← Book details Abinda Ke Cikin Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 78 OF 108

Sashe 78

Abinda Ke Cikin Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

_ADIRESHI: KUNTAU KARSHEN KWALTA KAN A KARASA YAN TIFA, DAIDAI GADON KAYA CEMENT.._

***

"Me ya same ki a kafa?"

Ya fad'a yana taba kafar daidai wajen da suka daure , wajen yayi shati yayi ja abinka da farar fata

"Wai dan karna gudu." Tayi maganar a hankali tana tuno abinda ya faru

Shiru yayi ya kalli k'asa bece komai ba, be san kalar rashin mutuncin da zai wa Madaki ba idan suka hadu, haduwar su ba zatayi kyau ba, zai nuna masa ya taba masa abinda ba zai iya kyale shi ba. Tunowa da yayi da mutanen da ya gabatar masa a matsayin iyayen sa ya tabbatar da Madaki ya gama raina shi, raini irin na karamin yaron da be san komai ba. Ko ina ya samo su ma oho, daga gani yayi amfani da talaucin su ne ya saka su aikin.

Shigowar Dr Labaran da Dr Fiddausi ya saka Sultan mikewa yana matsawa baya

"Dr. Ashe kana nan."

Mika masa hannu Sultan yayi suka yi musabah sannan yace

"Ina nan."

"Ok amarya ya jikin naki?"

"Da sauki."

"Akwai abinda ke miki ciwo?"

"Kaina."

"Owk zai daina a hankali."

Kallon ta Sultan yayi yaga tana ya mutsa fuska tana cije baki, sai ya maida duban sa wajen Dr Fiddausi yace

"Dr tana bukatar bacci kamar."

"Owk dama za'a mata allurar da zata huta sosai, nurse fati zata shigo dasu yanzu."

"Owk thank you Dr."

Fita tayi bayan ta duba abinda zata duba tayi wa Amrah bf da sauran abinda ya dace.

Kamar wanda maganar ta fizgo daga bakin shi haka yayi maganar da tun dazu yake son tambaya amma yana tsoron abinda Dr Labaran din zai ce

"Dr Safwan fa?"

"Alhamdulillah, zamu ce tunda an samu nasarar tsaida jinin kuma an cire bullet din, abu daya yanzu ake bukata shine jini, saboda yayi loosing jini da yawa,and he's still unconscious zamu dai ga abinda Allah zai."

"Dama ba'a saka jinin ba!?" Ya fad'a yana kallon Dr din hankalin sa a tashe

"No, an dauki sample na jinin nashi an kai lab za'a yi test, sannan na fad'a wa su Baba su tsaya da an yi test din su karba a samo jinin da sauri, ba'a san blood group dinsa ba kasan."

"Wannan ai emergency transfusion ne, ya za'a tsaya wasa Dr?"

"Kasan sabon tsarin asibitin tun bayan wanchan case da aka samu na yaron nan da aka sa ma wrong jini da akayi amfani da I'd card din sa wajen ganin blood group din nasa, ashe ba daidai bane a karshe  ya rasa ransa."

"Oh Allah." Ya juya da sauri ya fita, ya nufi blood bank din, yana tafiya kamar zai hard'e saboda sauri, ya rasa abinda yasa ake samun irin wannan negligence wasu lokutan a asibitocinmu.

Yana isa ya karbi blood bag yayi sauri ya kai lab din, AB+ ne shi haka ma Safwan, blood group dinsu daya dan be manta sanda suka yi ba lokacin zasu shiga school, ya tuna a lokacin bayan sun karbo result din suna dubawa Safwan yace

_"Kaga ashe ma har blood group dinmu dayà ne."_

_"What a coincidence." Sultan yayi maganar yana kallon result din_

_"Ikon Allah kenan, kaga duk wanda yake neman jini a cikin mu sai daya ya bashi."_

