← Book details Abinda Ke Cikin Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 108

Sashe 4

Abinda Ke Cikin Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta fito tsakar gidan kenan tana kwashe shanyar da tayi ya shigo, da sauri ya karba ya karasa ya bi bayan ta suka shiga ciki suna tsokanar juna, ruwa ya dauko a fridge yasha ya koma ya zauna yana maida hankalin sa kan ta sosai ya ce

"Hajjaju me ran karfe wajen ki nazo fa."

"Ja'iri ai nasan ba takanas dan ka gaishe ni kazo ba, ko da yake kafi dayan dan uwan naka mara kirki."

"Wanne dan-uwan nawa a ciki?" Yace yana dariya

"Wanene idan ba adunanu ba? Ja'iri jiya ya kira ya gama kare min tanadi, harda wai ya sami baturiya ba shi ba dawowa."

"Kai be kyauta ba, ni ai ba haka nake ba." Yace yana guntse dariyar sa

"Kaji dashi, Muhammadu ne kawai na kirki a cikin ku, ko jiya sai da ya biyo ya bani man ciwon kafa."

"Allah sarki ai da tare fa zamuzo, sai kuma Allah be yi ba."

"Kanka akeji, kace waje na kazo, ya akayi?"

Zamowa yayi ya zauna a kasa ya sosa kansa yayi murmushi

"Dama... Dama kamun kafa nazo hajiyar mu."

"Na sani ai, ja'iri."

"Allah Hajiya, kin ga gida be koshi ba ai ba za'a bawa dawa ba."

Washe vaki tayi cikin gamsuwa tace

"Amratu ce ko afiruwar?"

Shafa kansa yayi

"Amrah ce hajiya."

"Toh Masha Allah, wannan abu yayi min d'adi sosai, kaga dama na matsu ya tattaro su ya dawo dasu nan, dan idan suka cigaba da zama dasu a chan wa zai gansu har yace yana so? Ga ka yanzu hankali na sai ya kwanta,saura itama Afran Allah ya kawo mata nata, duk sai mu hada ku rana daya musha biki."

"Allah yayi muku Albarka."

Amin yace yana jin a ransa kamar yace Sultan kuma Afrah, idan yaso sai asha bikin rana daya, amintar su sai ta kara kulluwa gashi sun auri yan gida daya, har ya bar gidan yana sakawa da kwancewa akan yadda zai bullo wa Sultan akan maganar Afrah dan baya so maganar sa tayi karfi ba tare da ta Sultan din ba.
   Yana xuwa gida ya tarar dashi ya dawo,yana cin abinci hannun sa dunkule da wani abu, be bada muhimmanci akai ba ya zauna suka karasa cin abincin sai dai ya kasa bashi labarin kamar yadda yayi niyya, ji yayi ba zai fad'a masa ba sai dai yayi suprising nasa sanda zasu zo Kano dan Hajiya tace da sun gama secondary school zasu zo gida za kuma su dan dade, a lokacin xai bayyanawa kowa, kafin nan kuma zai ta nunawa Sultan hotunan Afrah ko Allah zai sa a dace shikenan burin sa ya cika.
     Fitar Safwan ya bawa Sultan damar bude bracelet din hannun sa, shafa shi yayi ya saki murmushi me kayatarwa

"Allah ka taimake ni, ka tsare min zuciyar ta, har zuwa lokacin da zan bude na shigar da soyayyar ta a ciki na sa mukulli na rufe ruf ba tare da ta samu space din kowa ba komai kankatar sa."

"Amin." Ya amsa da kansa sannan ya maida shi cikin dan box din da yayi masa musamman domin ajiye shi ya daga kasan kayan sa ya saka shi.

***Da safe suna chan bayan gidan Sultan na motsa jiki, Safwan na zaune a saman kujera yana chatting ya bada hankalin sa sosai akai har Sultan yayi masa magana be ji ba, tasowa yayi ya fisge wayar yana hararar sa

"Ohhh! Ina kokarin samo kan wata beb ne wallahi, sorry me kace?."

"Aikin kenan, Allah ya shirye ka kai da Adnan shegen ruwan ido."

"Kaga kuma hoton ka na tura mata wallahi, har kuma tayi falling ganin ka rataye da stethoscope tasan guy din hot ne."

"What? Wallahi amma kai ko? Toh ni an bada ni ma dan kaji."

Yace yana balle murfin ruwa ya kafa kansa yasha sosai sannan ya kalli Safwan da yake ta faman masa dariya

"Ha'a...What's funny kuma?"

"Kai mana, ji yadda ka wani ce an bada kai, ko uban waye ya bada kai? Tsaya ma... Aina ake bada namiji ne a garin nan? Idan ma hakan ne ai ni zan bada kai."

"Madallah." Yace yana gid'a kansa

"Bani wayata toh, naji reply dinta."

"Kasha maganin ka?" Ya bata rai ya ki basa wayar

"Na shiga uku ni wai kamar wani karamin yaro sai ance nasha magani ko ban sha ba? Katon magidanci dani haba, idan beb dita taji ai sai ta raina ni wallahi."

"Baka son wayar ka kenan, kasha ko baka sha ba?" Yace yana sosa saman girar sa

"Nasha wallahi."

"Good." Sannan ya bashi wayar shi kuma ya shiga ciki domin gyara jikin sa.

Wannan shine irin soyayyar dake tsakanin Sultan da Safwan, soyayyar tsakani da Allah da babu komai a cikin ta sai tausayi da girmawa a tsakanin su.

