Sashe 51
Abinda Ke Cikin Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Fita Daddy yayi sai a sannan sultan ya lura da Mah-Mah bata dakin, be ji fitar ta ba, dawo da kallon sa yayi kan Safwan da shima yake kallon sa. Cije baki Sultan yayi, da ace Safwan din Kalou yake da babu abinda zai hanashi bugunsa wallahi, amma duk da haka sai ta kama hannun sa ya murde sosai har sai da yayi kara.
"Karasa ni zakayi?"
"Baka kyauta min ba Wallahi ,baka kyauta ba ban kuma yi murna da abinda kayi ba Wallahi ko k'ad'an." (karyar banza😂ana so ana kaiwa market)
"Naji, ni bance baka kyauta min ba sai kai, wallahi da ace zan iya da sai na maka abinda zaka yi mamaki, me kaso kayi kenan? Shikenan ni kowa gani yake rayuwa ta limited ce shisa kowa sai ya hakura da abu ya barmin, sau nawa kana kwana da yunwa saboda ni? Sau nawa kana karbar duka na a makaranta, shine yanzu ma zaka sadaukar da abinda kake so saboda ni, nine abin tausayi ko? Kuma kaine kadai kasan abinda ya dace kenan."
"Safwan..."
"Barni kawai na gama fad'an abinda ke raina."
Ya fad'a a hasale
"Banji dadin abinda kayi min ba, kuma da ace sai da akayi auren na gano wallahi ba zan taba yafe maka ba, ta yaya ma kake tunanin zan iya rayuwa me dadi bayan na gano abinda kayi?"
"Duk baka fuskance ni ba Safwan, banyi dan wai kaine me rauni ni kuma zan iya jurewa ba, nayi ne saboda kai kafi komai muhimmanci a waje na, babu abinda zaka nuna kana so ina da iko dashi na hanaka,babu shi wallahi."
"Na yarda na yarda, amma ai baka da ikon chanja Abinda ke cikin zuciyar Amrah idan kana da ikon chanja taka ko?"
Shiru yayi be ce komai ba.
"Baka da amsa ai, malam karka sake irin wannan ganganci ne."
"Ba zan sake ba." Yace dan ya gane Jan maganar ma wani pain take karama Safwan din.
"Me yake maka ciwo yanzu?" Yace yana taba chest dinsa.
"Babu komai na dawo daidai bayan allurar, I'm just weak ne so zan kwanta nayi bacci zuwa anjima."
"Ok." Yace yana mikewa
"Zan dawo anjima na sake duba ka, if you need anything call me."
"Yes sir." Yace yana masa murmushi.
Fita yayi ya ja masa kofar, da sauri Safwan ya tashi ya zauna yana saka hannun sa a saman kirjin sa, babu abinda yayi sauki na daga abinda yake ji sai ma karuwa da yayi, da gaske cire soyayya a zuciya ba karamin abu bane.
"Allah ka sassauta min." Yace a hankali hawaye masu zafi suka sauko daga idon sa zuwa saman fuskar sa.
***Tana tsaye gaf da kofar, fuskar ta da ta dame sakamakon kukan da take wanda ya hadu da uban powder da ta gambaza ya sa ta sake chanja kama sosai, saura kad'an ya bigeta yayi saurin matsawa yana mamakin abinda take a wajen.
"Magana nake so muyi." Tace kai tsaye, tana saka bayan hannun ta, ta goge fuskar ta.
"Ok ina jinki." Yace yana tsayawa sosai
"Wai da gaske kayi aure?"
Maimakon ya amsa mata sai yace
"Akwai matsala ne?"
"Eh akwai, Mah-Mah bata fad'a maka komai ba?"
"Me fa?"
"Sakon da Mummy ta bata tun kana Canada."
"Sako, sako? Ban gane me kike nufi ba."
"Ya Sultan." Afrah ta kirashi tun kafin ta karaso wajen ganin shi tsaye da wadda ta tsana, Umaimah.
Juyowa sukayi su dukka, ta karaso da dan saurin ta fuskar ta a sake tace
"Ango kasha kamshi."
"Ke ko?" Yace yana murmushi
"Naji dadin yadda komai ya kasance wallahi,nayi muku murna."
"Thank you sis." Yace
"Dama Ya Adnan ne yace nayi maka magana kazo ka duba Amrah, tana kwance bata da lafiya, ya kira wayar ka baka daga ba."
"Me sameta?"
"Ciwon so mana." Tace tana dariya.
"Allah ya shirye ki, nasan ba zai wuce ciwon kai ba, bari na shiga ciki na dauko miki magana ki kai mata."
Kallon Umaimah tayi taga reaction din fuskarta, kamar hakan yayi mata dadi dan da tayi mugun hade fuska amma sai taga ta dan saki fuskar, da sauri kuwa tace
"Allah gwara dai kazo muje ka duba ta da kanka, kasan ta fa bata shan magani gwanda kawai ayi mata allura."
"Idan ma mutane kake tunani, toh tana dakin ya Adnan, mutane sun yi yawa a ciki shine Umma tasa muka rakata dakin Adnan ta kwanta a chan."
"Ok sai kiyi min jagoranci." Yace sannan yayi hanyar fita. Kallon Umaimah tayi ta sakar mata murmushi sannan ta wuce.
Wani irin kunci ne ya ziyarci zuciyar ta, wannan wanne irin wulakanci ne, magana fa take masa amma kamar ma ya manta da ita a wajen, ba ma kamar bane ya manta da babinta yayi tafiyar ta ya barta tsaye. Kukan da ta yi kokarin tsaidawa ne ya dawo mata saboda tsabar takaici. (iska na wahalar da me kayan k'ara)
***Itace a gaba yana biye da ita, da yake bangaren Adnan din a farkon shiga gidan yake shi yasa babu wanda ya ga shigar su sai yan tsirarin mutane. Kofar ta tura, sai ta tsaya bata shiga ba ta bashi hanya
"Iya nan zan tsaya."
