← Book details Abinda Ke Cikin Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 64 OF 108

Sashe 64

Abinda Ke Cikin Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A hankali ta tura kofar ta shiga kamar barauniya, ya na zauna a k'asan carpet ya kalmashe kafar sa dake sanye cikin bakar safa, hannun sa rik'e da cup yana shan tea suna magana da Adnan.

"Bafa za'a maida min daki dandalin masoya ba ehe."

Saurin sauke kanta k'asa tayi kunyar ya Adnan na sake kamata

"Idan mutum yaji haushi yayi zuciya shima."

"Haka kace? Karka manta yanzu matsayin yayanka nake."

"Au auw, haka ne fa, sorry babban yaya, na tuba."

"Yafi dai." Yace yana karasa sanya takalmin sa, yazo yayi hanyar fita yana cigaba da mita.

Ajiye cup din yayi ya mike tsaye sannan ya bud'e hannayen sa.

"Come please."

Noke kafad'a tayi, ya sake cewa

"Pleaseeeeee...."

"Ba kai ne ba."

"Are you still angry?" Yace yana matsawa inda take.

"Ok I'm sorry, bazan kara ba, wani abu ne ya faru which bana son ma tunashi, ba wai na manta dake bane, kina makale a nan."

Ya nuna saitin heart din sa.

"Kin yafe min?"

"Umm."

"Oya give me a hug." Ya sake bud'e hannayen sa wider than before. Kunya take ji, ta k'asa motsawa tayi abinda yake so, ganin da gaske ba zata yi ba yasa kawai ya saka hannu ya jawo ta, yayi hugging nata kam kam yana shakar daddadan kamshin turaren ta da ya kusa tafiya dashi zuwa wani bigire na daban.

"Knock knock..." Akayi knocking, janye wa tayi kad'an shi kuma ya amsa sallamar da Adnan yayi

"Sorry to interrupt, Safwan ne yake neman ka,it seems like yana ta kiranka baka daga ba, ya damu sosai yanzu ma ya shiga gida, rashin ganin motar ka da beyi ba yasa be kawo kana nan ba, ni kuma ban fad'a masa kana nan din ba tunda bansan dalilin ka ba."

"Nasan zai neme ni dama, shiyasa ma na ajiye motar a chan bayan layin."

"Ok idan ka samu time ka kirashi." Ya juya ya fita.

"Wani abu ne ya faru?" Ta tambaye shi tana kallon sa. Daga kafadar sa yayi

"Babu komai fa."

"Amma yake neman ka?"

"Eh tun jiya bamu hadu ba, kinsan dole ya neme ni."

"Owk." Tace tana jan bakin ta, tayi shiru dan taga alamar ba zai ce komai akai ba.
   Mood din sa ne taga ya chanja, yayi shiru alamar tunani yake yi. Tunanin kuwa yake yadda zai yi avoiding Safwan idan har zai zo wajen Amrah kafin ya tafi, baya so su hadu yafi so ya fita daga rayuwar tasu kamar yadda Mah-Mah tayi masa umarni, amma besan ta ina zai fara ba. Mikewa yayi ya kama hannun ta ya rike cikin nasa.

"Zan dawo da daddare, take care of your self, for me." Sai yayi kissing bayan hannun nata yayi murmushi

"Wannan abun yayi miki kyau a hannu."
Kallon hannun nata tayi, tayi murmushi kad'an, dayan hannun sa ya zura a aljihu ya ciro kud'i ya saka mata acikin tafin hannun ta

"Ki yi amfani dashi idan kina bukata,you are now my responsibility bana so ki tambayi su Umma komai kinji?"

"Nagode Allah ya kara budi."

"Amin ya Allah, amin."Abinda Ke Cikin Zuciya

Page 29

*Barka da sallah*

***Knocking ake sosai ta mike da k'yar cikin yanayin bacci me karfi ta nufi kofar, tun bayan tafiyar sa baccin ya dauke ta anan saman kujera, gajiya ce sosai a tattare da ita ga wani azababben ciwon kai dake damun ta plus gajiyar da oga kwata kwatan ya had'a mata jiya. Da k'yar ta isa gate din cikin dashashiyar murya tace

"Waye?"

"Ai nazata ko bin sa kikayi,wannan bugun da nayi tayi..."

Da sauri ta zare lock din tana jin dadi, tayi saurin rungume ta kankam.

"Bacci ya dauke ni wallahi."

"Baccin gajiya ko?" Afrah tace tana kashe mata ido daya, duka ta kai mata sannan ta mika hannu

"Kinji da gulmar ki, bani jakar kayan naki dallah."

"Yawwa kamar kin san na gaji."

Ta fad'a tana sakar mata jakar, ciki suka juya da nufin shiga suna cigaba da hirar su kamar ba jiya jiya suka rabo ba, suna haura balcony din aka buga kofar gidan da karfin gaske, kallon juna sukayi a tare

"Kina da baki ne?"

"A'ah..."

Sake bugawa akayi, ta ajiye jakar ta nufin kofar tana tambayar waye, ba'a yi magana ba sai cigaba da bugun da akayi, tayi saurin isa ta sake cire lock din, ta dan bud'e kofar kad'an ta yadda ba za'a ganta daga waje ba tace

"Waye?"

"Bako ne, maigidan yananan?"

"Baya nan."

"Toh... Ko dai ba address din bane, ko ba gidan Dr Sultan bane?" Yace cike da tantama

"Nan ne, amma baya nan."

"Toh Toh... Madallah, idan ya dawo kyace masa nazo."

"Toh wa za'a ce masa?"

Shiru be amsa ba, ta sake tambaya shiru, sai ta dan leka kanta wajen kad'an sai taga ashe ma ya tafi, rufe kofar tayi tana komawa ciki dan tuni Afrah ta shige.