Daga idon sa yayi yana kallon yadda jinin ke taruwa a bag din, yana kuma hasaso halin da Safwan din yake ciki, halin rai ko mutuwa. Gaba daya ji yake kamar be taba shiga aji da sunan koyon karatun likitan ci ba, kamar ma babu komai ma akan nasa sai tarin tashin hankali da tunanin halin da Safwan din yake ciki. Baya jin ko allura aka bashi a yanzu zai iya yiwa mutum balle su bada magani ko aiki.
    Yana kwance bayan sun gama daukar jinin sun fita yana hutawa kafin ya tashi Adnan yazo kansa ya tsaya, gaba daya shi kansa Adnan din a hargitse yake balle shi, yana tsaye har ya gama hutawa sannan ya tashi Adnan din ya taimaka masa suka fito daga ciki suka jera a tare zuwa main building din sannan suka karasa inda su Abba suke, lokacin har an fara kiraye kirayen sallar asubah, masallaci suka wuce kai tsaye bayan Adnan ya leka Amrah yaga tana bacci.
   Bayan sun yi sallar sun dawo, Daddy ya ciro wayar sa da yaji tana da vib a aljihun sa, yasan Mah-Mah ce kuma tun dare take kira anma sai ya kasa gaya mata komai ya tura mata da sakon zai iya kai wa dare be dawo ba. Abun yayi matukar daure mata kai,haka ta cigaba da kiran Safwan shima amma shi gaba daya wayar tasa ma switch off, abinda ya karaa tasar mata da hankali kenan har ta kasa runtsawa tana tunanin abinda zai sa Daddy kwana a wani waje kuma yaki daga wayar ta ma balle suyi magana, dole jikin ta ya bata akwai matsala. Shiyasa tana yin Sallah ta sake kiran sa dan zuciyar ta, ta gaza daukar abinda shaidan ke ta raya mata.
  Matsawa kad'an Daddy yayi ya daga wayar gami da sallama

"Dan Allah me yake faruwa ne? Hankali na ya kasa kwanciya Ina jin kamar babu lafiya, wani abun ya samu Safwan ne? Dan Allah karka boye min."

"Kina jina? Ki kwantar da hankalin ki, muna asibiti ne Safwan ya dan gamu da tausayi,Amma....

"Innalillahi wa Inna ilaihi rajiun, na shiga uku, me ya sami Safwan din?"

Ta fashe da kuka tana mikewa tsaye,

"Ki kwantar da hankalin ki, in Sha Allah zai samu lafiya."

"Innalillahi wa Inna ilaihi rajiun, Innalillahi wa Inna ilaihi rajiun."

Kashe wayar yayi ya girgiza kansa, yasan dama dole ne ta shiga tashin hankali, shiyasa ma kawai yace mata ta tawo din dan yasan ba ma yarda xatayi ta zauna a gidan ba, sai dai be san zuwan nata abinda zai haifar ba, be san ta yadda zata kalli abun ba baya so tazo ta sake saka sultan a cikin wani tashin hankalin, wannan na yanzu ma kad'ai ya ishe shi.

Kusan a tare Mah-Mah suka iso da su Afrah, har lokacin babu wanda yasan halin da Safwan din yake ciki. Sun shiga sun duba Amrah dake ta bacci suka fito suka rufe mata kofar saboda Dr tace tana bukatar hutu saboda kanta.
   Kasancewar Amrah a asibitin ya saka Mah-Mah ta gane me ya faru da Safwan. Sosai ta shiga yin kuka tana fad'ar maganganu, maganganun da suka sake saka Sultan a cikin matukar damuwa, da k'yar Daddy ya samu tayi shiru sai kuka da take k'asa k'asa su Umma na bata baki.
    Ana cikin haka Anty Amina ta kirata, kamar ba zata duba ba, ganin Amina ce yasa ta tashi ta daga kiran tana kuka.

"Lafiya Yaya?"

