← Book details Abinda Ke Cikin Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 102 OF 108

Sashe 102

Abinda Ke Cikin Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

RanoNet
www.ranonet.com.ng
Register for your amazing data at a very cheap price.
Mtn 1gb @300 naira only

***
Isowar su yayi daidai da faduwar gaban Mah-Mah, taji kamar an dauke wani abu me matukar muhimmanci a rayuwar ta, ta mike da k'yar, lokacin da taji an bud'e kofar an shishigo, ta dauki hijab dinta da k'yar ta saka ta fito, suna zazzaune a falon, daya bayan daya ta bisu da ido kafin ta karaso ta zauna tana musu sannu da zuwa, idon ta ya tsaya akan Gimbiya dake zaune kusa da wani dattijon mutum wanda bata raba daya biyu shine uban gidan mijin nata, sai dai yadda ta tsammani ba haka ta gani ba, ta zata zata ga wasu iyayen kuma daban wanda suka iso tare da Sultan, amma kuma ganin yadda Sultan din ya zama free da mutanen da tayi wa kallon bakin Daddy sai taji tunanin ta ya kwance.
   Gaisuwar da aka shiga yi tsakani ma duk hankalin ta baya kai, ta tafi tunani da addu'ar Allah yasa Sultan din shi kad'ai yazo, muryar Daddy ta tsinkaya a kanta yana maimaita

"Hajiya ko zasu shiga ciki?"

Da sauri tace

"Bismillah Hajiya ,muje ciki."

Murmushi Gimbiya tayi mata, ta maida mata itama sannan ta mik'e suka nufi ciki suka bar su a falon.
   Tashi Sultan yayi, Safwan ma ya mike suka fita, Maimartaba ya bisu da kallo Daddy na lura dashi, yayi murmushi me kyau sannan ya maida hankalin sa akan sa

"Nagode Nagode Nagode Alhaji Sulaiman, baki na ba zai iya kwatanta girman da kake dashi a waje na ba, nayi matukar farin ciki da na same ka a matsayin wanda sultan yake hannun sa, duk da dama na san cewa ko waye ya rike shi haka ba karamin mutum bane me girma da karamci, amma kuma ganin ka ya saka na kara tabbatar da cewa kaidin managarci ne, mutumin kirki ne wanda yasan ya kamata, kayi kokari wajen tarbiyyar su kuma har gobe kai ne uban su, basu da wani uba sama da kai, ina fatan amincin mu ya dore har zuwa zannatul Firdaus."

"Amin Maimartaba, Amin ya Allah, ni kaina nayi farin ciki da yadda al'amarin ya juye, haka dama Allah yake al'amarin sa, wannan din tsarin Sa ne, shi ya ga dama hakan ta kasance bamu kuma isa muce don me?"

"Haka ne, haka ne." Maimartaba yayi maganar yana girgiza kansa, yana jin farin cikin kasancewar mutumin da yake jin sa tamkar danuwansa a matsayin wanda ya rik'e mishi yara, riko irin na uba nagartacce. Sai kuma tunanin Muhammad ya fado masa, shi babu ilimin haka Allah ya kaddaro masa, amma babu komai hakan ma alhamdulillah.

"Ina fatan Sultan ya sanar dakai komai game da labarin Safwan da yadda ya kasance a hannun mu."

"Ya sanar dani, hakan ya kara girman ka a waje na, ka sani ba kuma zan dauke maka shi bane, har gobe daga Safwan har sultan duk ikon ka ne, ina so dai muyi zama na musamman saboda halin rayuwa, daga nan sai mu dunguma mu tafi Masarauta, idan komai ya daidaita shikenan."

"Allah ya bamu sa'a, Nagode Nagode da dukkan abubuwan da kayi min a rayuwa, Allah ya saka maka da alkhairi."

