← Book details Abinda Ke Cikin Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 39 OF 108

Sashe 39

Abinda Ke Cikin Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kin karba tayi ta cigaba da kukan da take yi, sosai kukan yake taba san dan dama kukan ta na daya daga cikin weakness dinsa, zai yi magana Mah-Mah ta fito kamar ana tunkud'ata, da sauri ya d'an ja baya sai dai kallon da take masa kad'ai yasa hantar çikin sa kad'awa.

"Lallai ban taba sanin baka da kirki ba sultan sai yau, bayan duk abinda na fad'a maka, amma dan rashin kirki ka rasa aina zaka yi soyayyar ka sai a cikin gida, a cikin gidan ma gidan su Safwan, wanda ya kasance bashi da wanda yake gani sai kai, be yadda da kowa ba sai kai, kai kad'ai ya iya Kaine kake daidai a koyaushe..."

"Mah-Mah ba abinda kike tunani bane Wallahi..."

"Rufe min baki!" Tace a dan tsawace

"Wannan shaidar kad'ai ta ishe ni." Tace tana haska masa hoton dake jikin fuskar wayar, hoton sa ne da Amrah sanda suka kusa yin gware, ba'a dauki hoton ba sai da aka tabbatar duk wanda ya gani kai tsaye zai ce rungume ta yake shirin yi,ji yayi kansa ya sara, ya dafe shi yana jingina da bango, sai ta cigaba

"Dama ance tsintacciyar mage bata mage, ka bani kunya,kuma na tabbatar kai ba dan halak bane dan baka san halacci ba, shiyasa su kansu iyayen naka suka wofintar da rayuwar ka, tir da hali irin naka na manta Alkhair."

Runtse idon sa yayi, yana ji ta cigaba da jifan sa da munanan kalaman da zuciyar sa ta gaja dauka.

***Sakin labulen tayi a hankali ta fito falon ta zauna a k'asa, da sauri Muhammad ya dube ta, yace

"Ta samu baccin?"

Daga masa kai tayi, idanun ta da yayi ja sosai yabi da kallo sannan ya mike

"Bari naje chemist din Bala na samo mata ko paracetamol ne."

"Ok." Tace tana zagba tagumi, fita yayi ita kuma ta koma ciki ta duba ta sannan ta fito ta had'a charcoal ta dora ruwa, ta dawo ciki ta zauna tana duba lokaci. Dogon bacci tayi sosai da ta jima bata yi irin sa ba, har akayi magriba akayi Isha'i sannan ta farka, tayi sallolin da suka tsere mata sannan tasha magani bayan ta d'an taba shinkafa da waken da Aysha ta dafa musu. Suka d'an taba hira ta koma cikin daki ta bar Muhammad yana kara ma Ayshan karatun wani littafin addini.
   Zagaye dakin ta hau yi tana tariyo abinda ya faru dazu da ta fita kasuwa, tabbas idan har ba gizo idonta yake mata ba toh tabbas shine, dan ba zata taba mantawa da fuskar sa ba duk kuwa da shekarun da aka dauka da kuma nad'in dake lullube a saman kansa.
   Tasan idan har ya tabbata ya ganta toh tabbas ya biyo bayan ta, kuma yaga gidan da take,ya zamar mata dole ta yi abinda ya kamata kafin komai ya lalace.
   Sak'a abinda ya kamata tayi ta kwana tanayi, Idan ta lalubo wannan hanyar sai taga ba me bullewa bace dan mutanen nan sun wuce duk inda hasashen me hasashe ya kai, idan tace zata gudu dole ne zasu san in da take tun da tasan ba zasu taba barin ta ba tun da suka gano tana raye bayan rufe babin ta da take tunanin sunyi da suka samu labarin hatsarin da ya auko ranar, wanda ba dan mutum daya a duniya ba da tuni tasan rayuwar ta, ta kare daga ita har yayanta. Shine ya taimaka mata ya karbe ta a mawuyacin halin da take ciki, duk da a lokacin ashe shima da nashi kudurin a kanta sai dai hakan be dame ta, tun da ya taimaka mata ya tseratar da ita daga mummunan hannu. Tunawa da tayi dashi duk da dama bata manta dashi ba ko da na sakan daya ne saboda abinda yake a tsakanin su da ba zai taba barin ta mantawa dashi din ba, tsawon lokacin nan tasan in da yake, amma bata taba neman sa ba, sai yanzu da wani tunani ya d'arsu a zuciyar ta, taji tilas tana bukatar ganin sa, ta kuma nemi taimakon sa a karo na biyu.
  Yadda taga rana haaka taga dare bata ko runtsa ba sai tsawon da taga daren yayi mata ma, anan kiran assalatu ta fito tayi alwala ta koma tayi Raka'atanul Fajr, tana zaune tana Addua tana jiran a kira Sallah Aysha ta tashi, alwalar tayi itama tazo sukayi sallar. Basu suka tashi daga wajen sallar ba sai da gari yayi sha. Shiryawa ta soma yi a gaggauce saboda yana yin gidan nasu da yadda layin bandaki yake, sannan ta saka Aysha ma ta shirya suka sha Koko suka fita. Napep suka hau har unguwar, a daidai kofar wani tangameman gida suka tsaya Aysha ta daga kai tana karewa gidan kallo, katon gaske ne iya ganin mutum, a hankali gate din gidan ya shiga budewa, wata bakar mota kirar Hyundai ta fito da mugun guda har ta kusa bige Aysha, da sauri Ammi tasa hannu ta finciko ta, tabi motar da kallo tana kisissima abu a ranta, girgiza kai tayi bayan kurar da ya bad'e su da ita ta lafa ta ja hannun Ayshan suka nufi gate din, suka kwakwasa a hankali, ta jikin har yar bular dake jikin gate din me gadin ya leko.

