← Book details Abinda Ke Cikin Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 75 OF 108

Sashe 75

Abinda Ke Cikin Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

***Tana zaune ta hada kanta da guiwa, tayi kuka har ta gaji, gashi babu wanda ya zo inda take tunda suka kawo ta suka ajiye ta, a tunanin ta irin kidnappers din nan ne, tunda yanzu k'asar gaba d'aya ta zama haka, amma rashin zuwan su da kuma yanayin yadda suka dauko tan yasa ta tsorata da su din su waye?
   Kallon kafarta tayi da suka saka wata igiya suka daure mata, bayan ta gwada guduwa tayi, ta cigaba da kukan da take rerawa, a rayuwar ta bata san wata wahala ba, bata da hayaniya ko yawan magana shiyasa yanzu duk ta shiga wani irin yanayi. Batayi zato ba ko tsammani taji an turo kofar dakin, ta dago idon ta ya sauka akan sa, babban mutum ne cikin shigar manyan kaya, ya tsaya daga kofa yana kare mata kallo

"Yarinya ce ma ai karama." Yace yana kallon na bayan sa

"Eh oga."

"Owk a cire mata igiyar nan, na fad'a muku karku mata komai fa, amma me yasa?"

"Guduwa taso yi ne oga."

"Kuna me zata gudu? Idan ma ta gudu ai kuna nan a kofar ba matsawa zakuyi ba ko? Sai ku hanata."

"Toh oga."

"Akwai abinci na tawo mata dashi a mota, a turo wani ya dauka, kici abinci kinji? Babu abinda zamuyi miki mijinki kawai muke bukata anan, ya kawo min kayana na bashi ke, Idan kika ga be zo ba toh tabbas baki da muhimmanci a wajenshi."

***
***A wani irin yanayi yake zagayawa ransa a matukar baci tunda ya samu labarin zaman Yarima Bilal sarki, tabbas wani yana masa zagon k'asa,kuma tabbas a cikin yaran sa ne da ido ya shiga binsu dukkan su sun sunkuyar da kan nasu k'asa,

"Waye munafukin dake fitar da maganganun mu?"

Duk sukayi tsuru tsuru, babu wanda yayi magana,

"Babu Wanda zai magana ko?"

Shiru

"Ku tashi ku bani waje, zan yi bincike duk wanda na gano sai na masa wulakancin da bai yi zato ba."

Sum sum sum duk suka mike suka fita. Lallai Yarima ya shammace shi, be taba kawo shi a rai ba balle yayi tunanin zai kawo masa matsala, amma tunda be samu zoben nan ba, mulkin nasa na dan lokaci ne kawai, shi zai yi kokarin samun sa sannan yayi amfani da karfin sa wajen samun cikar burin sa.

***Tsayawa yayi a harabar wajen yana waige-waigen neman abinda yake son ganin, kasancewar unguwar babu mutane ya saka wajen ya zama tsit babu haske ko kadan, ledojin da ya zo dasu ya daga ya kalla sannan ya nufi gidan yana fatan samun Ammi a ciki dan shi sam be yarda da Mutumin nan ba, kawai yasan boye ta yayi yana wasa da hankalin su, bayan kuma yaji maganar da suke ranar da wadannan mutanen ya sake tabbatar da hakan, shiyasa yayi ta bibiyar su har ya gane inda suke,ya kuma ga zuwan Madakin yau shiyasa yayi alkawarin shiga gidan yau ko ta halin kaka.
Kansa tsaye ya nufi cikin gidan, ya sa hannu ya kwankwasa kofar yana matsawa baya. Wata murya kakkaura tace

"Waye?"

Shiru yaki magana yana ji yana kokarin zare sakatar,

"Waye kai?"

"Alhaji ne ya aiko ni." Ya d'aga masa ledojin hannun sa.

"Meye wannan din?"

"Abinci ne."

"Alhajin yace ka kawo mana?" Ya karba ya bud'e daya, shinkafa ce da kaza, ya hadiyi yawu ya shiga kwalawa wanda suke tare kira.