"Kayya, nine zan maka wannan godiyar domin samun mutum kamar ka ba karamin abu bane, gaskiya yanzu tayi karanci a cikin al'umma, abu ne da yafi komai sauki dan uwan ka yaci amanar ka, ya ha'ince ka idan ka amince masa, ni kaina na hadu da sharrin dan uwa na, yayi komai dan kawai ya samu abinda idan ma ya samu anan duniya zai yi shi kuma ya bar shi, kafin shi wasu sunyi sun shude haka za'a yi wasu ma bayan shi su shude, haka rayuwar take baki daya, yau kai ne gobe ba kai bane."

"Tabbas haka ne, mutane ne basa ganewa, shiyasa ake yin abubuwa kawai ba tare da tunin gaba ba, son zuciya ya rufe wa mutane da yawa ido sun manta da ko babu tsufa akwai mutuwa, dole ne kuma ka girbi abinda ka shuka alkhairi ko sharri

***Tuni Gimbiya ta saki jikin ta da Mah-Mah, itama Mah-Mah da farko ta kasa sakewa amma ganin yadda matar ta sake da ita sosai yasa itama ta saki jikin ta, tare suka ci abinci tayi ta santin girkin da kayan snacks din, murmushi kawai Mah-Mah tayi tana jinjina wayewar matar, ruwan wanka ta had'a mata ta shiga wankan ita kuma ta fito ta saka fati ta tattare kayan da suka ci abincin ta gyara wajen.
   Zama Mah-Mah tayi a falo ta jira ta fito, chan sai gata ta fito ta shirya ta zauna tana kallon tv fuskarta fayau cike da farin ciki wanda kallo daya Mah-Mah tayi mata ta gane yanayin da take ciki da zuwan ta k'asar.

"Tunda muka zo banga Amrah ba?" Daya maganar tana kallon Mah-Mah

"Auw nan kusa damu ne gidan su ai, ta chan ta fara zata shigo anjima k'adan nasan."

"Ok Allah sarki, nayi kewar ta ne, Allah ya kawo ta."

"Amin." Mah-Mah tace maganar na tsaya mata a makwallato, tayi kewar ta? Yaushe sukayi sabo haka har da zata ce tayi kewar ta?"

"Allah sarki ai tana da shiga rai duk da rashin son maganar ta" Mah-Mah tace tana son maganar tayi tsawo ko ta dauki haske

"Tana da shiga rai kam, jinta nake kamar yar dana haifa, naso 'ya mace sosai Allah be bani ba, shiyasa zuwan da sukayin nan yasa muka shaku sosai, gata da hankali da nutsuwa."

"Haka mahaifiyar su take ai,mace me kirki."

"Allah sarki..

"Sun samu tarbiyya sosai ai."

"Ai daga gani, naji dad'i da ta kasance sirikar mu, sannan ta dace da Sultan, shi dinma ya samu tarbiyya nagartacciya,

Shigowa Sultan da Safwan sukayi hannun su sarke da juna, hakan ya saka suka maida hankalin su wajen su, fara'ar da Mah-Mah ta gani shinfide akan fuskar Ummi ya saka ta karkare abinda take tunani.

"Kuzo yaran albarka." Ummin tace tana mikewa, a Zbayyane take koman ta babu kunya, suka zube a gaban ta, ta kama hannun su dukka tana jin da ace yan biyun ta sun rayu da yanxu sun zama kamar Safwan, ina Aminatu ta shiga?  Tunanin ya gifta mata, tayi saurin girgixa kanta bata so tunanin ya bata mood dinta.

"Wai ko a gidan ku Sultan ya sauka ne?" Mah-Mah da mamaki ya kasa barin ta, tayi maganar kirjin ta na bugawa

"Achan suka zauna gaba daya, ai cewa nayi babu inda zasu sauka da ya wuce wajenmu, dole suka tattaro kayan su suka dawo."

"Angode da dawainiya."

Mah-Mah tace tana jin relief,katse mata hanzari Sultan yayi da maganar sa da bata zata ba.

"Mah-Mah..."

"Na'am Sultan?"

"Sune iyayena..."

"Na'a..aam!??"

