← Book details Abinda Ke Cikin Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 84 OF 108

Sashe 84

Abinda Ke Cikin Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da sauri Umma ta karasa ficewa kunya na kamata saboda itace a gaban Hajiyan kuma ta tabbata Sultan din ma yaji me Hajiyan tace. Girgixa kai kawai yayi yana kunshe dariyar sa.
Murmushi suka samar ma juna a tare, ya dora hannun sa a saman kanta daidai wajen bandage din, ta matse fuska kad'an

"Yana miki ciwo ne?"

"Ba sosai ba."

"Ok bari suzo sai su sake dubawa, yaushe akayi dressing wajen?"

"Dazu nurse din tazo tayi."

"Ok ya jikin naki?"

"Da sauki."

"Sosai?"

"Sosai."

"Sannu kinji?"

"Uhum."

"Shine kika koreni jiya ko? Wa na kama?" Yayi maganar yana matsawa kusa da ita sosai

"Ni? yaushe? Ni Allah ban kore ka ba."

"Kin manta?"

"Uhum... Ni.. Ni ban kore ka ba Allah."

"Uhum... Kinsan me? Nayi missing naki sosai, sosai, sosai, kuma nayi dana sanin tafiya na barki, bansan zan yi missing naki me yawan haka ba sai bayan da naje, naji me ma yasa na tafi."

"Uhum..." Tace tana juua idon ta,

"Kamar da gaske." Ta dora

"Allah da gaske nake."

Ya rik'e hannun ta ya dora a saman chest din sa

"My heart beats for you 💜💚💘" kinji?

Zame hannun ta tayi, tace

"Banji komai ba."

"Shikenan, ni bari naji naki, zan gane how much kikayi missing dina."

Da sauri ta ja baya ganin yana kokarin dora hannun sa a saman chest dinta

"Umm..mmm... Ba sai kaji ba dan Allah."

"Mesa? Ki tsaya naji mana idan ba tsoro ba."

"Dan Allah ,kaga fa bani da lafiya." Ta karashe tana karyar da muryar ta

"Matsoraci dai baya zama gwani."

"Ummm, kaci abinci?" Ta chanja maganar

Kallon ta yayi sosai, kallon cikin ido har sai da ta rufe idon nata saboda yadda kwarjinin sa ya cika wajen, daf da ita ya sake matsawa, ya rada mata wata magana a cikin kunnenta, maganar da ta saka ta kusan bude kasar wajen ta rufe kanta saboda kunyar sa, bata san Sultan ya kai haka ba, ita duk kallon da take masa dah na mara magana da son hayaniya bata taba tunanin zai iya irin wannan zantuttukan ba, kasa dagowa tayi tayi dana sanin yi masa tambayar, bata yi tunanin zai chanja maganar zuwa wani abu daban ba,tana jin sa yana mata dariya taki kulashi. Sai kuma taji ya daina dariyar lokacin da aka budo kofar

"Ya Sultan." Taji muryar mace na masa magana, dagowa tayi, ganin wadda bata zata ba a dakin yasa ta yin kicin kicin da fuska,

"Bansan kana nan ba, Mah-Mah ce tace nazo na duba ta." Tayi maganar tana kallon fuskar amrahn

"Ok gata nan, babyy za'a dubaki."

"Ya jikin?"

"Alhamdulillah." Ta amsa a kajarce

"Allah ya kara sauki." Sai ta juya kan Sultan

"Ya Sultan kamar fa ya Safwan ya tashi, naji ma ance kai yake nema."

Da sauri ya mike yayi fice ba tare da yace komai ba. Murmushin mugunta Umaimah tayi, dama chan tayi niyyar korar sa shiyasa tayi masa haka, tun da taga bata ganshi ba a chan tasan yana nan.
Wajen da Sulthan din ya tashi ta koma ta zauna tana karewa amrahn kallo, kallo irin na raini.

"Sorry na raba masoya ko? Opss I'm so sorry."

