← Book details Abinda Ke Cikin Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 57 OF 108

Sashe 57

Abinda Ke Cikin Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Wata lowclass girl ce, sanda muka zo da Abba itama tazo hutu gidan Mah-Mah, kamar ko niece din Mah-Mah ce a yadda naji, ta fiya jin kanta shiyasa ni sam bata min ba, sannan naga alamu da take taken ta, ya sultan take so."

"Ok yayi." Ta amsa a dakile, gaba d'aya sai taji hoton ya fita kanta, ta kasa dauke ido daga kansu har sai da ta ga SULTAN din ya shiga mota ya tafi, ita kuma ta juya zuwa cikin gidan, fuskar ta dauke da murmushin da ta barwa Amrah tunanin murmushiin menene?

"Karma ki bata lokacin ki akan irin wannan tsohuwar."

"Ba zaki gane ba Afrah, irin su zasu iya yin komai domin samun abinda suke so."

"Ya Sultan baya son ta, ba kuma zai taba son ta ba nasan, kalle ta fa kamar wata masara babu kyawun gani."

"Ke kike ganin haka."

"Comman, karki bata ranar ki da kanki da tunanin abinda ba me yiwu wa bane."

"Naji...Mu koma ciki Toh."

Ciki suka shiga still Afrah na cigaba da son ganin tayi convincing dinta ta kuma nuna mata dole sai ta yi shining idon ta, idan ta tsaya sanyi da salo salo sai dai taji anayi ba ita, dan yanzu mata akan namiji babu abinda ba zasu iya ba to win him over.

***Hannun sa daya na saman steering, daya kuma yana rik'e da wayar sa wadda yake kokarin kiran numbers din da yazo ya tarar da misscalls bayan barin wayar ta da yayi a mota ta kwana, jiya da ya dawo gidan be shiga da komai ba, abincin da ya tsaya yayi order ya dauka kawai shima kuma chacchakala kawai yayi ya rufe shi yayi kwanciyar sa. Bin kiran ya fara yi daya bayan daya wanda yawanci na abokan su ne sai yan asibiti. Yana gamawa dasu ya nemo number Amrah zai kira ta kiran mai gadin gidan Alhaji Safiyanu Madaki ya shigo, be daga ba sai da ta gama ringing sanñan yabi kiran.

"Hello..."

"Nine Sultan, na kikkiraka da layi na baka daga ba, idan ka samu lokaci kazo gida akwai maganar da nake so na fad'a maka."

"Ina wani abu me muhimmanci ne, maganar ba zata yiwu a waya ba?"

"Eh gaskiya."

"Shikenan zanzo."

Ya katse kiran be jira amsar sa ba, ya rasa me yasa kawai yake jin haushin Alhaji Safiyanu, ko dan tunanin da yake akansa na son Amfani dashi domin cimma manufar sa ne yasa hakan? Ko kuma dai akwai dalili? Ba zai dai taba bari yayi amfani dashi ba for his selfish interest.
  Jujjuya wayar take a hannun ta, zuciyar ta duk babu dadi, a zaton ta zai dawo bayan tafiyar tasa jiya, ko da bazata tare ba ya kamata ya dawo ya ganta kafin ya kwanta, kuma ta kirashi sau biyu be daga ba be kuma biyo kiran ba, duk sai taji ta damu da hakan, har sai da damuwar ta nuna a cikin yanayin ta.
    Wayar ce tayi kara, har ta dan tsorata dan bata yi zato ba, ta kalli sunan me kiran tana sake bata fuskar ta alamun tayi fushi kamar yana gabanta. Sai da ta kusa tsinkewa sannan ta d'aga muryar ta a chunkushe tace

"Hello?"

"Assalamu alaikum."

"Wa alaikasalam, goodmorning."

"Morning my wife, kin tashi lafiya?"

"Lafiya Lou."

"Ya naji ki haka haka? Are you ok?"

"Umm."

"Toh waye ya taba min ke? Umm? Tell me, adunanu ne ko afiruwa?"

"You, you, you."

"Ni kuma? Me nayi ni kuma? Bawan Allah."

"Baka dawo jiya ba, na kira no answer, kuma baka kira back ba sai yanzu."

"God! I'm so sorry kinji,wallahi jiyan nan ba zaki gane ba, anyway gani a kofar gida, kizo dakin Adnan sai muyi magana."

"Ok." Tace tayi hanging kiran ta tashi da sauri, sabuwar atamfar dake jikin ta wadda akayi ma dinkin simple gown ta sake dubawa, tayi mata kyau sosai ta karbi kalar fatar ta, dan lip balm ta shafa ta sake fesa turare ta fito,a falo ta ga Amrah da sauran bakin da basu tafi ba taja hannun ta suka fito.

"Rakani dan Allah."

"Ina kuma?"

"Ya Sultan ne yake dakin ya Adnan."

Da sauri Afrah ta kwace hannun ta tana ja baya.

"Wallahi ba zan je ba, an gaya miki wai ana raka mata ne wajen mijin ta, kiji ki da wani zance."

"Haba Afrah, dan Allah ki rakani."

"Kai you most be kidding me, yasin ban zuwa, zan iya kaiki bakin boarder dai, daga nan sai na yo kwana na barki ki karasa."

"Bakin boarder kuma?"

"Eh mana, iya kata bakin dakin."

"Muje naji." Tace tana sake jan hannun ta. Suna zuwa kofar dakin Afrah ta warce hannun ta, ta yi tafiyar ta tana mata dariyar mugunta.

