Sashe 32
Abinda Ke Cikin Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ta gama maganar tana dora kafa daya kan daya tare da juyawa ta kalli sauran one by one. Cike da tsantsar dariya irin ta rainin hankalin nan Gimbiya Najwa ta mike tsaye tare da yin taku daya biyu zuwa uku ta tsaya a tsakiyar su tana gyara kafadun rigar jikinta tace.
“Kwarai kuwa Hajjaju, ina jin kuma ni aka bawa damar karasa yin wannan daddadan mafarkin naki da kika fara. Domin kuwa ni na hango kai na akan wannan kujerar ta sarauniyar Basannabas. Kuma a cikin d'in bin halacci na har na baki mukamin Baba na, wato waziriya ta. Ke kuma..”
Ta Nuna Gimbiya Huwaila wato yar ciroma tare da cewa.
“Ke kuma na yi miki mukamin Baban Hajjaju Najwa, wato Galadima. Na san dai wan.....”
Bata karasa ba Gimbiya Najwa tayi saurin da katar da ita ta hanyar cewa.
“Ya isa dan Allah, wannan ai shirme ne. Idan zaku dawo cikin serious d'in ku toh ku dawo, amman ta ya zaku zauna kuna ta yi mana wasu zantuka na shirme. Yanzu mu maida hankali wajan ganin yarinyar nan ta yi aikin da muka bata, Salman d'an girman kai ne, ko uban shi be yi wannan jiji da kan ba wallahi.”
“Haka ne kam, dan naga kwanan nan itama ya fara yi mata gardama, juya dashi amman sai shigen fadin rai.”
Duk suka yi dariya tare da yin tafi da hannayensu. Gimbiya Huwaila ta ce.
“Sa'adatu ce ma ni take bani mamaki, matar nan Sam taki yadda da cewa yaran nan baya son ganin ta, amman kullum cikin wahalar da kanta take wajan koke koke da wasu addu'o'in ta na shirme. Ai gara ka yiwa kanka maganin matsalar ka, amman kace zaka jira ai sai ka dade, koma ka mutu baka cimma burin ka ba.”
“Ai Baba (Madaki) yace abu d'aya ne yasa shi barin matar nan. Shine baya daukar ta a matsayin mutun mai rai, amman da tuni yasa anyi shekara lahira.”
“Gaba d'aya manta ta nake a cikin tsarin rayuwa ta.”
Jaleela ta fada cikin yatsina fuska. Haka suka zauna suna ta shirya makircin su kamar yadda suka saba. Ita kuwa Sa'adatu tana sashen ta tana kukan zuci da na idaniya. Kuncin da take shiga wani lokacin har mutuwa take roko tazo ta dauketa saboda wahalar da ranta yake yi. Amman tasa a ranta komai daga Allah yake zuwa, yasan kuma lokacin da zai warware mata wannan masifar da take ciki.
Tsab ya yi shirin bacci, yaje ya kwanta akan gado sai gata itama ta shigo cikin shigar kayan bacci masu santsi gasu shara-shara. Gadon itama ta hau tare da rungume shi ya kawar da kai, tunda tasa hannunta ta shafi kirjinsa shikenan ya nemi nutsuwa ya rasa. Kansa ya yi girma yaji kamar an dora masa duniya da abinda ke cikin ta. Wani barin na zuciyar shi kuma yana kusanto masa ita akan ya yi mu'amala da shi.
Kafin kace menene ya firgice sun zama abu d'aya, koda suka dawo cikin hayyacin su wani gigitaccen bacci ne ya dauke shi. Ta tsaya tana kare masa kallo mai cike da fassarori kala-kala. Kanta ta dora saman kirjinsa take itama bacci ya dauke ta a jikinsa.
Garin ya yi shar gwanin dadi, sarki Salman ya fito akan farin doki da aka kawata shi da ado mai daukar hankali. A hankali yake tafiya har ya isa wajan wani ruwa inda wata tsohowar mata tana durkushe sai kuka take yi. Ya tsaya tare da sakkowa yaje kusa da ita cikin sassanyar murya yake mata magana.
“Baiwar Allah lafiya? Me yasa ki kuka a cikin mulki na?”
