Sashe 12
Abinda Ke Cikin Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Karka damu, take your time ina kyautata zaton zata yi accepting dinka, babu macen da zata ce dan uwana be mata ba, ba'a haifeta ba kaf duniyar nan."
"Wait... Yaushe nace maka maganar mace ne?"
"Karka manta nasan ka fiye da yadda kasan kanka, bayan haka ka ma tuna kana magana ne da heart doctor."
"Umm, sannu heart doc."
"Yawwa, shawara daya kawai kabi komai a sannu, karka zurfafa da yawa kazo ka fad'a ciki, kasan condition dinka dai."
"Yes boss."
Dariya sukayi gaba daya sannan sukayi sallama. Ajiyar zuciya Sultan ya sauke bayan sun gama wayar yana addu'ar sa komai ya tafi wa Safwan,be san yadda zata kasance ba idan har abinda ya ke tsoro ya faru.
Suna zaune suna shan coffee me zafi shi da Adnan ta fito, kanta a kasa ta wuce kitchen, da kallo ya bita har ta shige shi, sannan ya maida kansa kan abinda yake yi yana ayyana yadda take koman ta a nutse ba baragada, idan kaji hirar ta me tsayi toh waya take da Hajiya, Afrah ko magana suke da Umma, ya lura ko Adnan din ba wata hira suke ba sannan yana lura da ita, bata da wajen zama da ya wuce kitchen, tun anan ya gane yadda take da son girke girke, hakan yayi masa dadi dan yana d'aya daga cikin abinda yake so wajen mace kenan, iya sarrafa kalolin abinci. Tashi yayi ya dauki mugs din da suka gama,ya nufi Kitchen din, tana tsaye a gaban sink tana wanke abu a cikin dan basket da be lura da mene ba, ya shiga da sallama. Chak ta tsaya da abinda take tana jan numfashi kadan kadan, takun tafiyar sa taji abayan ta, tayi kamar ta zura da gudu sai ta dake tayi kokarin tattaro nutsuwar ta kafin ya gane yadda yake samun tasiri akan ta a duk sanda taji shi kusa da ita, a dan gefen ta kan wani babban table ya ajiye mugs din, turaren sa na hugo boss ya bige hancin ta, ta bude su a hankali ta shak'e shi sosai yabi ya shiga kowanne sashe na hancin ta.
"Sannu da aiki." Yace yana komawa jikin fridge sannan yayi folding hannun sa yana karewa kitchen din kallo.
"Uhmm." Kawai tace sannan ta juya ta saka kitchen gloves a hannun ta, ta sauke tukunyar da ke saman wuta. Shiru babu wanda yayi magana a cikin su, shi be fita ba, ya kuma ki barin ta, ta sake tayi aikinta, kadan kadan take jan tsaki tana jin haushin tsayawar da yayi dan har ga Allah ya shiga rayuwar ta. Dan satar kallon sa tayi taga ashe ma shi danna wayar sa yake hankalin sa kwance, yana kuma murmushi, murmushin da zata iya cewa babu abinda tafi so bayan idanun sa kamar su.
"Yadai?" Yace yana dariya, fuska tayi ta cigaba da abinda take pretending as if ma ba ta san yana wajen ba. Matsowa yayi kusa da ita sosai yace a hankali yace
"Please a zuba min abinda aka yi mana,ko so ake kamshi ya kashe mutum da ransa ne a gidan nan."
"Toh." Tace ta sauri tana yin wajen plates din har ga Allah ya takura wa rayuwar ta, ta dauko ta zuba masa da yawa ta mika masa, taki bari su hada ido.
"Yanzu fa muka gama shan wanchan abun ya ma sunan sa? Um? Um tuna min dan Allah."
"Coffee."
"Yawwa shi, toh aina zan zuba wannan kuma, sai dai idan tare zamu ci"
Da sauri ta kalle shi, sai ya kanne mata ido daya, tayi saurin kasa da kanta tana murmushi
"Idan zamu ci tare kinga ya ishe mu."
"Bari a rage toh." Ta dauko wani plate din da zuba masa wani daban daidai daidai, tana gama wa ta mika masa sai ya makale kafadar sa yaki karba
"Menene?" Tace tana kallon abincin sannan ta kalle shi
"Yayi min kadan wannan, daga cewa ki rage sai ki kwashe fiye da rabi."
"Toh ni bansan ya kake so ba, gashi ya zuba da kanka toh." Tace tana ajiye masa akan wajen zata juya, da sauri ya sha gabanta, ya marairace fuska,
"Dan Allah karki tafi,ki karasa aikin ki, zan koma gefe na tsaya,nidai kawai ki yi ta min magana karki yi shiru kinji, zan ci wannan din yayi min.*
"Toh ai na gama, shiryawa zan na tafi school."
"Zan je nima." Yace da sauri
"Amrah..." Umma dake nufo kitchen din ta kira sunan ta, da sauri tayi gaba, shi kuma ya daga murfin freezer din pretending kamar wani abu zai dauka, kafin Umman ta shigo Amrah ta fita sun hadu a hanya, magana tayi mata ta koma falon itama kuma Amrah ta wuce dakin su.