"Wai waye naji kin dad'e."

"Wani ne, bansan waye ba wai Sultan yazo nema."

"Ko sune na gansu a kofar gida suka bini da kallo, har ma na dan ji na tsargu domin yanayin su be min ba, kamar marasa gaskia wallahi."

"Toh..."

"Idan kunyi waya ki tambaye shi ko akwai bakon da yake expecting, dan yadda k'asar nan tamu ta lalace, gashi kiwon mutum ake ba dabba ba."

"Malama karki tsorata ni,babu abinda zai faru, tsarguwa kawai kikayi dallah."

"Toh Allah yasa." Tace tana dariya ganin yadda Amrah ta nuna alamun tsoro, sai ta kauda maganar suka shiga wata amma k'asan zuciyar ta sai taji ta kasa aminta da mutanen da ta gani dazun, addu'a tayi kawai ba tare da ta sake daga maganar ba dan yadda Amrah ta nuna ta tsorata karta kara tsoratata.
Ganin azahar ta tawo yasa suka shiga kitchen a tare, suka girka noodles suka ci a kitchen din sannan suka dawo falon suka cigaba da kallo suna hira, lokaci lokaci Amrah na kiran wayar Sultan amma switch off, da ta ga haka sai ta dinga tura masa message duk sanda ta kira tasan idan ya kunna dole zai gane. Addu'a ta bishi da shi suka cigaba da hira da Afrah Amma k'asan zuciyar ta babu dadi tana tunani da fatan Allah ya tsare shi ya kaishi lafiya ya kuma bashi nasara a abinda ya saka a gaba.

***Daga nesa ya hange shi tsaye ya na d'an dube dube, ya tsaida me napep din ya biya shi sannan ya fito yana gyara zaman jakar dake rataye a kafadar sa ya nufi inda yake. Tun kafin ya karasa ya ganshi yayi saurin tawowa suka hadu a hanya. Kallon tsanaki Sultan yayi masa kad'an sannan ya mika masa hannu suka gaisa yana karantar yanayin sa cike da nazarin abubuwa da dama a tattare dashi, na farko yanayin shigar sa sai kuma yanayin da fuskar sa take ciki wadda ta sake saka sultan din cikin wani yanayi na tunani.

"Muje ko?" Yace bayan ya dan kalli agogo samfurin apple dake hannun sa.  Har ya fara tafiya sai ya tsaya

"Musa ko?

"Eh Musa ranka ya dad'e."

Jinjina kansa yayi kad'an

"Kai ne jagoran tafiyar bani ba, kai ya kamata ka shiga gaba."

"Haka ne, bismillah." Yace yana nufar wata bakar mota, dakatawa Sultan yayi da bin sa yace

"Bana tunanin zuwan mu a motar gida zai taimakawa abinda zamu je yi."

"Tabbas ba zai taimaka ba, dama iya kar mararrabar zamu idan yaso sai mu karasa daga chan."

Jinjina kai yayi kad'an sannan ya bi shi ya shiga motar,shi kuma yaja suka tafi.

Tafiya ce me matukar nisa wanda tun sultan na duba dukkannin bayanan daya tatatara har ya hakura ya dangana da kallon hanyar yana sake lafewa a jikin motar da babu abinda yake tashi a cikin ta sai karar na'urar sanyaya waje.

La'asar sakaliya suka isa inda musan yace, ya gangara gefen wata yar karamar hanya zuwa wani madaidaicin gida wanda ya zama kamar shi kad'ai ne a wajen. Shi dai Sultan be ce komai ba yana bin komai da ido.

"Yallaabai ina dan zuwa dan Allah."

Da ka ya amsa masa ya fita da sauri ya shiga gidan, jim kad'an suka fito da wasu mutane su uku, suna magana har suka karaso wajen motar, ganin haka yasa SULTAN bude kofar ya fito.

"Barka da zuwa." Suka fad'a a tare har suna dan russunawa.

"Ranka ya dad'e wannan shine zamu bashi ajiyar motar, wadannan kuma su zasu dauke mu har Masarautar Saji Idan Allah ya yarda."

"Allah ya kaimu lafiya." Kawai yace

Babura ne guda biyu, Sultan ya hau daya Musa ma ya hau daya suka dauki hanyar Masarautar Saji.
Gabannin magriba suka isa, sai dai yadda harabar Babbar Masarautar ke cike da wasu irin manyan fitulu masu hasken gaske yasa wajen ya zama kamar rana, daga chan gefe suka sauke su, sannan suka nufi wata hanya daban suka bar Sultan da Musa a tsaye.
Da ido Sultan ya shiga bin Babbar Masarautar wadda take da fadin kasa sosai ga wasu manya manyan bishiyu masu kyau da suka kara kawata wajen, girman ta ya kai girman wani garin, gidaje ne daga kowanne bangare nata wanda ya kasance an musu ado da irin adon da ake ma gidan sarauta. Tun kafin su karaso Masarautar ya lura da yadda tsari da kyau da Allah ya bawa garin na Saji,babban birni ne cikin manyan birane wanda kai tsaye zaka kirashi da lamba daya indai akan kyau da tsari ne.
Hankalin sa ne ya dawo kan masu tsaron Masarautar wanda a kalla sun ta samma su talatin kowannen su babu annuri a fuskar sa, zagaye suke kawai kamar mayunwatan zaki masu farautar neman abinda zasu ce, amma idan akayi la'akari da dalilin da yasa aka sake bazasu a wajen zaka san cewa dole ne su jajirce dan kuskure daya zasuyi komai ya lalace.

"Karka yi magana duk abinda zasu ce kayi shiru, mun riga mun tsara komai."
Chapter 64 · 0% Book details