Karbar wayar Safwan yayi ya cigaba da yiwa Adnan magiya ya sake turo masa wasu pictures din, sai da ya gama wanashi sannan ya turo masa wasu da sukayi a wani eatery tana murmushi hankalin ta na kallon wani abu chan da be san menene ba, sai ya zuba mata idanuwa yayi ta kallon ta kamar ya samu tv,wunin ranar da hotunan yayi su, yana jin duk wata damuwa da matsalar sa na fita kadan kadan, yana jin sa so strong da yake son rayuwar sa tayi tsayin da zai nuna mata tsantsar soyayya cike da kulawa. Adah ya kan yi tunanin yadda kullum idan ciwon sa ya tashi kowa yake kawo masa mutuwa saboda masu irin matsalar sa ana musu kallon basu da rayuwa me tsawo, duk da haka be taba rok'ar Allah ya bashi tsawon rai ba sai yanzu da yake jin yadda soyayyar ta, take bin kowanne kusurwar gangar jikin sa tana maye gurbin duk guraben da suka bude saboda nauyin ciwon da yake dauke dashi.
   Kasa bacci yayi daren ranar ya dukufa rokon Allah ya ara damar da zai nuna mata gata ya maida ita sarauniya a fadar zuciyar sa.

***
Gida ne babba da ya zama islamiyyar tasu, wata baiwar Allah ce da suke kira da Aunty Muhsina yar asalin kasar Saudiyya da tayi karatun ta tun daga matakin primary har zuwa degree a bangaren addinin islama ta bude makarantar bayan dawowar ta kasar, hakan ba karamin taimaka wa musulmai mazauna garin yayi ba, sosai suke karatun su na addini tamkar suna gida, su Amrah sun yi nisa sosai a karatun nasu dan sun gama littattafai da yawa Qur'ani kuwa sun sauke shi har sun fara hadda, zaman su a kasar masu jajayen kunnen be sasu sun bar dabi'ar su ta Hausa Fulani ba, Umma a tsaye take akan su, haka ma Abba baya yarda da shigar banza suna kokari sosai wajen ganin sun kula da tarbiyyar su. Afrah ce ma me rawar kai, shiyasa ma iyayen suka fi saka mata Ido sosai domin su turawan babu ruwan su, balle yadda suke kyawawa dasu TubarkAllah Masha Allah.
     Sha biyu suke tashi daga islamiyyar tasu sai kuma gobe Idan asabar ce idan lahadi ne kuma shikenan sai wani satin, da yake babu nisa tsakanin su da gidan a kafa suke takawa.
   A kitchen suka tarar da Umma tana shiryen shiryen lunch, jakar su kawai suka ajiye suka sameta a kitchen din, suna aikin suna hira har suka kammala sannan suka tafi yin sallar azahar ganin lokacin yayi.
      Yan matan umman kyawawa ne na karshe, abin ka da Fulani da suke da kyau me sanyi, skin colour din su ba fari bane kal, ya dan sirka da duhu kadan sai suka kara yin wani irin kyau me sanyi da sai ka zauna dasu zaka kara ganin sa, musamman Amrah da take da manyan idanuwa farare tas, da dan madaidacin baki da dimple a both side din kumatun ta wanda ko bata yi magana ba in dai ta motsa fuskar sai sun loba saboda girman su.
   Tafi Afrah tsayi da kadan sannan ta fita cika, duk da ba wasu manyan yanmata bane amma sun yi saurin girma sosai, jikin su ya murje kallo daya zakayi musu ka tabbatar da tsantsar hutu da gayu sun samu matsuguni a jikin nasu.

****
Dukkanin fitar numfashin shi na fita ne da soyayyar ta, haka ma duk wani abu yanayin sa ne da ita a makale a zuciyar sa, tsawon shekarun nan be taba tashi ba tare da ya tuna ta ba, sai dai bashi da sukuni sanin cewa shi kadai yake kidan sa yake kuma rawar sa,Idan ya tuna sai duk tunanin sa ya kulle ya kasa katabus. Ya rasa irin son da yake mata, tun tana zanin goyon ta, tun ranar data fara zuwa duniyar nan, tun be san me yake ji akan ta ba, tun shi kansa be gama sanin shi din waye shi ba, me yake so mene baya so, be gane irin tasa kalar soyayyar ba sai da ya mallaki hankalin kansa, sannan ya tantance irin soyayyar da yake mata, yake kuma jin tsoron abinda zai biyo baya idan har ta zabi wani bashi ba.
    Ranar da ya ga hotunan su a status din Adnan, be runtsa ba ko kadan, yana tunanin yadda zata karbe shi. Zuciyar sa takan yi zafi idan ya tuna waye shi, maraya wanda bashi da UWA balle UBA bare azo maganar dangi, ya sani a aure nasaba na da matukar muhimmanci, toh shi be san kowa nasa ba ma bare azo maganar ma baki daya. Tunanin sa yakan katse idan ya tuna zai iya yiwuwa ma ba ta hanyar aure aka sameshi ba, da sauri yake neman tsari da haka duk sanda tunanin ya gifta ta kansa.
   Idan kuma ya tuna Daddy da Mahmah da gatan da sukayi wa rayuwar sa, sai yaji ya samu kwarin guiwar da zai nemi soyayyar ta, su kuma tsaya masa kamar yadda xasu tsayawa Safwan.

Wannan kenan!
Chapter 4 · 0% Book details