"Anjima in sha Allah za'a zauna sai ayi duk maganar da za'a yi, akwai bakin da zasu zo anjima k'adan in Sha Allah, ina fatan dukkanmu mu amfana da zaman, ina kuma fatan a samu fahimtar juna a zaman da za'a yi."

Sultan yayi maganar kansa na k'asa.

    Jikin Mah-Mah ne yayi sanyi, ta juya da sauri ta kalli Safwan da suke magana da Ummi cikin farin ciki, bata jin me suke cewa saboda yadda gaba daya jinta ya dauki a lokacin, kwalla ta taru a idon ta, Sultan da yaga komai yayi sauri mikewa

"Mah-Mah ina magana." Ya juya yayi hanyar corridor da zata kaika bayan gidan, tashi tayi da k'yar tabi bayan sa,ta same shi a tsaye ya hard'e hannuwan sa, yana ganin ta ya dire akan kafafuwansa, ya hade hannayen sa waje daya yace

"Mah-Mah dan Allah kiyi hakuri, nasan ba abu bane me sauki a wajen mu baki daya musamman Safwan, dan Allah kiyi hakuri."

"Sultan me yasa baka son farin ciki na? Ashe banyi maka abinda na chanchanci farin ciki ba? Ashe baka dauke ni a matsayin uwa ba Sultan? Kasan yadda nake ji? A duk ta dalilin ka? Kaine ka dage da bincike har ka gano wannan abun, duk da kuma kasan yadda abun zai taba ni amma ka share, burin ka kawai yadda zaka kuntata min ka hanani farin ciki, saboda kuskure daya da nayi kuma na baka hakuri akai, me yasa Sultan? Me yasa?"

"Wallahi Allah shine shaidata, banyi hakan domin nasan abinda zai faru ba kenan, ban taba tunani ko hasashen hakan ne zai kasance ba, ta yaya zan so tashin hankalin ki bayan ke din kece kikayi min dukkan gata, kike rik'e ni tamkar dan cikin ki, me yasa zan so ki shiga damuwa?"

"Saboda taurin zuciya irin taka Sultan, saboda nayi maka laifi shine nima kake so ka kuntata min, idan har gaskiya kake fad'a me yasa ba za'a bar maganar Safwan ba? Me yasa ka dage lallai-lallai sai ka musguna min ka raba ni da abinda ka san bana had'a soyayyar sa da kowa?"

"Saboda hakan shine daidai, saboda dole ne Safwan yasan iyayen sa, yasan ba mune muka haife shi ba, yasan wadannan bayin Allah masu karamci sune iyayensa, sannan suma su san dan su."

Daddy yayi maganar fuskar sa a had'e tamau, juyowa sukayi da sauri ta kalle shi, ya karaso yana sake tamke fuskar sa dan har ga Allah Mah-Mahn ta soma fusata shi. Dora yayi ya cigaba bayan ya tsaya a gaban ta

"Idan har kince ba'a miki adalci ba, su kuma iyayensu suce me? Mahaifiyar su tace me? Rasa yara har uku tsawon shekaru ba abu bane me sauki, bata taba sanin ya kake ji ba akan yayanka, gwara ke kinyi experiencing motherhood amma ita fa? Kinsan irin bakin cikin da ta kunsa? Kinsan me tayi going through all this year's? Baki sani ba, kawai farin cikin ki kike Kira, karki zama mace me son kanta, me butulcewa rahmar ubangiji."

"Dan haka dole Safwan shima ya san iyayen sa, su sanshi, ya rage nasu suce ya zauna damu,ko kuma su bukaci dan su kusa da su, duk hurumin su ne, ikon su ne ba namu."

"Iyayena Daddy? Ba kune iyaye na ba dama!!!?" Yayi maganar hawaye na zuba a idon sa sosai, da sauri Sultan yayi wajen sa, ya rik'e shi a jikin sa yana jin hawayen na neman zubo masa shima amma yayi ta maza ya tare su, dan baya bukatar su yanzu
Chapter 102 · 0% Book details