← Book details Abinda Ke Cikin Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 108

Sashe 29

Abinda Ke Cikin Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Abinda ya faru shine, mahaifiyar Umaimah ce ta kira Mah-Mah tayi mata maganar a matsayin wanda ita Umaiman take so, bayan sun ajiye wayar ne Mah-Mah tayi ma Afrah magana a WhatsApp dan duk tunanin ta Sultan da Afran sun daidai ta kansu dan a yadda taga suna yi kafin ya tabi tayi ta adduar hasashen ta ya zama gaskiya, shiyasa ma da Safwan yazo da maganar Amrah taji dadi tayi kuma yiwa sultan fatan samun Afran, maganar Umaimah tasa ta son jin wani abu daga bangaren Afran kafin ta tuntubi shi sultan din, idan tasan akwai wani abu tsakanin su toh zata san yadda tayi ta bawa Anty Aminan hakuri ba tare da Sultan din ma yasan abinda ke faruwa ba balle yaga rashin kunyar Umaiman da mahaifiyar ta. Sai dai kuma abinda taji wanda yasha banban da abinda take tunani yasa zuciyar ta, ta kad'a tsoron abinda zai samu Safwan dinta ya shige ta, ta tabbata idan ya samu labarin Sultan ke soyayya da Amrah daya kwallafa rai zai iya hakura, hakan kuma na nufin me? Tayi ta faman sakawa da kwancewa akan abinda ya kamata tayi, kafin komai ya kwabe musu, sai dai abu daya da yayi mata zafi ainun shine tasan tabbas Sultan yasan da maganar Safwan din tunda tasan babu yadda Safwan zai yi wani decision a rayuwar sa ba tare da sanin Sultan din ba, ta kuma tuna da kanta ta tambayi Safwan din bayan an sallamoshi daga asibiti, ta kuma bashi shawarar ya sanar da Sultan , kenan ya san komai amma yayi gaban kansa ya manta da komai yake kokarin kafa kansa,bayan yasan halin da Safwan din zai shiga idan komai ya bayyana? Wannan tunanin ne ya kara bata mata rai ainun, a haka Hajiya Umma wata yar uwar ta da suke kusan sa'anni a dangi ta shigo ta sameta, ta manta ma shaf sunyi waya tace zatazo, sai da ta ganta ta tuna, ta kuma kasa rike abinda yake cikin zuciyar ta, sosai Hajiya Umman ta shiga ingizata, da kalaman da suka sata aikata abinda zai iya zamar mata dana sani anan gaba.
Farko dai shiryawa tayi a gurguje suka fita a motar Hajiyan Umman da drivern ta, zasu fita daga layin Safwan ya shigo, ya tsaya suka gaisa da Hajiya Umman sannan Mah-Mah tace masa yanzu zasu je su dawo. Adawo lafiya yayi musu ya wuce cikin layin su kuma suka fita.
Kwatance Mah-Mah ta dinga yiwa drivern har suka isa kofar gidan, ya faka daga chan gefen gidan, Hajiya Umma ta kalli Maman tace

"Ta sanki ne?"

"Eh ta sanni." Ta amsa tana jin wani shashi na zuciyar ta na yin rauni, tana jin kamar abinda zata suke shirin yi be kamata ba,sai dai da ta tuna saboda Safwan zatayi, saboda samar masa lafiya sai taji wannan bangaren na Zuciyar ta na danne wanchan.

"Ki zauna anan, bari naje ni nasan me zanyi."

Sai ta bud'e kofar ta fita,ta nufi gidan. Kamar an dasa Mah-Mah a wajen ta k'asa cewa komai har ta shige ciki, kamar tace ta dawo amma sai ta hau karfafa kanta da tunanin abubuwan da Hajiya Umman tace mata.

Da sallama ta shiga gidan, Hajiya na na zaune tana kallon Arewa 24 ta amsa tana mata maraba sannan ta nuna mata wajen zama, maimakon ta zauna sai ta yi zaman dirshan gaban Hajiya cikin girmamawa ta gaida ta, ta amsa mata a sake duk da bata gane ta ba, lankwashe murya tayi cike da son tura sakon da tazo dashi cikin kan Hajiyan

"Hajiya magana ce me matukar muhimmanci ce ta kawo ni, kinsan yadda zamanin nan ya zama, shiyasa mutane yanxu basa taimako, domin idan ka taimaki mutum ka dauko shi daga rana ka kawo shi inuwa, sai yayi kokarin turaka ranar."

"Haka ne kam."

Hajiya tace cike da gamsuwa.

"Toh abinda ya kawo ni Hajiya akan jikar ki ne Amrah."

Gyad'a tayi ta sake gyara zama jin an ambaci tauraruwar zuciyar ta

"Wani abun Amratun tayi ko ya akayi?"

"Ko d'aya Hajiya, wato abinda ke faruwa shine..."

Sai ta dauko labarin dauko Sultan daga orphanage din nan,da kawo shi gidan da duk abubuwan da suka faru da yadda aka rike shi tamkar Safwan, sannan sai ta gangaro kan rashin lafiyar Safwan din, ta karkare da cewa

"Toh kinji duk wannan alkhairin da akayi wa yaron nan, ashe shi sam ba haka bane a cikin zuciyar sa, babu wanda yake son ganin baya irin Safwan da iyayensa ba kuma ya san cigaban Safwan din ko k'ad'an, hakan tasa da yaji maganar dake tsakanin Safwan din da Amrah sai da yasan yadda yayi ya shiga tsakani, ance ma Amrah bata son shi da farko tunda dama chan ita Safwan take so, toh ba'a san ya akayi ba sai gashi yanzu ta k'ek'ashe k'asa tace sam shi take so, ta kuma ciwa Safwan mutunci har ta kaishi da kwanciya asibiti, wanda likita yace Zuciyar shi daf take da daina bugawa idan har be sami abinda yake so ba..."

