← Book details Abinda Ke Cikin Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 108

Sashe 19

Abinda Ke Cikin Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

“Toh sai akai yaya? Ina ruwana dan ta kasa sa yar ta. Ni Khadija ba ‘yata bace? Kafin na samu nawa ‘yayan wana fara samu a duniya? Mahaifiyar ta Jamila daga ni sai ita, Kuma duk duniya babu wanda nakeso sama da ita duk cikin yan uwana, Kuma gudan jininta wadda itama ‘ya ce agare nin zan ki kyautatawa? Shekara nawa ina rokon abani ita na rike hakan bai samu ba sai yanzu. Karki batamin rai hajia. Yauwa Khadija monday zaki fara attending classes dinsu, Na tsawon watanni uku ne kacal. Hameeda ga MasterCard dina da safe ki kaita shopping ki sauya mata da irin shigar mu tanan, Ku bawa tailor dinku dinkunan ta, Ki kaita saloon a gyaro mata kan ta amata manicure..”

Ni dai shiru nayi ina sauraron Kawu tamkar a mafarki, Mami tayi kwafa tana kada kafa,

“Alhaji wannan yawon ai ba na Hameeda bane sai dai ko driver ya kakkaita. Amma ya za’ai ta katse schedules dinta ta kaita koina?”

“Toh Hajia ai gidan ki ne, Ya’ya kuma naki ne ko? Shikenan yayi kyau! Khadija ki shirya da sassafe ni zan kaiki ko’ina. Jeki debi abinci kici ki kwanta.”

Kada kai nayi na silale na gudu da’ki, Ina jiyo sanda ya koma parlorn sa, Mami nata tsaki tana mita, Hameeda ma na taya ta. Jiki na gaba d’aya ya saki yayi sanyi, A darare Na fita na shiga kitchen na zuba abinci naci acan, Na koma daki na kwanta. Saboda Banda nauyin Bacci ina jiyo sanda Ya Shukra ta dawo suka hau bata labari . A haka bacci yai awun gaba dani, Bansan sanda suka dena magana ta ba.

*WASHE-GARI*

Da wuri na tashi na shirya, Na wanke bandaki, saboda na fara gane kanshi da amfanin wasu abubuwan dake cikin sa. Sunata kumbure fuska a haka na bisu na gaggayshe su, Ranar Kawu ko abincin safe bai ciba yace muje, Gurare sosai ya kai ni ya narkomin kayan yan gayu da atamfofi da laces da materials, Abayoyi suma fal da takalma da jakankuna Harda kayan kwalliya dana man shafawa. Ya biya ya bawa tailor ya gwada ni, Daga nan muka je salon aka wankemin kai na, Aka gyaramin kafata da farata na. Wallahi tamkar ba ni ba. Daga nan ya biya dani kasuwar waya, Ya siyamin dalleliyar waya ta zamani. Wallahi tsabar farin ciki Bansan sanda nasa hawayen dadi ba, Na shjga kwararawa Kawu addua. Ranar dai gaba d’aya cinyeta mukai a bukatu na, Sannan ya dire ni a gida ya wuce kasuwa.

______________________
KUNA BUƘATAR A TALLATA MUKU KAYAN SANA'ARKU A PAGES ƊIN BOOKS ƊIN ZAFAFA BIYAR 2021?.

To kuzo ga dama ta samu💃🏻💃🏻.

        Ina ma'abota son a tallata musu hajojinsu a kafafen yanar gizo suke?.

Tofa kuzo dama ta samu, dan jerin gwanon haziƙan marubanku ƴan biyar sun fiddo muku da hanyar da kuma kasuwancinku zai zagaya lungu da saƙo ta dalilin shafukan littatafai.

Ga duk mai buƙatar a saka masa tallan kayan sana'arsa a shafin littatafan mu na zafafa biyar zai iya tuntuɓar waɗan nan Numbers 0903 234 5899 or 09033181070 ta WhatsApp, idan har agama buks ɗin kana buƙata a sakamaka talla zamu saka maka akan farashi mai sauƙi. Idan kuma wasu adadin pages kake buƙata koda ɗaya ne duk zamu saka maka akan farashi mai sauƙin gaske🤓.

Kuyi maza ku kawo, mai haja shike talla, mai saya kuwa shike neman sauƙi😻😻😄🤗.

______________________
ZAFAFA BIYAR
NA KUDI NE:::

Duka BIYAR 5 zaku samesu akan garabasar naira 700 kacal,

Guda hudu 4 Kuma 500,

Guda uku 3 Kuma 450,

Guda biyu 2 Kuma 400,

Guda daya akan 300.