A hankali ta tura kofar ta shiga kamar barauniya, ya na zauna a k'asan carpet ya kalmashe kafar sa dake sanye cikin bakar safa, hannun sa rik'e da cup yana shan tea suna magana da Adnan.

"Bafa za'a maida min daki dandalin masoya ba ehe."

Saurin sauke kanta k'asa tayi kunyar ya Adnan na sake kamata

"Idan mutum yaji haushi yayi zuciya shima."

"Haka kace? Karka manta yanzu matsayin yayanka nake."

"Au auw, haka ne fa, sorry babban yaya, na tuba."

"Yafi dai." Yace yana karasa sanya takalmin sa, yazo yayi hanyar fita yana cigaba da mita.

Ajiye cup din yayi ya mike tsaye sannan ya bud'e hannayen sa.

"Come please."

Noke kafad'a tayi, ya sake cewa

"Pleaseeeeee...."

"Ba kai ne ba."

"Are you still angry?" Yace yana matsawa inda take.

"Ok I'm sorry, bazan kara ba, wani abu ne ya faru which bana son ma tunashi, ba wai na manta dake bane, kina makale a nan."

Ya nuna saitin heart din sa.

"Kin yafe min?"

"Umm."

"Oya give me a hug." Ya sake bud'e hannayen sa wider than before. Kunya take ji, ta k'asa motsawa tayi abinda yake so, ganin da gaske ba zata yi ba yasa kawai ya saka hannu ya jawo ta, yayi hugging nata kam kam yana shakar daddadan kamshin turaren ta da ya kusa tafiya dashi zuwa wani bigire na daban.

"Knock knock..." Akayi knocking, janye wa tayi kad'an shi kuma ya amsa sallamar da Adnan yayi

"Sorry to interrupt, Safwan ne yake neman ka,it seems like yana ta kiranka baka daga ba, ya damu sosai yanzu ma ya shiga gida, rashin ganin motar ka da beyi ba yasa be kawo kana nan ba, ni kuma ban fad'a masa kana nan din ba tunda bansan dalilin ka ba."

"Nasan zai neme ni dama, shiyasa ma na ajiye motar a chan bayan layin."

"Ok idan ka samu time ka kirashi." Ya juya ya fita.

"Wani abu ne ya faru?" Ta tambaye shi tana kallon sa. Daga kafadar sa yayi

"Babu komai fa."

"Amma yake neman ka?"

"Eh tun jiya bamu hadu ba, kinsan dole ya neme ni."

"Owk." Tace tana jan bakin ta, tayi shiru dan taga alamar ba zai ce komai akai ba.
   Mood din sa ne taga ya chanja, yayi shiru alamar tunani yake yi. Tunanin kuwa yake yadda zai yi avoiding Safwan idan har zai zo wajen Amrah kafin ya tafi, baya so su hadu yafi so ya fita daga rayuwar tasu kamar yadda Mah-Mah tayi masa umarni, amma besan ta ina zai fara ba. Mikewa yayi ya kama hannun ta ya rike cikin nasa.

"Zan dawo da daddare, take care of your self, for me." Sai yayi kissing bayan hannun nata yayi murmushi

"Wannan abun yayi miki kyau a hannu."
Kallon hannun nata tayi, tayi murmushi kad'an, dayan hannun sa ya zura a aljihu ya ciro kud'i ya saka mata acikin tafin hannun ta

"Ki yi amfani dashi idan kina bukata,you are now my responsibility bana so ki tambayi su Umma komai kinji?"

"Nagode Allah ya kara budi."

"Amin ya Allah, amin."
[4/12, 11:04 PM] Maman Maryam: Hafsat Rano

28

***Ciro wayar sa yayi ya kira, ganin an bud'e kofar gate din yasa ya fito ya rufe kofar ya nufi cikin gidan, gaisawa sukayi da Baba Maigadi ya wuce kai tsaye inda suka hadu ranar, kafin ya karasa isa sukayi kichibis dashi,

"Laaa."

"Kana lafiya Ameer?"

"Lafiya Lou Wallahi."

"Masha Allah, Alhaji na ciki?"

"Eh bismillah." Yayi gaba ya bishi a baya.
Su biyu ne a falon suna magana k'asa kasa, suna ganin shi suka mike tsaye, wanda suke taren ya kafe shi da ido babu ko kiftawa

"Shigo mana Sultan."

"Barka da rana."

"Barka dai, kana lafiya?"

"Lafiya Lou."

Sai suka zauna a kusan tare

"Me za'a kawo maka?"

"Babu komai."

"Ok, abinda yasa na kiraka,akan tafiyar nan ce, sun riga sun san da zuwan ka, saboda haka zamu chanja rana, ko alamis ko asabar, sannan tafiyar ka kai kad'ai ba zata yiwu ba, duba da baka da sani akan hanyoyin shiga Masarautar, saboda haka ga Musa, shine wanda zai jagorance ka a tafiyar."

"Akwai wani abu bayan nan?"

"Akwai, kurkuku me lamba 108 akwai mutane biyu masu matukar muhimmanci a tafiyar nan taka, ka tabbata ka samu ganin su,kayi magana dasu ko da na wssu mintuna ne."

"Sai me?"

"Shikenan ina tunanin, sauran abubuwan idan kaje chan zaka gane."

"Alhamis zamu tafi, ka zama cikin shiri."

"Na barku lafiya."

Yana fita suna shigowa, mace ne da namiji, kallon su yayi çikin wani yanayi, sai kuma ya wuce su da sauri ya fice ganin yadda suma suke kallon sa.
Chapter 57 · 0% Book details