Yadda tayi maganar kawai ya isa ka gane inda ta dosa, shiru Amrah tayi zuciyar ta na mata zafi, tasan Umaiman da gayya tayi abinda tayi saboda tasan waye Safwan a wajenshi. Shigowar Afrah ya saka Umaiman mikewa tana cigaba da taunar chewing gum tace

"Allah ya kara sauki Amarya, bari naje wajen angon naki akwai muhimmiyar maganar da yace zamuyi."

Wani irin tukuki ne ya dinga tasowa Amrah,tana kallo ta juya ta fice fuskar ta cike da farin ciki,wani kuka Amrah taji ya taho mata, da sauri Afrah ta dakatar da ita

"Wallahi idan kika ce Zakiyi mata kuka zaki sha wuya, irin wadanda yan iskan sai ka nuna musu kai ma dan kanka ne wallahi sannan zaku daidai ta,tazo har inda kike, ta saka ki kuka bayan shi Wanda take magana akai ba wai saurayinki bane, mijin ki for that matter, lallai."

"Tama raina ki ne, da tun farko ma zata shigo miki haka kai tsaye bayan taga kowa a waje, ni wallahi dan bana wajen ta shigo ne da sai na hanata wallahi."

Cigaba da sababi Afrah tayi bata tanka mata ba, sai kawai ta kwanta tana jin zafin abinda Umaiman tayi mata.

***Sultan na zuwa ya tarar har lokacin Safwan na baccin sa, be farka ba kuma, sai a sannan ya gane dalilin da yasa Umaiman tayi masa haka, so take ya bar dakin dan tasan ba zai iya kuma sake tsattsallake su Umma ya sake komawa ba. Dole ya hakura zuwa lokacin da kafa zata dauke a barta ita da Afrah kawai shine zai sake.
Tunawa da yayi da yace zai sake kiran Babah yasa ya kira a lokacin, Gimbiyar ce da kanta ma ta daga,suka gaisa suka dan yi magana ta nuna farin cikin ta akan zuwan da ya ce zai yi, sannan ta bawa Babah yace ya turo da ACC details dinsa sune zasu dauki nauyin zuwan nasa, da yaso yayi musu ganin ran baban ya baci ya saka ya sauko ya hakura yace zai turo. Da haka ya samu ya lallaba su sukayi sallama. Yana kashe kiran wani kiran ya shigo, ya daga

"Ka shigar da Hukuma cikin abinda ya had'a mu, toh ka sani idan bincike yayi bincike zai nuna kowa ,ciki harda wadanda baka taba tunani ba."

"Me yasa ka kirani?."

"So nake mu hadu, zaka ga abinda zai baka matukar mamaki, idan har ka yarda zaka zo,kai ka dai kuma, zan turo address din in da zaka sameni, karka sha wahalar kiran Yan sanda domin ni Alhaji Safiyanu Madaki ba zan kamu ba."

"Ni kad'ai nake da matsala da kai,saboda haka karka sake saka wani nawa a ciki, zanzo ka turo da address din."

"Ok karfe uku na yamma daidai."

Bin wayar Sultan yayi bayan ya katse, kenan Madaki yana kasar ko dawowa yayi? Ko kuma kuskure aka samu yan sandan suka ce ya bar kasar ko kuma ya saye yan sandan, cikin biyu dole ayi daya, yafi zargin saye sun yayi, wannan kasar tamu shiyasa ba zamu cigaba ba ko k'ad'an.

"Zanzo na sameka Madaki, ni kad'ai kamar yadda ka bukata.!"

**Not Edited©® Hafsat Rano

Page 43

*MIMICOS COLLECTION*

Gidan kayan kawa da kayan alatun kece raini, ina masu neman inda zasu gwangwaje su gyagije da jakunkunan yan gayu, laces, atamfa takalma, kayan yara, jewelries designer perfumes masu dan karen kamshi da sauran su?, kuyi maza ku karzayo *MIMICOS COLLECTION* Muna nan a Naibawa titin danhassan ,layin sp baba muhd ko a neme mu a number wayar mu
07035209753. Muna maraba da masu siyan daidai ko sari. Kuma muna aikawa a kunne lungu da sako na fadin kasar nan. Karku bari a baku labari. MIMICOS COLLECTION gidan yan gayu, kayan yan gayu masu tafiya daidai da zamani.

