← Book details Abinda Ke Cikin Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 79 OF 108

Sashe 79

Abinda Ke Cikin Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Safwan!" Ya kira sunan shi ganin yana kokarin bude idonsa,daina motsawa yayi ya tsaya chak, sai kuma yayi wani nishi me karfi sannan ya bud'e idon ya dora su akan Sultan dake tsaye a gaban sa a rikice ya shiga kokarin had'a magana, maganar da ke fitowa daga chan k'asan mokoshin sa,

"Karka yi magana, karka ce komai." Ya rik'e hannun sa kakam ya shiga duba shi yana son tabbatar da komai daidai.

"Sultan, Nagode, Nagode sosai da duk kulawar ka gareni, kayi dawainiya dani tun muna yara har yanzu baka daina ba..."

"Shissh, ka daina magana kana hurting kanka, baka bukatar yin magana kayi shiru dan Allah."

"Dan Allah ka barni na ce wani abu."

"Ba zaka sake magana ba, sai na baka dama." Yace yana cigaba da duba shi

Shigowa duk sukayi, Mah-Mah ta karaso da sauri tana kuka

"Safwan, sannu kaji, sannu." Ta rike hannun sa tana kuka sosai, kukan yadda ya zama a cikin kwana daya kachal

"Mah-Mah...." Yayi mata murmushi kad'an wanda ya tsaya iya kan lips din sa kawai

"Na'am, nice Safwan, sannu Allah ya baka lafiya."

Matsawa baya sultan yayi, ya saka bayan hannun sa ya goge fuskar sa. Dr ne suka shigo da sauri, Dr Labaran ya fara fad'an shigowar da sukayi dukkan su, babu kuma wanda yaje ya kirasu da ya farfado, fita duk sukayi aka bar Sultan da ya rike hannun Safwan din.

Duddubawa suka sakeyi Sultan na kallon su, sun dad'e suna tsaye a kansa suna bincike,kafin Dr Labaran ya fita ya bar Dr Osas da wani Dr Bashir suna cigaba da duba shi. Dr Labaran na fita Safwan din ya fara tari sosai, tarin da ya saka Sultan mikewa tsaye yana mamaki da tsoron abinda ya kawo tarin, sosai tarin ya cigaba da karuwa wanda ya saka su Dr Osas a cikin tashin hankali suka rufa akansa, aman jini ya fara sosai kamar zai amayar da kayan cikin sa, rik'e shi sultan yayi tsoro na shigar sa, idon sa yayi masifar kad'awa yayi wani irin ja, jijiyoyin kansa duk sun fito radau suna harba jini da sauri sauri, kokarin tsaidawa Safwan tarin suke sai dai abin nasa kamar ma gaba gaba yake yi.
   Kamar wasa sai ga wasu manyan Dr hadda su Dr Ahmad duk sun zo, su wajen bakwai akan sa hadda Sulthan duk da shi babu abinda yake yi babu kuma abinda yake aikatawa sai bin su da ido kawai yake kamar ma be san abinda yake faruwa ba, ko kuma shima ya samu wata babbar matsalar a kansa dan ko juya kan baya iyayi saboda yadda yake masa ciwo.
   Sun yi iyakar kokarin su da zasu iya, sun yi duk yadda suke tunani da hasashe,amma babu wanda ya iya da abinda Allah ya hukunta. A hankali gabobin jikin sa suka dinga saki har suka saki gaba daya suka tsaya chak suka daina aiki gaba d'aya.

Sai a lokacin Sultan ya samu wani karfi, ya ture Dr Ibrahim yayi kan Safwan din

"Safwan! Safwan! Ka tashi dan Allah, karka yi min haka, ba zan iya dauka ba ,zuciya ta ba zata iya dauka ba, dan Allah kar muyi haka da kai ka tashi."

Rike shi dr Labaran yayi yana kokarin kwacewa ya saka karfi sosai ya matse shi yana son fad'a masa magana amma yaki sauraran sa, kokari suke dukkan su ya sauraresu amma gaba daya jin sa da ganin sa sun dauke, sai gashi zai zube sukayi saurin tallafar sa aka dora shi a dayan gadon suka shiga bashi taimakon gaggawa.