Dauke da abincin ya fito da bottle din ruwa me sanyi ya zauna, ya fara ci Adnan ya dauko spoon suka ci tare, kunnen sa kamar zai cire saboda yadda abincin yayi dadi sosai, yana ci yana lumshe ido be san sanda ya fara yiwa umma santi ba, tayi ta mishi dariya Adnan na tayata, sai da suka cinye abincin tas sannan suka tashi kowa yayi nasa waje.
***Wayar ta tayi haske, ta dauka tana duba sakon da ya shigo, karo na shida kenan da irin wannan sakon na shigowa wayar ta, babu suna sai number waya, daga Nigeria ne ta sani, amma bata san waye ba, ta kuma kasa tunanin kowa dan babu wanda ta sani da zai mata hakan, sake maimaita karantawa tayi,sannan ta ajiye ta shiga wata sabgar.
***Zufa ce ta rufe shi, numfashin sa na kaiwa da komowa a tsakanin kirjin sa, yau ne karo na wajen biyar da yake irin wannan mafarkin, me cike da firgitarwa. Duk sanda ya farka bayan hakan yakan samu kansa da shiga tsananin firgice me yawan gaske, wanda har yake hanashi aiwatar da komai. Yana ji aka d'an taba kofar dakin nasa, ya mike da kyar ya nufi kofar ya bude, tana tsaye ta harde hannunta a kirjin ta, idanun ta sun fad'a ciki, kallo daya yayi mata yasan tayi kuka, kukan da ba ka iya boyeshi a cikin idanun ka, gefe ya matsa mata ta gifta shi ta shiga ciki tana dan kallon yanayin dakin, a gaban gadon ta tsaya, ta yaye bargon da yake hargitse akai ta ninkeshi ta maida shi wajen ajiyar sa, sannan ta hau gyara dakin. Toilet ya wuce ta ya shiga, yayi alwala ya fito, a shinfid'e ya tarar da abun sallah, gefe jallabiya da yar karamar counter, wai gawa yayi ya kalle ta na d'an sakanni sannan ya tada sallar.
Bayan ta gama gyara ko'ina ta yi hanyar fita daga dakin, ya dakatar da ita.
"Ina bukatar hutu, kwakwalwata a chunkushe take da tunani kala kala, bazan samu fitowa ba yau."
Kallon sa tayi sai tasa kai ta fice ba tare da tace komai ba. Da jikin gadon ya jingina, ya rufe idon sa yana tariyo abubuwan da suka faru, yaushe Maryam zata daina ganin laifin sa, yaushe ne zata gane abinda ya aikata shine kawai mafita, mafita a gare su baki daya.
Zuciyar sa ce ta dauke shi zuwa lokaci chan baya, a sanda komai yake tafiyar musu daidai basu da wata matsala a duniya, sai kuma ta sake daukar shi zuwa wata ranar. Ranar da ba zasu iya mantawa da ita ba, ranar da ta zame musu ta musamman a cikin rayuwar su, ana tsuga ruwan sama ne, me karfin gaske, gari yayi duhu sosai, ko ina yayi shiru kamar babu sauran me numfashi a doron kasa. A daidai lokacin ne...
Kalmashe kafarsa yayi yana murza goshin sa da yan-yatsun sa, yana jin kamar a lokacin komai yake faruwa, kaddara na da suna daya, sai dai tana da fuskoki masu yawan gaske, wanda baki ba zai iya lissafa su ba. Breakfast din sa ya kalla, dake shirye a saman dan madaidacin teburin dake cikin dakin nasa, ya dauke kansa yana komawa saman kan tafkeken gadon da ta gama gyarawa yanzu ya mike kafafuwansa,sannan ya jingina da fuskar gadon yana cigaba da bitar rayuwa da yadda take zuwar ma mutum da fuskoki mabanbanta. Kira ne ya shigo wayar sa, sai a lokacin ya tuna har ita wayar ya kamata ya kashe dan da gaske yau hutawa yake so yayi, ya jawo ta da nufin kashe kiran sai dai ganin me kiran yasa shi fasawa, shine mutum na karshe da zai k'i amsa wayar sa ko a wanne hali yake. Ya jima yana magana dashi, sannan ya kashe gami da danne power off ya ajiye ta anan saman bedside drawer.
Be fito ba sai chan yamma, lokacin yaji karfin jikin sa, duk da haka yana bukatar ganin likita, domin yadda yake jin jikin sa da k'yar idan ba jinin sa ne ya hau ba, yana tsoron ciwon da zai kwantar dashi a yanayin da yake ciki yanzu, ga girma ya fara kamashi ga abubuwa da yawa da yake fatan su daidaita. Yana ji lokaci ya kusa da zai fuskanci kowa da komai, ya bayyana wa duniya kansa da ya jima yana boyewa.
Sai dai abu daya ne yake dakatar dashi da cikar burin sa, ta ina zai fara neman ta? Bayan be san inda ta nufa ba tun wannan ranar. Bashi da madogara sai Allah, dan haka addua ce kad'ai zata iya dawo masa da farin cikin da ya rasa,ko yace da suka rasa baki daya.
Yau ma kamar sauran ranakun, hawayen bakin ciki ne ke fita daga idanun ta, tana kaichon irin rayuwa da son zuciya tana jin dama za'a dawo da baya da ta goge duk wani shafi na cikin rayuwar ta ta baya. Rufe idon ta tayi tana hasko komai kamar a lokacin ne yake faruwa