***Murmushi kawai Sulthan yayi, bashi da abin fad'a, idan ma akwai toh be san me zai ce ba, sai kawai ya matsa gaban inda Aminatu take, yace

"Ya sunan matar da ake tunanin itace ta karbi yaran?"

"Safiyya." Maman Yara ta amsa duk da ba da ita yake ba, juyowa yayi yace

"Ina tunanin itace." Yace yana zama

"Ka samu labarin ta ne?"

"Eh...."

Zumbur Aminatu ta tashi

"Aina? Tana ina dan Allah?"

Sosai ta bashi tausayi

"Bansan takamaimai inda take ba, amma na hadu da Muhammad."

"Muhammad?"

"Eh yace min sunan Ammin su Safiya, sannan kuma tana hannun Madaki, sannan kuma yace min shi din yan biyu ne amma shi kad'ai ne a wajen Ammin, bata kuma fad'a masa ina dayan yake ba."

"Dan Allah ina yake? Ina so na ganshi dan Allah!"

"Kiyi hakuri, zaki ganshi, ki kwantar da hankalin ki."

Komawa tayi ta zauna, suka cigaba da magana da Maman Yara yana kara samun information din da duk yake bukata. Sai da ya tabbatar ya kwantar mata da hankali sannan yayi musu sallama ya tafi.

***Duk da be san abinda zai tarar ba idan ya je amma ya saka a ransa zai je din, shi kad'ai kuma dan baya son sake saka kowa a cikin matsalar sa. Sai da kusan ukun tayi sannan ya samu sakon sa da address din, yayi murmushi me kyau

"Lokaci yayi." Ya furta yana mikewa daga inda yake zaune, ya riga ya shirye komai, ya kuma tabbatar da ba za'a samu matsala ba. Gida ya fara zuwa, yayi wanka ya gyara fuskar sa da sajen sa, yayi fes dashi kamar wanda zai je zance, ya saka manya kaya farar shadda da Babbar Riga da akayi wa aikin bakin zare, ya saka hula da takalmin sa sau ciki tare da bakar safa, sosai ya fito kallo daya zaka yi masa kaji ya burgeka. Motar sa ya dauka yayi mata key kai tsaye ya nufi address din.

A waje ya tsaya, ya tura masa da sakon ya iso, ya ciro wani farin glass ya saka a fuskarsa, ya bud'e kofar ya zuro kafafuwan sa yana jiran sa. Yana zaune wani matashin yaro yazo yayi masa magana. Kashe motar yayi, ya kulle ya bi shi suka nufi wani katon gida. Bangarori ne da yawa a gidan, sannan akwai mutane masu yawa a ciki, wanda da yawan su hadiman gidan ne sai kuma wasu maza manya da su kuma suke gadin ciki da wajen gidan. Wuce su sukayi, suka dangana da wata babbar kofa, inda yaron ya saka hannu ya bud'e sannan ya ja baya kad'an

"Yana ciki."

"Ok." Yace ya kutsa kansa ciki, Madaki da yake tsaye yana jiran isowarshi ya sha jinin jikin sa, ganin irin shigar da Sulthan din yayi wadda ta fito da shi sosai ya cika, kwarjinin sa da yake hana Madakin masa wasu abubuwan ya sake bayyana, be taba ganin shi da manyan kaya haka ba, shiyasa ya ji wani abu ya taba shi, wanda ke zaune tare da Madakin ne ya amsa sallamar Sultan din, be jira an bashi wajen zama ba yayi wa kansa wajen zaman, ya hard'e kafarsa ya shiga girgiza ta tana lilo.

"Gani? Me yasa kake nema na?"
Chapter 84 · 0% Book details