"Wa kuke nema?" Yace yana musu kallon tsaf

"Maigidan muka zo gani."

"Maigidan fa? Kun sanshi ne? Kuma yasan da zuwan ku ko Yaya?"

"Be san da zuwan mu ba, kace masa Safiyya ce kawai."

Shiru yayi yana tunanin yaje ko kar yaje, dan yasan halin Alhaji sarai a irin wannan abun sai ya jawo ya kore shi ma daga aikin, sake kallon su yayi yaaga dai basuyi kama da almajirai ba sai dai talakawa ne kana kallon su, sai ya saki kofar ya tafi cikin gidan yana addu'ar Allah yasa kar a samu matsala.
  Tsawon mintuna goma sai gashi ya dawo, hannun sa da d'an karamin complementary card ya mika mata

"Yace ki sameshi a nan." Ya juya ciki

Juya katin Ammi tayi, ba haka taso ba dan tana bukatar ganin sa yanzu yanzu, kafin lokaci ya kure mata, kafin abinda take tsoro ya faru, hannun Ayshan ta sake ja da sauri suka bar kofar gidan, zuciyar ta fal zulumin abinda zai je yazo.  *_Abinda Ke Cikin Zuciya_*

*_Hafsat Rano_*

Page 19

www.instagram.com/zeeherbalsaphrodisiac.

_*ASSALAMU ALAIKUM SISTERS..!_*

_*INA MASU NEMAN INDA ZASU SAMU INGANTATTUN: _*
_*HERBALS APHRODISIACS MA’ANA NA GARGAJIYA BANA HADIN BATURE BA MAI SIDE EFFECT..?_*

_*TO KU MATSO, DOMIN NESA TAZO KUSA.._*

_*ZEE HERBALS APHRODISIAC_*
_*ZEE HERBALS APHRODISIAC_*
_*ZEE HERBALS APHRODISIAC_*

_*MUNZO MUKU DA INGATTTUN KAYAYYAKI WANDA ZASU GYARA KI CIKI DA WAJE_*

_*MUNADA SUPPLEMENT MASU GYARAN JIKI DANA FATA, WANDA ZASA SAKI KIYI SHEKI FATAR KI TAYI LAUSHI. TAYI LUWAI LUWAI TAMKAR TA JARIRAI_*

_*AKWAI SUPPLEMENT NA KAYAN MATA WANDA ZASU GYARA KI, KIJI KI TAMKAR BUDURWA, SUPPLEMENTS DINMU BASU DA SIDE EFFECT, DOMIN AN HADO SU NE DAGA INGATTATTUN ITATUWA, WATO NATURAL PRODUCTS NE ACIKI._*