ZAFAFA BIYAR
NA KUDI NE:::

Duka BIYAR 5 zaku samesu akan garabasar naira 700 kacal,

Guda hudu 4 Kuma 500,

Guda uku 3 Kuma 450,

Guda biyu 2 Kuma 400,

Guda daya akan 300.

Ma'ana
Each one is 300
2 is 400
3 is 450
4 is 500
5 is 700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO- *0812652655*
ACCOUNT NAME- *HAFSAT LAWAN GAMBO*
BANK NAME: *ACCESS BANK*

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

*+234 903 234 5899*

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

*09033181070*

Karku Bari ayi Babu ku domin wannnan salon na daban ne
SABUWAR SHEKARA
SABON SALO

TEAM#ZAFAFABIYAR🔥©Hafsat Rano
38-40

ZAFAFA BIYAR NA KUDI NE!!!

_INA MA’ABOTA KARATUN LITTATTAFAN HAUSA? WANDA ZAI NISHADANTAR DAKU, YA FADAKAR, YA KUMA TSUNDUMA KU A KOGIN LOBAYYAR KAUNA? TO KU MATSO KUSA... DOMIN MUNZO MUKU DA ALBISHIR DIN WANI GANGARIYAR LITTAFI.. DAYA NE TAMKAR DA DUBU.. YAZO DA WANI SALO NA DABAN WANDA ZAI SANYAYA ZUKATAH.._

_LITTAFIN *UNCLE NE...* LITTAFI NE FIRST OF ITS KIND, DA YAZO A WANNAN SHEKARA TA 2021. AN BAJE KOLIN BASIRA A BOOK DIN UNCLE NE.._

_”Wait... Dakata hafsat Rano, Kina nufin NIMCYLUV, dai shararriyar murubuciyar nan itace tazo da wani salon rubutun..?..”_

_”Kede bari Billyn Abdul.. Tsaya kiji kanun labarin a tak’aice..*NIMCYLUV* Tace book din a ta’kaice labarin *UNCLE NE* ne yana tafe:_

_Da farko yana mata kallon uwa wacce ta haife shi kuma jigon rayuwarsa, ashe itace silar rushewar rayuwarsa😢yarinyar da yakewa kallon ƙanwa uwa ɗaya Uba ɗaya ita aka wayi gari ta zama MATAR SA🙆🏻‍♀️ ƙaddara ta haɗashi da (Ahlil kitab) kiristan ya bata farin ciki, kulawa, soyayya, harya samu ta musulunta, Dalilinta sbd al'ƙawarin aure da yyi mata,ashe ba sonta yake ba🤔yaje birnin NUFAR domin kai masu tayin Muslunci, sun amince da hakan amma sharaɗin dole ya kwanta da ƴarsu,🤦🏼‍♀️gashi bashi da cikakkiyar lfy mazantakarsa bata aiki😫 ashe mahaukaciya ce ta haife shi.._

“_Kai lalle akwai runguntsumi acikin wannan littafi..  Ba za’ayi babu ni ba, Domin Za’a sha lagwadar romon dadi. shin tayaya ake biya Hansatu?_”

_”Ai ta Abdul..LITTAFIN *UNCLE NE* Naira 300 ne, Idan kuma kana son vip inda za'a ake posting sau biyu a rana kuma za'a baku littafan data rubuta na kuɗi sai ka bada 600 mai ma kon 1k.. number asusu wato bank account details: 0116886423 : account name sulaiman Na’ima S. Bank name: unioun bank: Sai a tura shedar biya ta 08119237616... A nuna mata ƙauna ta hanyar turowa ta account🤲🏻kamar yadda Za’a  faranta maku a littafin UNCLE NE_
_(Best romantic love story of the year//Had’adden labarin kauna na shekarar 2021)_

***Mikewa Mah-Mah tayi zumbur, tayi hanyar dakin, Daddy ne yayi saurin rike ta, ya girgiza mata kai cike da tausayin halin da take ciki, yasan tana son Safwan son da bata taba yiwa wani irin sa ba, ya kuma san yadda take fama duk lokacin da wani abu ya samu Safwan din, shiyasa ma yanxu da Safwan din yake a halin da babu wanda zai iya fad'an me zai faru, ya ke tausayin ta sosai, irin tausayin da yaji a wasu lokuta da suka sude a lokacin da basu samu haihuwa ba.