Ma'ana
Each one is 300
2 is 400
3 is 450
4 is 500
5 is 700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO- *0812652655*
ACCOUNT NAME- *HAFSAT LAWAN GAMBO*
BANK NAME: *ACCESS BANK*

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

*+234 903 234 5899*

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

*09033181070*

Karku Bari ayi Babu ku domin wannnan salon na daban ne
SABUWAR SHEKARA
SABON SALO

TEAM#ZAFAFABIYAR🔥
[3/16, 7:39 AM] Maman Maryam: *Wannan littafin na kudi ne idan kina so ki karanta ki tuntubi numbobin nan*

*0903 234 5899*
Or
*09033181070*

© Hafsat Rano
Page 11

***A kusan tare suka isa falon, Abba ya zauna a saman kujera, shi da ita kuma suka zauna a k'asa, ya kalmashe kafar sa cike da girmamawa kansa na k'asa, satar kallon sa Amrah tayi sai kuma ta sauke kanta itama jin Abba ya fara magana

"Labari ya same ni, Umman ku ta fad'a min abinda ke faruwa tsakanin ku, dukkanin ku namu ne, kai d'an mu ne kamar yadda Mamana take a wajen mu,dan babu abinda zan cewa Alhaji Sulaiman sai godia, dan haka ko da na samu labarin naji dad'i, amma kuma akwai abinda ya bani mamaki, munyi magana da shi Alhaji Sulaiman, sai dai kuma labarin ya sha banban da wanda naji yanzu, kayi magana da su ne akan maganar?"

"A ah Abba, dama ina so ne a d'an kara lokaci."

"Toh... Toh shikenan dai, zanyi magana da shi muji."

"Toh Abba." Ya amsa.

"Shikenan zamuyi magana idan Allah ya kaimu, ke kuma Mamana, jeki ki sami Umman ku."

Tashi sukayi a tare, ya wuce dakin su ita kuma tayi ma Umma knocking, tana shiga tayi saurin tashi

"Amrah...Kun taba wata magana da Safwan ne?"

Shiru tayi, sai da Umman ta sake maimaitawa sannan tace

"Yana yawan yimin text messages amma bayan haka bamuyi wata magana ba."

"Kin sani? Amma kuma baki taba fad'a min ba? Har sai dai mahaifin ku ya karbi maganar shi? Ya kuma amince."

"Ummah!" Ta zaro idon ta

"Eh sunyi magana kuma har ya amince musu, sai dai duk wannan ba matsala baçe, tun da ko an daura aure ma ana iya fasawa, matsalar itace, ta yaya kike so mu aura miki k'ani bayan ga wansa kuna soyayya? Kinsan me hakan zai haifar? Sannan ni tun da nake ma ban taba ganin yan uwa masu kaunar junan su kamar yarannan ba, me kike tunanin zai faru?"

Kuka ta saka sosai, ta fara girgixa kanta tana matsowa cikin dakin sosai

"Kuma wallahi Umma ni Ya Sultan nake so, bana son Ya Safwan."

Dafe kai Umma tayi, wannan shi ake kira gaba kura baya siyaki, tayaya zasu warware wannan abun? Wa zasu bawa a ciki su hana? Hakan zai iya kawo matsala sosai da iya hasashen ka ba zaka hasaso me zai faru ba, ta lura da yadda suke son junan su ita da Sultan, ace kuma an bawa kanin sa ita ya zata kasance kenan, rarrashin ta tayi, sannan tace

"Kije ki kwanta zamuyi magana da Abban ku, komai zai zo da sauki in Sha Allah."

Daki ta wuce da sauri ta fad'a kan gado, ta saka kuka sosai, Afrah ta taso tana tambayar ta menene amma ta k'asa amsa mata, zuciyarta zafi take mata sosai, ga wani irin tsanar Safwan da take ji, dan me yasa zai kai maganar wajen iyayensu bayan shi da ita basu taba wata doguwar magana ba, me yasa xai mata haka? Wayar ta dake ajiye a gefe ta shiga kara, tayi saurin tashi ta dauka, ganin shine yake kira ta daga da sauri, babu sallama babu komai tace

"Ina ganin girman ka, tun kafin nayi maka abinda baka taba tunani ba ka koma ka samu su Mah-Mah kace ka janye maganar auren daka je musu, dan bana son ka, bana son ka ko kadan!"  Bata jira komai ba ta kashe kiran ta sake fashewa da kuka.

_"Bana son ka, bana son ka ko kadan!!!._"

Wata murya a bayan kansa ta shiga amsa kuwwa a cikin kunnensa, runtse idon sa yayi ya dafe kansa da hannayen sa, ya fara ganin dishi dishi, a hankali a hankali dakin ya soma juya masa, sunan Allah ya shiga ambata yana jin yadda numfashin sa ke sarkewa, kafin duhu ya mamaye ganin sa baki daya.

Kuka take sosai da k'yar Afrah ta bata baki tayi shiru sannan ta bata labarin abinda ya faru tun farko har xuwa karshe, ta kuma rufe da bata son shi ko kadan ita Sultan take so, mamaki ma ta bawa Afrah dan bata taba tunanin soyayya zata kama Amran haka ba. Haka suka kusan raba dare suna maganganu sai wajen asubah suka kwanta. Da safe Ummah ta kirata bayan Abbah ya fita, suka kara tattauna maganar ta kuma kwantar mata da hankali da cewa kila Abba ne yayi mistaken sunan ya dauka Safwan sukace, Amma yace xai kira Alhaji Sulaiman din sai ya karaji. Jin haka ya saka ta kwantar da hankalin ta, ta kuma cigaba da walwalarta tana ji a ranta tasan babu wanda zai mata auren dole.

****
Chapter 19 · 0% Book details