello da Sarkin Usman wanda ya kasance mahaifin ka, a lokacin ne Sarki Abubakar ya hadu da wani mutum ya fita ran gadi, ya bashi wannan zoben ya kuma tabbatar masa da duk wanda zoben nan ya zaba shine zai yi Sarautar Saji, haka yazo gida ya kira dukka yaran sa, kowanne aka bawa zoben sai zoben ya fad'i daga hannun sa, har aka zo kan Sarki Muhammad Moddibo Saji wanda shine kakan ka, sai zoben nan ya zabe shi, tun daga lokacin hakan ya zama al'adar Masarautar Saji, babu me Mulkarta sai wanda ya mallaki zoben nan. Bayan kakanka Sarki Muhammad Moddibo Saji, sai mahaifin ka shima ya hau, ya kuma cigaba da kasancewa da zoben nan duk kuwa da shi be wani yarda da zoben ba kasancewar sa dan boko. Sai dai be sani ba,Sarki Bello yayi amfani da karfin Malaman tsubbun sa, ya chanja komai akan zoben, inda ya zama duk wanda ya mallaki zoben toh tabbas shi ne zai karbi mulkin, saboda haka yasa nayi ta kokarin samun zoben, saboda daukar fansar abinda Sarki Bello yayi wa ahalin mu baki daya bayan hawan sa kan karagar mulkin, ya kore mu daga Masarautar kora irin ta wulakanci. Sai dai ban samu damar daukar zoben ba duk kuwa da na samu damar hakan ba adadi, babu wanda zai iya kai hannu akan zoben sai kai kad'ai sultan, saboda karfin zoben duk wanda ya dauka kafin ka dauke shi zai iya rasa ransa ma baki d'aya."
"Me yasa sai ni kad'ai zan iya?"
"Saboda kai ne wanda zoben ya zaba tun kana cikin mahaifiyar ka, shiyasa suka salwantar da cikin tun kafin ka zo duniya, sai kuma Allah ya kaddara sai ka taka."
"Me yasa zoben ya zabe ni? Bayan komai da kaga ya faru da bawa mukaddari ne daga Allah, dama chan an rubuta zai zama abun ko zai samu abun."
"Sultan baka san sha'anin Sarauta ba."
"Muhammad shine yaron da Safiya ta raina? Ina wanda kai ka tafi dashi? Yana raye ko ya Mutu?"
"Shine, kuma shima dayan yana raye, wanda akayi nufin kashe su ni kuma na taiamaka wajen tseratar dasu."
"Yana Ina?"
"Sultan..."
"Yana Ina?" Kallon zoben Madaki yayi, sai kuma ya kalli Sultan yayi murmushi ya matso daf dashi yace
"A duk labarin nan, wannan zaifi maka dadin sauraro, ina fatan ka bani tukwaici me girma."
"Ina jinka."
Wayar sa ya ciro ya nuna masa wani hoto
"Kasan wañnan?"
Shiru Sultan yayi ya kurawa hoton ido, babu ko kiftawa amma ya kasa magana, ya rasa me zai ce sai kawai ya daga kansa a hankali zuciyar sa na bugawa da sauri da sauri yace
"Na sanshi."
"Good. " Ya sakar ma Sultan din wani shu'umin murmushi, girgiza kai Sultan yayi yace
"Kana nufin...?" Kafin ya karasa Madakin yace
"K'warai da gaske, kana mamaki ne? idan kana mamaki kayi bincike shi, zaka samu sauran bayanan a wajen sa."
Da sauri ya mike ya nuna shi da hannu
"Ban yarda ba, ba zan yarda ba kuma saboda kai din ba abin yarda bane, babu karyar da ba zakayi ba domin cikar burin ka."
"Zaka iya bincike idan har baka yarda ba, bani da amsar da zan baka domin har yanzu ban samu bayanin komai daga gareshi ba."
Komawa Sulthan din yayi ya zauna, ya taba Bluetooth din dake makale a kunnen sa, wanda sai a lokacin Madaki ya lura dashi, yayi saurin tashi cikin tsananin tashin hankali
"Kar muyi haka da kai Sultan!"
"Arrest him!" Yace a lokacin da kofar falon ta bud'e, suka shigo a guje su wajen goma suka zagaye Madakin.
"DSS!" Ya furta yana zaro idon sa
Sara masa Sultan yayi, ya matso gaban sa, yasa hannu ya bud'e tafin hannun sa da ya dunkule zoben, ya zare yana cigaba da murmushi
"This belong to me, greediness din ka, ya kaika inda kake a yanzu, idan baka yi bayanin inda ka kai min dan uwa ba zakayi bayani a office din su, kasan kuma su ba kamar roundom police bane da zaka yi bribing da banzan kud'in ka ba."
"Amma kasan ba haka mukayi da kai ba?"
"Kai ne ka koya min, kuma dan ka, dan cikin ka shine ya taiamaka har hakan ta kasance!"
"Ameer!" Ya furta da karfi yana zaro ido
"Kuje dashi Sir! Thank you so much."
"Karka damu Dr, zamuyi abinda ya kamata."
Tusa keyar Madakin sukayi suka fito dashi, sai a sannan ya ga yadda akayi wa cikin gidan, an tattara dukka ma'aikatan an zuba su daki Daya. A Mota suka sashi suka tafi dashi tare d wannan wanda suke taren. Wajen motar sa Sulthan ya nufa yana jin wani karfi na saukar masa,yana jin sai yanxu yayi abinda ya dace. Shafa fuskar sa yayi ya saki murmushi
"Canada!" Ya furta a hankali yana lumshe Ido
"He can't wait ya isa garesu." tare da amrahn sa, tare da yan uwan sa da yake fatan samun su, sai kuma abinda Madakin ya nuna masa ya dawo masa, tsoro ya shige shi, me yasa Madakin zai kawo masa shi a matsayin wanda zai nema, me yasa be gaya masa komai kai tsaye ba kamar yadda ya bàshi labarin zoben, ko dai da gaske yake? Nooo ba zai yiwu ba!
***Chan bayan asibitin Maman Yara ta nufa, ta samu wani waje da babu komai ta ciro layoyin nan, ta saka ashana ta kyesta musu wuta, tana kallon yadda wutar ta tashi sama sosai dan har sai da ta ji tsoro, kafin kuma wani bakin abu baki kirin ya fito daga ciki yayi sama shima....
Yau dai ga guntun page, bani da enough charge. Muje zuwa Canada, it's gonna be fun!!!!!! ©® Hafsat Rano
Page 44-45
***Tana kallo har wutar ta gama ci, ta watsa ruwa ta karasa kashe ta, zuciyar ta babu dadi ga wani irin kanta da ya hau sarawa kamar zai cire. Dafa wa tayi da k'yar ta karasa dakin nasu ta kwanta zazzabi na rafke ta.