Ba tare da ta wai go ba ta gyara yagaggen mayafin da ke jikin ta tana share hawaye tace.
“Yara na duk sun guje ni, ba su san gani na bare ganin fuskata.”
“Suna raye kuma?”
Tace,
“Ban sani ba ni, sai dai ina ji a jikina tabbas suna raye. Me ye amfanin yaran da zaka haifa da cikin ka amman su guje ka? Me ye amfanin wahalalliyar nakudar da zaka haifi yara amman su gaza sanya ka farin cikin rayuwa? Kaico da irin wannan duniyar mai cike da tsantsar hasara....”
Ta wai go a fuska sai kawai yaga fuskar mahaifiyarsa, ta riko kafafunsa ta riƙe gam tana cewa.
“Zan tafi, zan kuma yin nisa da yara na da suka kasa gane matsayina a gurin su. Ka tausaya min ka dawo min da yara na, gwara mu zauna cikin talauci tare da su akan su yi arzikin da za'a raba mu. Karka tafi ka bar ni ya shugaba, ka tuna yadda ake ji idan aka rasa wani bangare na jiki. Ka tausaya min ya......”
Sarki Salman dake kwance kan katafaran gadon shi, ga matarsa kwance a jikin sa, kawai sai ji ya yi ya tashi a gigice yana sakin wata firgitaacciyar kara. Jikin shi kuwa sharkaf kamar an tsamo tsumma daga cikin mai....
*KHADIJA*
____Wajen Aisha kawata naje, Wadda muka yi British da ita, yanzu ta kai matakin lecturer a jami’a. Mun sha hira sosai kafin na dau hanyar dawowa gida. Ta babbani shawarwari sosai akan rayuwa, Da yadda zan cigaba da gudanar da ita. Kasancewar garin damina ne tuni hadari ya hadu aka shiga kwarara ruwa tamkar da bakin kwarya.
Gashi na sallami TK driver tun dazu nace yaje ba komai zan dawo idan na kammala. Adaidaita sahun da nake ciki sai tangadi take a titi tamkar zata kifar damu saboda yadda iskar damina ke kad’a ta. Ganin gamu ga gidan rediyon mu hakan yasa na tsaida shi na falfala da gudu na tsaya a rumfar motoci, Waya na lalubo na kira Mas’oud nasan shi kullum yana nan, Baya da day off Saboda kasancewar sa babban ma’aikaci awajen, Na sheda masa ina waje ruwa ya tsare ni. Cikin barin jiki kuwa sai gashi
Da lema a hannun sa ya karo yai saurin rufamin ita akai,
“Sannu Habibaty.. Ya akai haka, Ina kika je?”
“Hmm bari dai Habiby.. Wai zuwa nayi na gayda Aisha da naje wankin kai, Kasan kusa da jami’ar sune shine na biya.”
“Ayyah sannu, Muje ciki ki huta, Dama wannan damina da ake marka marka..”
“Allah yasa mu wuce Lapia..”
Nace dashi, Muka shiga ciki, Kowa yagan mu sai ya tsokane mu, musanman ni. Wai na biyoshi wajen aiki na kasa hak’uri. Office dinsa muka shiga. Sai rawar sanyi nake.Rigar sanyi ya dakkomin acikin kayan custume da ake ajiyewa. Muka shiga hirar soyayya hankalin mu kwance,
“Kyanta ace Ruwan nan da ake ni da ke muna matsayin mata da miji. Mezesa mu wani fito aiki.. Ai sai dai ragargazar soyayyah da..”
Katshe shi nayi. Domin sai ina taka masa birki, Kunya ce ke lullube ni duk sanda yai wadannan kalaman,
“Wai love sai Yaushe zaka zo ka gayda Kawu daddy ne?”
“Zanzo Insha Allahu! Banason zuwa ne batare da komai ya kammala ba. Kinga akwai gini da kawo kudi da sauran su. “
“Gini kuma love?”
“Oum waleeda gwara ace son samu komai na rayuwar da zamuyi ya zama na is ready . Banason muyi wahalalliyar rayuwa.”