"Ok." Yace yana cire takalmin kafar sa sau ciki, kayan da yasa ne na dazun farare sai dai ya ajiye babbar rigar a mota lokacin da yaje ganin madaki. Dan karamin madaidaicin daki ne da yasha carpet gaba daya me taushi, takawa ya shiga yi kafar sa sanye da ankle sock baka, tun da suka dawo be shigo dakin ba sai yau. Daga chan saman gadon ya hange ta, ta cure waje daya kamar sardine ta lulluba da mayafin ta daya sauko ya rufe kafarta ruf ya kwanta a k'asa.
Ja yayi ya tsaya yana lissafi da kidddigar abubuwan da suka faru dashi a cikin awoyin da basu gaza biyar ba. Haduwar sa da Madaki da yadda ya haska masa wani haske na daga abinda yake son sani, sannan sai kuma aure, auren da ya cire daga tsarin sa a yanzu sai gashi Allah ya chanja komai ba tare da yayi komai ba.
Idan yace ya taba tunanin komai zai chanja a dan karamin lokaci irin haka yayi karya, Lallai idan ka dogara da Allah komai zai zo maka da sauki.
Motsawa tayi, kamar zata juyo sai kuma ta fasa,ta cigaba da baccin ta, duk d ba jin dadin baccin take ba amma zai rage mata mugun tunanin dake damun ta, tunanin ta a gidan Safwan suna rayuwa a inuwa daya.
Ta gaban ta ya tsaya, ya tsura mata ido yana kallon doguwar fuskar ta tun daga saman girar ta, zuwa habar ta,dan madaidaicin hancin ta da ya dace da yanayi da tsarin halitar ta,zuwa d'an karamin bakin ta. Abu yaji ya tafi masa daga makoshin sa ya fad'a cikin sa, kamar ace ka tara abu a bakin ka sannan ka hadiye shi a lokaci guda, sai dai nasa be san menene ba.
Durkusawa yayi akan guiwowin sa, a gabanta yasa hannun sa daidai hancin ta, yadda yaji tana fitar da hucin zafi yasa yayi saurin kai hannun sa saman kanta, yaji wani irin zafi, da sauri ya sa hannu ya yaye mayafin da ta rufa dashi, hakan yasa ta farka da sauri. Da wani irin yanayi take kallon sa, me yake yi anan? Ta tambayi kanta, tunowa da tayi yasa tayi saurin tashi.
"Jikin ki yayi zafi sosai." Yace ba tare da ya kalle ta ba, yana kallon wayar sa. A kunne yasa wayar
"Kizo please ki tawo da bowl da abu haka me tsafta kamar towel ko pieces na wani abu, me kyau dai."
"Yawwa, da ruwa da cup." Yace bayan ya sake kira. Ajiye wayar yayi a gefen gadon, ya kalleta, ta tatttare kafafuwan ta, ta dora su a saman gadon ta cusa kanta tsakanin kafafun nata tana jin wani irin faduwar gaba.
"Sannu." Yace mata sannan ya fita, da sauri ta dago kanta tabi bayan sa da kallo, me yake haka? Tana nan taji an taba kofar, da sauri ta maida kanta ta rufe idon ta kam, kamshin turaren sa da ya karu akan wanda ya fita ya bari yasa ta gane shine ya dawo, tana jin sa ya ajiye abu a kusa da ita, sai kuma taji an shigo, sai taji maganar Afrah.
"Gashi Dr." Tace tana ajiye kayan hannun ta.
"Yawwa kanwata."
"Zan iya tafiya?" Tace
"A ah taimaka mata, tasha maganin nan, sai ki taimaka mata ta goge jikin nata, inda hannun ta ba zai kai ba ki tayata."
"Tabdin, wallahi Allah aiki umma ta sani, wasu baki tayi tace na kaisu ciki nà basu abinci."
"Toh... Yanzu ya za'a yi?" Ya tambaya yana kallon bangaren Amrah yaga reaction dinta
"Ka taimaka dan Allah, kafin nan na gama idan yaso abinda zan karasa sai na karasa."
Da sauri Amrah ta dago ta kalli Afrah, bata san Afrah cikakkiyar mahaukaciya bace sai yau, tasan me kuwa me take fad'a? Kallon da Afrah taga Amrah nayi mata ne yasa tace
"Please Ya Doc, kaga kai doctor ne ita kuma patients dinka ce, ai ba wani abu bane ko?" Ta karashe tana kunshe dariyar ta ganin yadda daga Sultan din har Amrah suke kallon ta kamar wadda tayi wani sabo.
"Bari naje." Kawai tace ta fice da sauri, tana fita ta saka dariya sannan tasa key ta rufe kofar ta waje tayi tafiyar ta.
"Nan da la'asar sai na dawo na bud'e su, kafin nan ita ta gama ciwon soyayyar tata." Tace tana tura key din a aljihun da akayi mata a jikin gown din ta.
Ba ruwana yasin, Mom Sultan kina Ji dai ko?😁😁😁
KUNA BUƘATAR A TALLATA MUKU KAYAN SANA'ARKU A PAGES ƊIN BOOKS ƊIN ZAFAFA BIYAR 2021?.
To kuzo ga dama ta samu💃🏻💃🏻.
Ina ma'abota son a tallata musu hajojinsu a kafafen yanar gizo suke?.
Tofa kuzo dama ta samu, dan jerin gwanon haziƙan marubanku ƴan biyar sun fiddo muku da hanyar da kuma kasuwancinku zai zagaya lungu da saƙo ta dalilin shafukan littatafai.