"Mudi, mudi! Zo kaga abin arziki."

"Menene?”

"Duba, Alhaji yace akawo mana."

"Kai kai, kutrun ubanchan, yo kodai Ya hajj ya samu abinda yake so ne? Wannan dabge haka."

"Toh waya sani, muje ciki a ga yadda za'a kasafta ta." Sukayi ciki sun ma manta da shi da yake tsaye, da sauri yabi bayan su, ya makale jikin wani gini, su kuma suka shiga ciki suka dira akan abincin kamar tsofaffin mayunwata. Sai da suka gama cinye abincin tas suka tsotse kashin sannan maganin ya soma aiki a kansu, a hankali suka dinga bajewa suna kwanciya bacci me nauyi na dauke kowannen su.
  Da sauri ya fito, ya bud'e dakin ya tsaya yana kallon yarinyar dake zaune ta dora kanta a saman guiwar ta,

"Ke kad'ai ce anan?" Da sauri ta dago

"Kwantar da hankalin ki, babu me zuwa yanzu, ke kad'ai ce anan?"

Daga mishi kai tayi tana hawaye

"Babu kuma wata matar da kika tarar anan?"

"Babu."

Dafa kansa yayi kamar zai ihu, ina Ammi take toh?

"Shikenan, muje." Yayi gaba d sauri, ta biyo bayan sa sukayi hanyar fita da mugun sauri. Wata mota ce ta shigo layin suka yi saurin makalewa a jikin wani kango, ya dube ta cikin tashin hankali yace

"Number wa kika sani a yan gidanku?."

***A daidai wajen da suka hadu jiya yau ma suka hadu, Sultan na shiga motar ya kwanta dan zai iya cewa jiya sam be runtsa ba, yana tunani, ga wani irin son ganin Amrah dake nukurkusar zuciyar sa, yasan ta da saurin kuka, yasan kuma tayi babu iyaka watàkila ma hawayen nata ya kafe. Gefe daya kuma zuciyar sa na muradin sake ganin su, yayi musu albishir ya kuma cika musu alkawarin da yayi musu, amma baya so su dawo kasar har sai komai ya kammala zai je da kansa ya dauko su, ya dawowa da Masarautar da mutanen ta abinda suka rasa tsawon lokaci.
  Kai tsaye gidan Madaki ya kwatantawa Safwan suka dau hanya, kafin su karasa aka kira sallar magriba, suka tsaya a masallaci suka fara yin sallar sannan suka karasa. Fitowa sukayi a tare, Safwan ya rufe motar suka nufi gidan suna tafiya a jere. Kwankwasa gate din Sultan yayi Maigadin ya leko, yana ganin shine yayi saurin bud'e kofar yana washe baki.

"Yallaabai barka da zuwa."

"Barka dai Baba."

"Alhaji na ciki?"

"Yana nan, magana za'a yi masa? Dan nasa kamar ransa a bace yake."

"A ah ai yasan ma da zuwan mu, kawai ka jagorance mu zuwa wajen sa."

"Ah toh ai shikenan ma, bismillah."

Suka bi bayan sa, sun kusa isa Safwan yaja hannun sultan ya tsaida shi

"Hold your temper man, ka bar komai a hannu na."

"Zan iya gaggaya masa magana ne a yadda nake jin raina."

"Yaushe sultan ya zama me zafin zuciya?"

"Ba zaka gane ba, wannan mutumin devil ne."

"Duk da haka, Amrah na tare dashi so sai mun bi komai a sannu."

"Shikenan, I ll adjust."

"Better."

"Bismillah, Alhaji kayi baki."

"Su waye?" Yace ransa a bace

"Mune." Sultan ya amsa suna kutsa kai cikin falon. Tashi yayi tsaye

"Dama nasan zaka zo, nasan zaka zo ai mace ba wasa bace,ina aike na?"

Daga masa hannu Sultan yayi, ya kalli zoben da sauri, ya shiga matsawo yana son gasgata idon sa, da gaske complete zoben ne ko kuwa dai wani zoben ne daban? Yasan tun a wanchan lokacin aka rasa barin zoben amma aina sultan ya samu har ya hade shi sannan har ya saka shi a hannun sa.

