← Book details Abinda Ke Cikin Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 108

Sashe 9

Abinda Ke Cikin Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

***Da safe Abba ya kirasu ya sanar dasu yadda tafiyar ta zama, sai dai kafin lokacin Umma ta chanja shawara zata zauna din kawai bayan tayi tunanin yadda zata barta ita kadai har tsawon wasu watanni, Amrah har da guntun hawayen ta, amma jin cewa idan su Afrah suka dawo suma zasu je sai ta hakura ta saki ranta, abinda zatayi yanzun burin ta ne, ta jima tana so da kauna, haka Allah ya tsara shiyasa ma hakan ta faru.
   Sun shirya tsaf ranar da zasu tafi, tayi kokarin kwantar da hankalin ta sukayi musu rakiya har airport ita da Adnan da Umma, sai da suka ga tashin su sannan suka koma gida.
   Ranta a jagule ta wuce dakinsu ta kwanta kawai tana jin gidan yayi mata fadi sosai, sun saba komai tare suke yi da Afrah, suyi fad'a su shirya basu taba nisa da juna ba tun bayan sun dawo kasar. Ranar bata ci abincin dare ba,haka tayi kwanciyar ta a daki har bacci ya dauke ta wanda bata tashi ba sai da gari yayi haske, duk lokacin da bata sallah takan makara sosai ta rasa dalili ko dan bata kwanciya da niyyar tashi da wurin ne shiyasa, haka ta fito lokacin su Umma sun gama breakfast suna zaune suna kallo a tv ita da Ya Adnan, joining dinsu tayi bayan ta dauko breakfast din ta, ta dawo tsakiyar falon, tana ci suna kallo had'e da hira har zuwa lokacin da ta tashi ta koma daki ta dauki wayar ta,ta kwanta tana game cikin kwanciyar hankali.
Suna ta sa rai da kiran su Abba, sai dare kiran ya shigo, tana daki umma ta shigo da wayar a kunnenta suna magana, sai ta mika mata ta zauna gefen gadon. Da Abba suka fara gaisawa sannan Hajiya ta karba, sai Afrah, sun dan yi hira da Afran tana bata labarin tafiyar tasu, sai da umma ta karbe wayar ta sannan suka hakura, rufo mata kofar tayi suna cigaba da magana da Abban.WhatsApp ta hau suka cigaba da maganar su, sai gashi hira ta mika kamar ma suna tare da juna.
Sati d'aya tsakani ta fara zuwa makarantar, da farko ta kasa gane yadda tsarin yake, sai a hankali ta fuskanci komai sai gashi ta ware tana ganewa sosai, ba kadan take jin dadin makarantar ta da yadda ake gudanar da komai cikin tsari da kwarewa.
Da safe kafin ta tafi sai ta gwada abun da aka koya musu, sannan ta dauka ta kai wa malamar tasu ta gani, ba karamin mamaki malamar take ba ganin yadda take da kwazon dauke komai da anyi musun, bata san cewa duk abinda ya zama kana da passion akai ba, zaka bada dukkan nutsuwar ka wajen koyan sa.

***
Da tsananin murna Safwan ya shigo gidan jin labarin saukar su, a tunanin sa harda gimbiyar zuciyar sa tun da Adnan be fad'a masa yadda tafiyar ta sauya ba, turus yayi ganin Afrah ita kadai sai Umaima dake gefe tana faman danne danne a waya fuskar ta a chunkushe ta juya tana kallon gefe kamar bata yi maraba da zuwan na Afrah ba.
Da murna ta tare shi

"Ya Safwan."

"Wa nake gani kamar yar afiriri, Innalillahi gaskia an kwana biyu, Masha Allah."

Rufe fuskar ta tayi da tafin hannun ta, tasa dariya tunowa da sunan da yake fad'a mata da tana karama.

"Ya Safwan baka chanja ba, kana nan da tsokanar ka wallahi."

