Sashe 53
Abinda Ke Cikin Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Me?" Yace getting more closer than before, sai ta hau stammaring. Hannu yasa ya sakalo waist dinta ya yi hugging dinta firmly. Mutsu-mutsu ta fara ya sake riketa kam yana manna hancin sa akan fuskar ta. Runtse idon ta tayi sanda taji saukar bakin sa a saman kanta, sannan yayi kissing saman idon ta, da both side na cheeks dinta.
"Matsoraciya." Yace yana sakin ta, kamar zata fadi sai kuma ta tsaya tana jin kamar ta nutse saboda kunya.
***Da wani irin yanayi ta shiga bud'e idonta, a hankali har idon nata ya gama budewa tas ta kuma fuskanci a inda take duk da duhun da ya mamaye dakin, ta san wajen tun tsawon lokaci kuma babu abinda ya chanja sai ma kara tsufa da wajen yayi. Dakin horo kamar yadda mutanen Masarautar ke kiran sa dashi, dakuna ne na kara kananan gaske, sai dan karamin makewayi a cikin kowanne, shekarun baya ta taba kasancewa a cikin wajen sai gashi yau ma ta sake dawowa ciki. Sai dai wannan zaman yasha banban da wanchan.
Bata san tsawon kwanakin data dauka a wajen ba, daga ruwa babu wani abu da ta saka a cikin ta, ba wai dan ba'a batan ba, sai dan bata jin akwai sauran kalar makircin da bata sani ba.
Ta galabaita sosai tana kwance lamo a k'asa taji takun tafiyar mutane da maganganu k'asa k'asa, kafin ta gama tantance muryoyin nasu aka budo kofar aka shigo, da k'yar ta cire kanta ta kalle su, ta maida kanta k'asan tana jin wani irin tsanar su na sake karuwa a zuciyar ta.
"Kin dauka zaki iya tsere mana?" Daya ya tambaya yana fashewa da dariya.
"Idan har kin yi tunanin bamu san inda kike ba tsawon lokacin nan yasa bamu neme ki ba toh kinyi karya, mun barki ne zuwa lokacin da ya dace."
Bata ce kala ba, tayi shiru tana jin su har suka gama suka fita.
"Allah kana kallo, karka bawa wandannan azzaluman nasara."
***A matukar firgice ya tashi, yana lalubar glasses din idon sa, hannun sa ya sauka akan wani abu kamar kwalba, yayi yar kara kad'an ya tashi sosai sannan ya kunna bed side lamp. Babu komai a dakin da zai nuna wani abu ya faru kamar yadda ya gani a mafarkin sa. Kasa komawa baccin yayi har gari ya waye sosai, hadiman sa ne suka shiga kaiwa da komowa a bangaren har komai ya daidaita kamar yadda aka saba kullum. Suna zama a fad'a mutumin ranar ya sake dawowa, wannan karon a dan rikice yake fiye da ranar. Umarni aka bawa kowa ya fice ya rage daga shi sai Maimartaba Sarki Bello Moddibo Saji, faduwa yayi k'asa jikin sa na rawa yace
"Allah ya baka yawan rai ranka ya dad'e, abinda yake tunkaro mu babba ne wannan karon. Shukar da sukayi tayi yad'o har ta fitar da amfani, amfanin dake neman zamar mana matsala a yanzu."
Sai ya sauke kayan hannun sa, ya fito da mudubin ranar, wannan karon danjoji guda uku ne masu matukar haske suke tunkaro su sannan sun fitar da shape kamar triangle daya a sama, sai da Sarkin ya d'an zabura har ya kusa direwa daga kujerar sa sai kuma ya daidaita yana duban sa.
"Ya akayi haka ta faru? Bayan mun samu TABBACIN hakan ba zata faru ba, bayan babu sauran abinda muka bari da bamu rufe ba, toh ina matsalar take? Waye ya ha'ince mu? Waye yaci amanar mu da muka kasa sani sai yanzu da komai yake shirin karewa? Waye wannan!"
"Ranka ya dad'e!"
"Kafin faduwar rana, ina so kazo min da bayanin wanda yaci amanar mu, ka nemo shi ko waye."
"An gama ranka ya dad'e." Yace da sauri yana tattare komai.
Yana fita Sarki ya bada umarnin yau babu zaman fada. Kowa yayi mamaki dan hakan bata taba faruwa ba.
Manage please©® Hafsat Rano
Page 25
Wannan littafin na kudi ne, AMANA CE, duk wanda yayi mana sharing dinsa shi da ALLAH! Idan kina/Kana so ki/ka karanta ki/ka tuntubi numbobin nan*
*0903 234 5899*
Or
*09033181070
*
Kafin faduwar ranar kamar yadda ya bashi umarni, ya dawo da labarin da ya firgitashi ainun. Faduwa yayi kamar ko yaushe yayi gaisuwa, sannan cikin tsantsar biyyyar ya soma bayani.
"Akwai gagarumar matsala ranka ya dad'e, akwai shiri me girma akan zoben nan, wanda idan aka yi wasa zai koma hannun da ya fito ba tare da shi hannun yasan da hakan ba."
"Kamar ya?"
"Zai shigo masarautar nan bisa umarnin Madaki, zai kuma dauki zoben nan, sannan zai damka shi a hannun Madakim, wanda idan har hakan ta kasance, komai ya lalace,komai ya baci."