"Ba sai ka matso ba, kamar yadda ka gani, zoben ne cikakke, sai dai yanzu abu biyu ne zasu saka ni baka zoben nan, na farko alkawarin da kayi min na had'a ni da iyayena idan na dauko maka zoben, sai na biyu matata, ba muyi haka da kai ba, mesa zaka daukar min mata?"

"Saboda ka turo yaron da na aike ku tare, wanda ya tabbatar min ba zaka bani zoben nan ba tunda ba haka muka tsara ba, shiyasa ni kuma nayi maka abinda nasan zaka kawo min zoben cikin ruwan sanyi,amma ya akayi haka? Ya akayi ka samu zoben dukkan sa?"

"Wannan ba damuwar ka bace, ina so ka cika alkawarin ka na farko, maganar iyaye na, sai kuma matata da nake son gani yanzu, idan har ka cika wadannan sharudan zan cire maka zoben na baka."

"Kana so ka kure ni ne Sultan?"

Shiru yayi yana kauda kansa gefe,

"Ina zuwa." Yace ya tashi ya shiga wata kofa, be dad'e ba ya dawo sai dai tare yake da wani tsohon mutum da kuma wata dattijuwar mata, kallo daya zakayi musu ka tabbatar da yadda talauci yayi musu katutu, wahala sosai ta nuna a jikin su barin ma tsohon da har wani malkwadewa yake saboda rama.

"Gasu nan, wadannan din sune iyayenka, kar kuma ka tambaye ni ta yaya, zaka samu amsar komai a bakin su."

"Yaro Sultan ashe kana raye?" Suka had'a baki wajen fad'a, ba wai yanayin su ne ya hana Sultan din magana ba, sai yadda Madaki yake so ya raina masa yawo, be san yasan abubuwan da ba lallai shi din ya sani ba,Amma duk da haka ba zai yi saurin mika wuya ba, zai bishi a yadda yaso din. Tashi yayi yana masa kallon cikin ido, kallon da ya dan firgita Madakin amma ya dake, idanun Maimartaba sak yake gani a cikin kwayar idon Sultan din, amma sai ya dake ya jira yaji me zai ce

"Ka cika alkawari daya, saura daya."

"Ka fara bani zoben ni kuma zan baka matar ka..."

"Ai ba haka mukayi ba..."

Karar wayar sa ta katse shi, ya ciro ta yana kallon number, kafin ya daga ya saka ta a kunnensa

"Na turo maka da address yanzu yanzu kazo ina tare da matar ka, kazo kafin su farga saboda haka kayi sauri dan Allah."

Da sauri yace

"Gani nan."

Sai ya juya wajen Madaki

"Zan dawo, abu ya taso min urgent amma zan dawo."

Ya juya da sauri Safwan yana take masa baya.

Waya Madaki ya dauka yana jan gashin gefen bakin sa yace

"Yaro be san wuta ba..."

"Hello! Gashi nan ya fito,ku bishi ku kawo min zoben hannun sa, idan yayi gardama ku harbe shi!"

**Assalamu alaikum Lovelies 😂 ina neman ahuwa bisa rashin jina a yadda ya kamata, hakan ya samo asali ne sakamakon wani baban uzuri daya rike ni, amma in Sha Allah na dawo. Masu cewa sunyi fushi akan littafin nan kuyi hakuri, kurciya Billy da Xoxo sukayi min na bace bàt a yanar gizo😂😂😂 Da na dawo kuma sai ya zama duk sanda na dauki wayar zan yi typing sai bacci ya kwamushe ni. Ahuwa bayin kaina bane😂😂😂 Lolz😎😎😎😎😎😂

Gashi nan readmore 10ne cif na biya Bashi😂⛹️⛹️⛹️⛹️⛹️⛹️

ZAFAFA BIYAR
NA KUDI NE:::

Duka BIYAR 5 zaku samesu akan garabasar naira 700 kacal,
Chapter 75 · 0% Book details