Sashe 5
Abinda Ke Cikin Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
***Graduation gowns ce maroon colour sanye jikin su, fuskar su kadai zaka kalla ka shaida tsanar farin cikin da suke ciki, taro ne akeyi a cikin tsari babu hayaniya wajen. Gefe Adnan ya samu ya fara Skype shi da Safwan yana nuna masa duk abinda ke faruwa a wajen, tun farkon fara gift ga students din da suka chanchanta, daga Amrah har Afran suna ciki, haka aka kirasu aka basu kyaututtukan su gwanin sha'awa.
Kwance yake a daki ya rufe ko ina yana more kallon komai kamar yana wajen, turo kofar Sultan yayi cikin shirn fita, ya tsaya yana kallon yadda yake kallon waya yana murmushi, zuwa yayi da niyyar lekawa Safwan ya tashi yana boye wayar yana dariya
"Kai matsalar ka kenan, Idan ana shirin suprising naka sai ka bata plan din, Allah yaso baka ga komai ba."
Yace yana sake boye wayar, tabe baki Sultan yayi ya dauki jakar sa ya rataya.
"Idan tayi wari zamuji ai, na lura da take taken ka yaro."
"Karka damu, nayi alkawarin kai ne na farko da zan fara sanarwa komai da zarar an dace, kai dai ka taya ni da Addua ina neman abu me muhimmanci a rayuwata, infact idan na same shi ma zuciya ta zata samu sauki da kaso hamsin cikin dari, kaga kai ma saukin ka ne ba kayi ta fama dani ba bayan kai ma kana da life ahead of you."
Yanda yayi sounding a karshe kana ji kasan abun na taba shi, sai ya ajiye jakar ya matso ya dafa kafadar sa kafin yace
"I promise to give you my maximum support, karka manta lafiyar ka itace priority dina, zan yi duk abinda zanyi wajen ganin ka cika burin zuciyar ka."
"I trust you." Yace yana murmushi
Musabiha sukayi ya fice shi kuma yayi dialing number Adnan dan ya kashe kiran tun da suka fara magana da Sultan, jin be daga ba sai kawai ya ajiye wayar ya fita daga dakin.
****Toh masu karatu, me kuke tunanin zai faru? Akwai chakwakiya ko nace chakwakiyoyi a gaba.
Abin da ke Cikin Zuciya littafin kudi ne, daya daga cikin jerin littafan Zafafa Biyar, domin mallakar naki sai ki tuntubi wadannan lambobin
0903 234 5899
Or
09033181070
Not edited
Rano 👌💞
[3/4, 11:35 PM] Maman Maryam: *_Abinda Ke Cikin Zuciya_*
©®*_Hafsat Rano_*
Free page (3)
***
*_SMM OPANAGE_*
Juya aikakkiyar wasikar take a hannun ta, zuciyar ta a jagule kamar ta dora hannu aka ta saka ihu ko taji saukin zafin da take mata, sai da tayi mata duban tsanaki sannan ta ninke ta, ta hada da sauran kayayyakin da take tarawa, ta ajiye su a ma'ajiyar su, sannan ta fito wajen yaran dake jiran ta.
Ranar a kasalance tayi komai, daga karshe ma sai ta shige ciki da niyyar ta kwanta ta huta ko ta samu zuciya da gangar jikinta su samu nutsuwar da suka rasa.
***
Da sauri Safwan ya bi bayan shi, har ya kai gate zai fita ya tsaida shi da d'an gudun sa
"Lafiya kuwa?" Yace sanda ya fuskance shi, sai ya ga kamar idon sa yayi ja
"Babu komai kaina ne ya dan yi dum, sai kuma na tuna sakon Daddy, kasan fa time na kurewa bamu ma gama hada kan kayan ba balle mu kai."
"Shine duk ka damu haka? Chill guy muje mu karasa shan furar chan sai mu karasa hade kayan gobe da wuri sai mu kai musu."
Girgiza masa kai yayi
"Karka damu, bari na je gida idan ka gama sai ka sameni."
"Shikenan tunda ka dage, bari naje sai na shigo.".
Sai ya juya shi kuma ya fita yana jin wani irin emptiness da besan na menene ba, ya san dai kawai ba normal yake jin sa ba. Daki kawai ya wuce direct ya kwanta rigingine ya daga kansa sama yana tunanin yadda rayuwar sa take, idan ya tuna shi din maraya ne, bashi da kowa da zai nuña a matsayin jinin sa, sai yaji duk komai ya kwance masa, amma idan ya tuna gatan da kuma Allah yayi masa ya tsamo shi ya inganta masa rayuwa sai yaji duk tunanin ya kau, baya fatan ganin iyayen sa domin Mah-Mah da Daddy sun cike dukkan gurbin da iyayen nasa suka bar masa shi open, sannan ga dan uwa amini da zai iya cewa bashi da kamar sa duk fadin duniyar nan, soyayyar da yake masa daga Allah ce, Allah ne ya hada su cikin Ikon Sa, ya kuma saka kauna a tsakanin su,kauna me tsanani da ta zama wani jigo na rayuwar sa.
Bashi da wata matsala da su, haka kuma iyaye ya dauke su, ba kuma ya fatan Allah ya kawo ranar da zai butulce musu. Daya daga cikin abinda yasa ya zabi bangaren lafiya, kuma bangaren zuciya saboda ya riga yasan Safwan ne rayuwar iyayensu, Shima kuma haka, duk lokacin da ciwon sa ya tashi su kan rasa sukuni, har sai sun ga ya dawo daidai sannan komai yake komawa daidai.
Safwan mutum ne shi be faran faran da jama'a da son duk wani da zai rabe shi, fuskar sa a sake take da wuya ka ga bacin rai a fuskar sa while Sultan bashi da fara'ah sai dai fuskar tasa a sake take ba irin a daure nan ba. Yana da kazar kazar shiyasa ma Daddy yafi dora shi akan duk wani abu kafin yace Safwan sau daya ya kira Sultan sau goma.
Yana kwance yana sakawa da kwancewa aka kira sallah, sai ya mike ya dauro alwala ya wuce masallaci. A chan suka ya tarar da su adnan bayan sun idar sai suka samu waje a nan bakin layin sukayi zaman su suna hira irin wadda maza samari ke yi galibi, hirar siyasa, kwallon kafa sai kuma hirarrakin yan mata. Safwan da Adnan sune akan gaba wajen kawo tactics din saye zuciyar mace, inda sultan sai dai yayi musu dariya kawai idan abin dariya ne. Chan Adnan ya zungure shi ya bata rai yace
"Kaifa wallahi dan rainin class ne, kana yin kamar baka san komai ba, kamar wani uztaz."
"Toh da menene?" Ya amsa masa yana dariya
Wani abokin su Mubarak yace
"Gaskiya ne ya sheik, irin ku ne soyayya ke wa kamun kazar kuku, kuzo kuna ciwo kamar ba zakuyi rai ba."
"Allah ya kiyaye wallahi.". Safwan yace yana mikewa
"Sultan yafi karfin yace yana so a wulakanta shi wallahi, gaye iya gaye ga nutsuwa ga aji, ai sai na zaba na darje kafin na yarda ya kula koma wace."
"Kai ne ma zaka aurar dashi kenan."
Adnan yace yana buga tsaki
"Kusan haka ne ko bro?"
"Hakan ne ma." Ya amsa yana murmushi
Sai sauran suka sa ihu da shewa irin ta samari masu jini a jika.