"Dan Allah ki kwantar da hankalin ki, ki barsu suyi aikin su, mu cigaba da addu'a in Sha Allah zai samu sauki, kinga fa wajen su nawa ne a ciki, muyi addu'a kawai."

Komawa tayi ta zauna amma ta kasa tsaida kukan da take, kukan da duk wata uwa da danta ya samu kansa a irin wannan tashin hankalin zatayi.

Farkawar Amrah ya saka duk suka tafi dakin, taimaka mata Umma tayi ta zauna ta jingina da pillow. Kowa yayi mata sannu, Mah-Mah tana dubata da koma chan dakin da Safwan yake ta zauna ta barsu, tana zama yan uwanta mata suka zo suma suka zauna tare duk akayi jigum ana jiran tsammani.
   Dadewar likitocin a ciki ya kara tashar da hankulan su, kowa ka gani addu'a ce a dauke a bakin sa. Da gudu Dr Bash ya fito, suka tashi gaba daya sukayi wajen sa

"Dr ya Ake ciki dan Allah?"

"Sai dai kuyi hakuri." Yace musu ya wuce da sauri, ya dauka wa Dr Ahmad abu ya dawo ya wuce su ya shiga ciki.

Rik'e Mah-Mah akayi da wani mugun jiri ya kwashe ta, saura kadan ta fadi a wajen Allah ya taimaka suka rik'e ta,

"Innalillahi wa Inna ilaihi rajiun, Innalillahi wa Inna ilaihi rajiun,kulli nafsin za'ikatil ma'aut!" Sai tayi shiru bata sake cewa komai ba, kawai ta shiga bin yan uwan nata da ido da suke kuka amma ta kasa magana,

"Kiyi kuka Dan Allah, kiyi kuka ko zaki samu sauki, karki ce zaki kume dan Allah kiyi kuka."

"Anya da gaske suke?" Tace tana kallon ta

Sai kuma ta dafe kanta

"Sai dai kuyi hakuri, kenan ya mutu, haka likitan nan yake nufi ko?"

Ta sake tambaya tana kallon su, tausayinta ya saka kowa har wadanda suke kusa da wurin zubda hawaye, sai kawai ta dinga juya kanta da sauri da sauri tana girgiza shi

"Be kamata ya mutu ba, Safwan ya sha wahala, gaba daya rayuwar sa a jinya ya yi ta, tun haihuwar sa kawo yanzu be ji wani dadi ba, kullum a wahala yake, ya kamata ace shima yayi rayuwa irin ta kowa.... Be kamata ya mutu ba..." Da sauri Anty Farida ta rufe mata Baki

"Dan Allah kiyi shiru, karki yi sabo, zafin mutuwa ba zai saka kiyi Sabo ba, Allah ne ya halicci Safwan, ya dora masa jinya ba wai don Baya son sa ba, a ah sai dan Ya gwada karfin imanin sa da namu, yanzu kuma da ya karbi abin sa, bamu da hurumin tambayar dan me? Domin Shi yafi mu sansa."

"Nayi shiru, nayi shiru." Ta Shiga fad'a tana girgiza kanta

"Astg...." Ta dinga maimaita

Sai a sannan kuka ya zo mata, ta durkusa a wajen ta shiga yin sa a hankali ba tare da daga murya ko ihu ba.

***Duk sun dukufa akan Sultan da ya ke kokarin shiga mugun hali, suna bashi tallafin da zasu iya. Dr Ahmad ne kad'ai akan Safwan wanda yake kokarin ganin ya tabbatar da zargin sa. Da sauri ya matso da ventilator machine ya had'a ya saka masa yana kokarin ganin ya daidai ta respiratory failure da ya samu dazun, kamar an fisgo numfashin haka ya dawo da karfi har sai da ya fitar da kara, sai kuma ya shiga fitar dashi da dan sauri da taimakon Allah da taimakon Machine din. A hankali ya fara daidaita har ya dawo daidai, sai dai har lokacin babu wani abu a jikin Safwan din daya motsa sai wannan numfashin da ya samu nasarar dawowa.
Chapter 79 · 0% Book details