_*KAI BA ANAN KADAI MUKA TSAYA BA, MUNA DA INGATTUN KAYAYYAKIN MATA WANDA KESA KISHIYA KWAFA, WANDA DUK INDA SARAUNIYA TAKAI KIN WUCE, WANDA ZASU TSATSO MIKI MARTABAR KI DA KIMAR KI_*

_*AKWAI INGATTATTUN MAGUNGUNA, NA CUTUTTUKAN DA SUKA SHAFI DAN ADAM DAMA JINNU.. KAI DAMA WANDA BAMU AMBATA BA.. ZEE HERBALS APHRODISIAC (MASARAUTAR INGATTATTUN MAGUNGUNA KENAN)_*

_*KYAU, ARHA, INGANCI, RAHUSA... SAI ZEE HERBALS APHRODISIAC_*

_*MANHAJOJIN MU NA SOCIAL MEDIA: KAMAR INSTAGRAM DA WHATSAPP DAMA NAMBAR TARHON MU: DOMIN SHIIGA KUGA IRIN KAYAYYAKIN MU TUNTUBE MU TA_*

_INSTAGRAM LINK DIN MU:_

www.instagram.com/zeeherbalsaphrodisiac

_WHATSAPP LINK DIN MU:_
https://Zeeherbalsaphrodisiac.whats.bz

_NAMBAR TARHON MU_
08169380189

_*DA A BAKA LABARI GWARA KA BAYAR.. KIZO A DAMA DAKE YAR UWA, KI ZAMO DAYA DAGA CIKIN KASAITATTUN MATA MASU AJI.. MUNA GARIN KATSINA, SANNAN KAYAN MU MUNA BADA SU AKAN FARASHIN SAYA ‘DAI DAI KO SARI.. MUNA TURA KAYAN MU A KO’INA A FADIN NAJERIYA._*

_*BE YOUR OWN BOSS, BUILD YOUR OWN EMPIRE, BE THE WHOLE WORLD OF HIS MAJESTY( YOUR HUBBY) BE THE ONLY CENTER OF ATTRACTION WITH ZEE HERBALS APHRODISIAC. OUR PRODUCTS LASTS LONGER AND VERY EFFECTIVE. NO SIDE EFFECTS. AVAILABLE N WHOLESALE/ RETAILS.. DELIVERY IS NATIONWIDE. 100% TESTED AND TRUSTED_*

****

Tun da ya tashi yau yake jin sa babu dadi, kamar zai samu attack musamman yadda garin yake da alamun hadari, mafiya yawan lokuta a irin wannan yanayin asthma tafi tasar masa shiyasa ma daya ga yanayin garin na yau kamar akwai kura kura ma sai yayi zaman sa a daki, be san me yake faruwa ba har zuwa sanda hadarin ya taso, ya tashi da sauri ya rurrufe windows ya sassauke labulayen ya koma ya zauna still yana jin sa kamar mara lafiya. Yana zaune yaji an saka hannu an taba kofar, ya kalli kofar kadan sannan ya tashi yaje ya bud'e, tana tsaye idonta na fitar da hawaye me zafi, zafin maganganun da Mah-Mah ta gama fad'a ma Sultan ba tare da tayi la'akari da ita dake tsaye a wajen ba, ta gama tayi shigewar ta ciki lokacin har yayyafi ya dan fara kad'an kad'an.  Da sauri cikin tashin yace

"Subhanallahi,Me yake faruwa? Wani ne bashi da lafiya?"

Girgiza mas kai tayi, karo na farko da taji ya bata tausaya saboda yadda ya rikice har yana hada kalmomin wajen fad'a, gefe ya matsa mata ta shiga cikin dakin, sannan ta zame a hankali ta tsuguna a k'asa tana cigaba da kukan,

"Dan Allah, na roke ka da Allah free me, ka taimake ni dan Allah karka bari ayi auren nan, wallahi bana son ka da sigar soyayya, ban taba son ka ba kuma bazan taba son ka ba, idan ma na aure ka toh wallahi zuciya ta ba zata taba kasancewa da kai ba, ta yaya kake tunanin zan iya yi maka biyayyar aure bayan bana son ka ko da kadan ne?"
Chapter 39 · 0% Book details