"Amina, Safwan ne kidnappers suka harbe shi, yanxu haka bamu san halin da yake ciki ba."

"Innalillahi wa Inna ilaihi rajiun, yaushe?"

"Jiya."

"Wayyo, Allah ya bashi lafiya, bari zan kiraki yanzu, bari na duba ko za'a samu flight sai mu tawo da Umaimah Ya Ummah, ki kwantar da hankalin ki Allah zai bashi lafiya."

"Amin."

Katse kiran tayi, ta koma wajen da ta taso ta zauna.

Fitowar Dr's din daga dakin ya saka duk suka mike, Su kayi wajen sa

"Dr ya jikin nasa? Ya farfado?"

"Ku cigaba da yi masa addu'a, duk da akwai numfashi a tare dashi amma yana cikin critical condition, addu'ar ku kawai yake bukata a halin yanzu."

"Innalillahi wa Inna ilaihi rajiun." Suka had'a baki, matan suka cigaba da kuka mazan kuma suka matsa baya suka jingina da bango suna addu'a. Sultan da yaji wani dum a tsakiyar kansa yayi saurin bin Dr din,

"Dr, dr..."

"Na'am, Dr ya masu jikin?"

"Alhamdulillah."

"Allah ya basu lafiya."

"Amin ya Allah, Dr me kuke gani game Safwan?"

"Eh toh, kasan dai ba zamu fito fili muce wa iyalen mara lafiya ba zai rayu ba, ko mu fad'a musu abinda zai tada musu hankali, amma maganar gaskiya Safwan baya responding, kasan da matsalar heart din nan tashi, dole abin zai sake zama complicated, ga jinin da ya rasa, I can't say enough, amma kaima Dr ne, a very good one ma, ka shiga ka ganshi, ka duba report din da dr Labaran ya rubuta."

"Shikenan Dr, thanks you."

"Allah ya bashi lafiya."

Ya wuce shi, kasa motsawa daga inda Sulthan yake yayi, yaji kamar an sare masa gabobin sa, da k'yar ya ja kafafuwan sa a hankali ya kaisu dakin, ya tura kofar kamar me jin tsoro, tsoron abinda zai tarar.
  Da wani irin yanayi yake kallon wanda yake kwance a gadon asibitin, wanda yake amsa sunan Safwan dinsa, yayi wata iriyar rama ta ban mamaki, ga wani mugun fari da yayi wanda kallo daya zaka masa kasan babu wadataccen jini a jikin sa. Numfashin sa dake sama sosai ya kalla ta jikin oxygen din dake makale a hancin sa, fuskar sa ta sirance sosai leben bakin sa ya bushe yayi fari fat.
   Rike gefen gadon sultan yayi, ya durkushe a wajen kuka na tawo masa, kukan halin da Safwan yake ciki, kuma duk a dalilin sa, a dalilin son faran tawa birnin zuciyar sa, yes yasan yana da bukatar iyayen sa a kusa dashi musamman da ya tabbatar da wanzuwar su a doran k'asa ba wai mutuwa sukayi ba, amma da ace an bashi zabi tun farko, an bashi zabin haduwa dasu ko shigar Safwan din wannan halin toh tabbas zai zabi ya hakura da su din saboda Safwan din.
   Babban dalilin da ya saka shi k'in fad'a wa har Amrah abinda ya shirya da tafiyar sa duk dan kar su shiga ciki,duk dan kar wani abu ya same su ne, sai gashi komai ya juya masa, a lokacin da yake farin cikin samun asalin sa, a wannan lokacin ne kuma yake bakin cikin halin da Safwan da Amrah suka shiga saboda shi.
  Gani yayi ya motsa, ya tashi da sauri yana son gasgata abinda idon sa ya ke gani, da gaske motsin yayi, yana kuma cigaba da kokarin motsa jikin nasa duk kuwa da ciwon da yake jiki.
Chapter 78 · 0% Book details