← Book details Abinda Ke Cikin Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 71 OF 108

Sashe 71

Abinda Ke Cikin Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

***Gaba d'aya hankalin su ya tashi, duk wanda Afrah ta kira a daren nan sun samu labarin sace Amrah, hankalin Safwan yayi mugun tashi dashi da Adnan da Abba suke yawon zuwa police station da wasu wuraren da ya kamata, idan ka gansu zaka dauka basu da lafiya ne gaba dayan su yadda duk suka chanja halitta suka koma wata kala ga wahala ga rana ga yunwa sosai. Babu wani da yake da sukunin saka wani abu a cikin su babu ma me tunanin nan, su umma da sauran yan uwa na gidan ana jimama, Afrah kuwa zazzabi ne ya rufe ta sosai sai da aka yi mata allura sannan aka samu tayi bacci.
Har la'asar ana jiran kiran wayar su kamar yadda akayi tunani amma babu wanda ya kira, hakan ya sake daga hankalin kowa musamman Ummah da Afrah dan lokacin ta farka.
Zuwan Hajiya ya sake hargitsa wajen, kuka take tana kiran sunan Sultan tana cewa ya cuce su, duk hankalin mutane ya koma kanta wadanda ma basu san komai akai ba suka bada hankalin su akanta, sosai take kukan tana cigaba da cewa

"Ni dama chan ban yarda da yaron nan ba, Yaron da aka ce ba'a san asalin sa ba, babu abinda ba zai iya aikatawa ba, ban yarda wasu ne suka dauke Amrah ba, sai dai shi da kansa ya sace ta."

"Haba Hajiya, haba Hajiya ya za'a yi mutum ya sace matar sa, dan Allah ki daina fad'a." Wata Kanwar Abba tace tana kokarin saka Hajiyar tayi shiru, amma maimakon haka sai ta sake tunzura ta

"Idan bashi ya sace ta ba yana Ina? Wanne irin abu ne zai taso masa haka ya tafi ya bar yarinya da kai ta kwana daya, kuma duk kiran duniya an kira wayar sa a kashe, sai ki gayan gidan uban da yaje ko shima sace shin akayi?"

"Kiyi hakuri dan Allah, ko ma menenn Allah zai bayyanata cikin koshin lafiya, zargi yanzu duk bashi gane Addua ce kawai mafita." Wata yar uwar Umma da takaici ya kama tayi maganar tana jin kamar ta tashi ta bar wajen. Ganin babbace yasa Hajiya yin shiru bata sake cewa komai ba. Mutanen da suka shisshigo jaje da yan uwa suka shiga tattaunawa akan abinda hajiyar tace kowa na tofa albarkacin bakin sa.

***Shiru dare ya tsala sosai baka jin karar komai sai daga chan nesa,idon Sultan biyu yana jiran shigowar Yarima kamar yadda yace masa dazu, yana yi yana duba time din wayar sa da ya saka ta a flight mood, yana so ya kira Amrah amma baya so ya tashe ta daga bacci, ba kuma yaso su fara waya Yarima ya shigo. Jin an taba kofar yasa ya daga kansa, kananan kaya ne a jikin sa da pcap daya sauko da ita zuwa saman fuskar sa. Girgixa kai Sultan yayi da Allah ya shirya a ransa da tabbas Yarima ba mutumin arziki bane yadda yake abubuwan sa. Ba zai so wani abu ya hado su dashi ba dan yasan mutane irin su nada hatsari musamman mutum da yake mu'amula da kayan maye.
Be jira abinda Yariman zai ce ba ya mike

"Ka shirya ko?"

"Eh."

"Ok muje." Yace yayi gaba, Sultan yabi bayan sa, suka fito a tare, da sauri bayin dake kofar wajen suka taso, yarima ya daga musu hannu duk suka koma da sauri.
Tafiya kad'an sukayi suka isa, kamar yadda yake a jikin zanen Masarautar da yake tare dashi haka yake a zahiri, da ido ya Kalli tsari da kyaun wajen kamar a wata k'asa, katon gini ne na gaske wanda ya kasance bangaren Maimartaban, shuke shuke ne masu matukar kyau da suka sake kawata wajen sai wasu fitulu masu haske mara karfi kala kala suka sake kawata wajen sosai. Wajen yafi kowanne bangare yawan masu tsaro dan ciki suke dam suna kaiwa da komowa, yana cikin tsarin Maimartaba Sarki Bello Moddibo Saji, yawan masu tsaron sa Wanda yake jin kamar yawan nasu shine garkuwar da, kamar babu abinda zai same shi tunda suna zagaye dashi, sai dai be sani ba, babu abinda suka isa suyi masa akan abinda ya Allah ya kaddaro masa zai faru dashi.
Basu yi mamakin ganin Yarima a wannan lokacin ba, bayan tafiyar sa kenan daga wajen mahaifin nasa, amma babu wanda yake da Ikon hanashi ko tambayar shi abinda ya sake dawo dashi din, hakan kamar ganganci ne wanda zai iya jawo ma mutum rasa ransa ma baki d'aya. Be amsa gaisuwar da suke ta faman jera masa ba, wadda take shiga ta fita ta dayan kunnen sa saboda rashin muhimmanci ta gareshi har suka dangana da babban falon Sarki Bello Moddibo Saji. Tsayawa yayi ba tare da ya shiga ba, ya kalli Sultan dake bayan sa yayi wani kayataccen murmushi, wanda ya bar Sultan a tunani kala kala, be yi magana ba ya kutsa kai cikin falon Sultan na biye dashi. Babu ko d'igon haske a ciki, sai da ya nemi ma kunnin hasken dakin ya kunna haske ya mamaye ko ina. Babu kowa a falon sai karar na'urar sanyaya daki da ta cika wajen sosai wani irin sanyi me ratsa bargo na huda su. Tsum Sultan ya tsaya yana sake karewa falon kallo yana son ganin wani abu da zai sake bashi haske akan abinda yake shirin yi. Sai dai babu komai kasancewar babu wasu shirgi ko tarkace a falon komai neat a muhallin sa.
Da hannu Yarima ya nuna masa wata kofa bayan ya matso kusa dashi sosai,

"Wannan itace kofar da zata kaika turakar Maimartaba, kuma anan zaka samu abinda kake nema, kayi sauri bamu da lokacin batawa zan jira ka anan."

Daga masa kai Sultan yayi yana sake damke barin zoben dake hannun sa sosai ya nufi kofar bakin sa dauke da addu'a.

ZAFAFA BIYAR
NA KUDI NE:::

Duka BIYAR 5 zaku samesu akan garabasar naira 700 kacal,

Guda hudu 4 Kuma 500,

Guda uku 3 Kuma 450,

Guda biyu 2 Kuma 400,

Guda daya akan 300.

Ma'ana
Each one is 300
2 is 400
3 is 450
4 is 500
5 is 700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO- *0812652655*
ACCOUNT NAME- *HAFSAT LAWAN GAMBO*
BANK NAME: *ACCESS BANK*

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

*+234 903 234 5899*

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

*09033181070*

Karku Bari ayi Babu ku domin wannnan salon na daban ne
SABUWAR SHEKARA
SABON SALO

TEAM#ZAFAFABIYAR🔥 ©Hafsat Rano

Page 34
Chapter 71 · 0% Book details