Sai ta saka kuka kamar gaske tace

"Baki ga yadda yar'uwata mahaifiyar Safwan din ba ta fige ta lalace saboda tunani, gashi taki yarda ayi ma Sultan din magana a tsawatar masa saboda Zuciyar musulunci irin tata, ni tsoron da nake ma Allah yasa ba asirce miki jika yayi ba tun da kinga yana chan tare dasu."

Sai kuma ta hau girgiza kai

"Ai babu wani dogon tunani ma tabbas abinda yayi kenan, gashi baka san asalin yaro ba ma karka dau yarka ka bashi azo gaba akeji, tunda kinga su iyayen da suka rikeshi tsakani da Allah ma be barsu ba ballantana kuma matar da take ikon sa idan ya aureta, ai sai abinda yayi."

Iyakar baci ran Hajiya ya baci, a rayuwar ta ta tsani cin amana da duk wani abu da xai shafe ta, iya zaman su da mutanen nan basu taba ganin wani abu da zai nuna cewa ba sune suka haife shi ba, amma ya rasa ta inda zai saka musu sai ta kashe musu d'an nasu k'waya d'aya,aiko in dai tana numfashi hakan ba zata taba faruwa ba, aure da Safwan da Amrah kamar anyi an gama indai ita ta haifi Abban nasu. Mikewa tayi tsaye ta ce

"Nagode sosai da wannan labarin da kike zo dashi, a yau ba sai gobe ba zan nuna mishi ni ke da iko da d'ana da jikokina, zan kira iyayen Safwan din suzo a tsaida maganar rana, dan bazan yarda jikar tawa mafi soyuwa a gareni ta fad'a hannun da zamu zo muna dana sani. Shiyasa aka ce tsintacciyar mage... Allah ya kyauta."

"Amin." Tace tana sakin murmushi ba tare da ta bari hajiyan taji ba, sai ta mike ta gyara zanin ta sannan ta bud'e jakarta ta ciro kudi duhu biyar CIF ta ajiye a gefe

"Gashi Hajiya aci goro."

Kallon kudin Hajiya tayi ta girgiza kanta

"Gaskiya ba zan karbi kudinki ba a wanne dalilin?"

Ta kura mata ido da kallon dake nuna kamar tana son karantar yanayin ta, da yake gogaggiyar mace ce sai tayi saurin wayance wa tace

"Haba Hajiya karki dauki wannan kudin da wata manufa, ko daya ba abinda kike tunani bane, tun kafin na zo nayi niyyar siya miki goro dan ni wallahi daya na dauke ki da Hajiya ta, dan idan ba me son ka ba, babu me zuwa ya sameka akan abinda ya shafi ahalinka, ki dauki wannan kudin a matsayin kyauta daga d'aya daga cikin yayan ki ki samin albarka dan Allah."

Jinjina kai Hajiyan tayi dan bata da bakin magana kuma sai kawai tace

"Allah yayi albarka nagode."

"Amin." Ta amsa sannan tayi mata sallama ta fita.

Mah-Mah na hango ta, ta bud'e kofar motar, tana jiran ta karaso dan har ga Allah hankalin ta ya kasa kwanciya akan abin, da hannu ta nuna wa driver alamar ya shigar da kayan sannan ta zauna a wajen zaman ta

"Albishirin ki?"

"Goro." Mah-Mah ta amsa sai dai kana jin yadda muryar ta,ta fita zaka gane kamar akwai d'an tsoro, tsoron abinda kunnuwan ta zasu jiyo mata.

"Komai dai an gama dan Hajiya ta tabbatar min a yau zata kira mahaifin yarinyar sannan zasu aiko wakilan sa suzo asa musu rana kinga kowa ya huta kenan."

Kada kai Mah-Mah tayi, sannan tace

"Me kike fad'a mata da ya fusata ta haka?"

"Me na fad'a mata kuwa? Bayan gaskiya, na fad'a mata waye Sultan a wajenku, na kuma bata LABARIN komai, na tabbatar da ban bar gurbi daya a cikin kanta da zai bata damar tunanin ko sharri aka masa ba..."

Sai ta bawa Mah-Mah labarin komai ba tare da ta rage komai ba, ta rikice sosai ta fara fad'a

"Haba Yaya Umma ya zakiyi haka, wannan sam be kamata ba."

"Kinga dalilin da yasa ake cutar ki ko? Ke saukin kai shikenan kina kallo za'a kashe miki d'an kina wannan tsoron naki."

"Amma ai da ba ta haka akayi ba."

"Ta yaya za'ayi kenan? Lokaci fa ta fiya yake, kinga idan fa baki koyi yadda zaki tackling problem tun da wuri ba wallahi a ciki zaki dinga kwana, ni dai nayi Abinda nake ganin shine daidai, kuma ba komai yasa ni yin hakan ba sai dan naga hakan shine daidai, sannan kuma na dauka Safwan nima d'ana ne zan iya zartar da komai akansa..."

"Amma idan hakan be miki ba, toh Allah ya baki hakuri da na shiga Abinda bani da iko akai."

Ta karashe tana kallon window alamun bata ji dadi ba

"Kiyi hakuri ni ba da wata manufa da fada ba."
Chapter 29 · 0% Book details