Kullum dai zancen kenan. Na ka’da kai kawai ina mai mamakin kalaman sa. Ni fa wallahi Saboda rin k’aunar da nake masa ko lefe zan iya yafe masa .
“Shikenan Mine! Amman da ba sai ka wani wahalar da kanka ba, Ko da irin haya sai mu fara ko..?”
“Shi kenan Oum Waleed zan samu alhajin mu da maganar, Kinsan suna ganin Ya Haysam bai aure ba gani zasu yi nayi kankanta.”
Cuno baki nayi gaba na masa gatsine,
“Ai. Ai.. Ni dai nai dai nima ba canai nima ayi auren ba. Kawai dai saboda Kawu daddy yasan da kai ne.”
“Haba tawaje na.. Ai ke tawa ce. Nine mallakin gangar jikin ki da soyayyar ki Insha Allah. In Shaa Allahu zaki ji..”
Banbashi amsa ba saboda nasan yanzun sai ya kauce hanya. Mikewa nayi na saqale jakata. Ganin ruwan ya tsagaita.
“Zan tafi gida...”
“Okay muje na sauke ki..”
Gaba nayi yana biye dani abaya muka shiga mota ya tayar. Tunda ya fara tuki na juya masa baya ina kallon waje. Yanayi na damina gari yayi shar-shar dashi.
“Oum Waleeda fushi ake dani..?”
“Haba ni na isa? Kawai Ina kallon sarautar Allah ne.”
“Ina son ki.. Ina miki son so tawan..”
Rufe fuska ta nayi da tafin hannaye na da suka sha kunshi na sudan, Sunyi maroon gwanin sha’awa.
“Lallen ki Yayi kyau...”
“Godia nake Habiby..”
Har k’ofar gida ya kai ni, Dai dai lokacin da Kawu Daddy ya dawo Shima. Ganin na fito yasa Mas’oud fitowa Shima ya rissina ya gayshe da Kawu daddy daya futo da sauri da alama mantuwa yayi,
“Kawu daddy sannu da zuwa..”
“Yauwa Sannun mu Khadija..! “
“Yallabai Barka da rana...”
“Barka kadai... Ya aiki?”
“Alhamdulillah!”
Mas’oud ya bashi amsa yana sosa kai, Kawu daddy ya kalle ni ya kalle shi,
“Kamar na san shi ko?”
“Abokin aikinta ne ni yallabai..”
Cewar Mas’oud, Na juya na galla masa harara,
“Abokin aiki kuma?”
Na tambaye shi ina hade girar sama data Kasa,
“Oganta ne ni.. Naga garin da lema shine na sauke ta..”
Mas’oud ya bani amsa yana kallon Kawu daddy. Nayi k’wafa kawai ina galla masa harara,
“Ah Allah sarki, ai na gane ka yanzu. Kai ne mai jinyarta a asibiti. Angode sosai. Tukur driver baya nanne?”
“Eh nace ya dawo gida dazun.”
Musabaha sukai da Kawu daddy ni kuma na shige cikin gida da sauri, Kawu na biye dani. Ya dauki brief case dina a parlor da alamun shi ya manta, Har ya kai kofa, Ya juyo,
“Khadija..”
“Na’am Kawu daddy..!”
“Idan kin samu Lokaci zuwa gobe haka zamuyi magana Insha Allah.”
“Toh.. Kawu...daddy..”
Na bashi amsa a rarrabe saboda yadda cikina ya soma hautsinewa, Kodai ban kyauta bane yadda Mas’oud ke kawo ni gida? Wata zuciar tabani amsa da ‘Kwarai baki halacci ba Khadija. Driver sukutum guda da mota fa aka baki..
“Kawu kayi hak’uri ..”
“Kin cika Shirme! Wayace lefi ki kai? Magana kawai zamuyi ta hankali. Alkhairi ne In Shaa Allahu.”
Yana gama magana ya fice da sauri, Ni kuma na haye sama ina hada hanya. To maganar me zamuyi? Oho.....
.
ZAFAFA BIYAR
NA KUDI NE:::
Duka BIYAR 5 zaku samesu akan garabasar naira 700 kacal,
Guda hudu 4 Kuma 500,