"Kema nasan baki chanja ba ai, surutun yana nan."

Sai ya dan rage murya kadan yace

"Ina dunkum din, na ganki ke kadai."

Fashewa tayi da dariya sosai shima yana tayata

"Wai dama baka manta da sunan nan ba, tab ai kuwa nasan Amrah yanzu da zata ji sunan nan sai ta kusan sumewa saboda haushi."

"Ina kika barta?" Ya tambaya cike da zak'uwa

"Ai nida Abba kadai muka zo, ita da umma sai mun koma."

"Shit!" Yace yana jin duk farin cikin sa na barin sa, Umaima da ta maido hankalin ta wajen hirar su ta dan tab'e baki ta cigaba da bin wakar ta, dan ita har ga Allah yarinyar batayi mata ba, dadcin d'ad'awar ta daji daga in da tazo, sai taji wani abu me kama da tsanar ta ya shiga zuciyar ta nan take, ya bata mata happy mood din ta baki daya.
Ba'a son ransa ba, ya zauna suka cigaba da hirar ganin Mah-Mah bata nan kuma Umaimah bata da niyyar kulata, sai dai kaso tamanin na hankalin sa yana chan wajen tunanin yadda ya sa rai da ganin ta a yau, sai dai kash.

Kansa a kasa bakin sa dauke da sallama ya shigo falon, da sauri Umaima ta tashi kamar dama zaman jiran sa take, gaishe shi tayi ya amsa kirjin sa na wani irin bugu, da Afrah ya fara yin tozali sai da zuciyar sa tayi wani irin tsalle, tunanin sa zai ganta zaune kusa da Afran, be shirya ganin ta a lokacin ba, sai dai a take yaji babu abinda yake son ganin kamar ita. Da kyar ya ja kafar sa a kasalance ya karasa shigowa falon ba tare da ya lura da Umaimah dake faman washe mishi 32teeth dinta ba, iyakar shak'a ta shak'a musamman yadda taga gaba daya daga Sultan din har Safwan din sun bada attention dinsu a kan bakuwar, a zuciye ta wuce ciki tana sake jin wata irin tsanar ta.

Da Mah-Mah ta dawo ta tarar da Afrah murna sosai tayi, ta rasa inda zata sata saboda farin ciki, har zuwa dare ana abu daya, hira sosai tsakanin su har basu san lokaci ya ja haka ba babu wanda ya nemi abinci, ba kuma su bi takan Umaima dake chan daki tana kunci ba.
A tare suka shigo da Abban da Daddy, suka zauna a falon, Sultan da Safwan kowa na kokarin gaida Abba a kunyace kowa da tasa manufar a zuciyar sa, ya amsa musu a sake had'e da yan tambayoyi, tare suka ci abinci da iyayen nasu sannan suka tafi suka basu waje don su samu damar tattaunawa.
Zancen tafiyar Sultan Daddy yayi Abba inda ya roki alfarmar zai xauna a tare dasu har ya kammala, Abba be ji dadin alfarmar da yace ba, dan shima ai Adnan anan din ya zauna bayan sun tafi kuma har ya karasa karatun sa Abban be taba biyan ko sisi ba. Sai wajen tara Abban ya tafi bayan Daddy yasa su Sultan sun maida shi gidan Hajiya sannan suka dawo gida.
Daga nan gidan Afrah ta fara yawon zagaya dangi, Safwan ne ya dauki nauyin yawon nata duk inda zata bata da matsala. Zaman ta da Umaimah be dame ta ba, bata ma san me ne ne game da ita a zuciyar ta ba, a tunanin ta ma haka yanayin ta yake shiyasa ta debe ta, ta watsar ta cigaba da harkokin ta kamar tana gaban Ummanta. Dama chan ita bata da duhun kai balle yanxu da suka waye suka goge da rayuwa, hutu da gayu ta kowanne bangare, ga uwa uba kyawun da Allah ya basu.
Chapter 9 · 0% Book details