"Babu wanda yake da ikon kai hannu akan zoben nan face shi d'in tsatso ne daga tsatson wannan ahalin, waye wannan da zai shigo Masarautar nan har ya iya daukar zoben?"
"Allah ya baka yawan rai, shine abu na karshe da muka kasa gani, muka kasa samun amsar sa, abu daya muka sani shine ranar jummah me zuwa hakan zata kasance."
"Idan har mun fuskanci abinda kake so ka fad'a, kenan Madaki...?
"Be hakura ba tsawon wannan lokacin yana bibiyar duk ayyakun mu."
Gid'e kai Sarkin yayi cikin gamsuwa sannan yace
"Waye yake mana zagon k'asa?"
"Ayi min aikin Gafara ranka ya dad'e, ba kowa bane sai Yarima me jiran gado."
Tsaye ya mike, da sauri kamar idon sa zai fado k'asa, sai kuma yayi k'asa da kansa cikin tsananin mamaki, mamakin abinda yake shirin faruwa dashi, d'an cikin? Ko dai be gani daidai bane? Amma kuma babu yadda za'a yi yayi wasa da aikin nan ko dan muhimmanci sa ga mutane masu dama.
"A kira sarkin kofa!"
Da gudu wani bafade ya fita, cikin kankanin lokaci ya dawo tare da wanda aka kira da Sarkin Kofa
"A tsaurara tsaro a kara matakan tsaro a kowacce kofar shigowa da fita daga Masarautar nan, sannan ya atabbatar babu wasu bakin fuska da zasu shigo ba tare da an tantance su ba, duk wanda yayi gardama ko ya nuna wani abu da baku yarda dashi ba, a aika shi garin da ba'a dawowa!"
Takawa ya shiga yi cikin tsananin bacin rai, ya juya ya shige ciki ya bar mutane da yawa da tunanin abinda ke faruwa ko yake shirin faruwa, babu wanda ya taba ganin sarkin a irin wannan yanayin.
**Tun da ya koma ciki sai ya k'asa zama, ya jawo akwatin karfen dake k'asan gadon sa ya bude ta, kayayyaki ne a ciki birjik masu muhimmanci a wajen sa, sai dai kaf ciki babu kamar barin zoben nan wanda zai iya cewa shine duk matakin nasarar sa. Yana nan a inda ya ajiye shi, ajiyar zuciya ya sauke da karfi ganin babu abinda ya sameshi, maidawa yayi ya rufe ruf ya tura ta ciki.
Kamar yadda ya tabbatar da shud'ewar mutane masu yawa a baya, haka zai tabbatar da shud'ewar duk wani abu da zai kawo masa cikas a cikin mulkin sa. Ko da kuwa kusancin sa ya kai kusanci dake tsakanin d'a da mahaifi ne.
A lokaci me tsawo, bayan shud'ewar wasu al'amura da suka zama wani sirri nasa, sirrin da duk amintar dake tsakanin su bata sa ya sanar dashi ba, sirrin da ya zama wani tsani na duk nasarar da ya samu. Sirrin Kasancewar sa Sarki a Babbar Masarautar irin Masarautar Saji. Sai dai yasan yayi abubuwa da yawan gaske kafin hakan ta kasance, wanda ya tabbata Idan har za'a koma baya, idan har za'a tariyo masa abubuwan da suka farun ba lallai ne ya iya yarda da gaske sai da ya yi irin wannan gwagwarmayar ba sannan komai ya kasance ba.
Ya tuna wani lokaci, suna zaune da shi, suna hira irin ta makusanta aminan juna, ya dauko masa zancen da yayi amfani wajen samun nasarar sa, yayi amfani da damar ya jefi tsuntsu biyu da dotse guda daya.
Dunkule hannun sa yayi ya daki iska dashi, ya ja iska zuwa hunhun sa, sannan ya fito da ita.
_"Bello... Ina so kasan ba ko yaushe ne rayuwa take tafiyar wa mutum a yadda yaso ba, sau da dama abubuwa na chanja salo da alkibla daga inda bakayi zato ko tsammani ba..."_
Kalaman da dan uwan sa ke yawan maimaita masa a wanchan lokacin, sai dai be taba daukar su da muhimmancin da har zai zauna yayi bitar su ba, amma a yanzu sai yaji yana bukatar sanin ma'anar su, musamman da yake hango wani gagarumin abu na tunkaro su. Ta Ina zai fara? Safiyya da aka tabbatar masa da wanzuwar ta a cikin Masarautar sa duk da har yanzu be je ya ganta ba, ko kuma Safiyanu Madaki dake shirin kawo masa cikas ta inda be yi zato ba. Idan kuma ya gangara kan matan nan guda biyu, da taurin kai ya hanasu amsa abinda yake nema a wajen su tsawon lokacin nan. Ta Ina zai fara ne? Yarima Bilal na masa zagon k'asa, d'an da ya haifa da cikin sa, yake ma so mara iyaka. A bangare daya kuma, hasken da ke tunkaro Masarautar tasa da ya gani da idon sa, wanda adah yake ganin su dishi dishi amma yau sai ya gansu da matukar haske, suna kuma da kusanci da shi a duk inda suke.
Gabatowar magriba yasa shi katse tunanin sa, ya fita zuwa masallacin dake cikin Masarautar suka gabatar da sallah.. Zaman sa yayi a cikin masallacin har sai da akayi Isha'i sannan ya koma shashen sa da rakiyar manyan makusanta sa. Sun yi tunanin zai zauna dasu akan abinda ke faruwa sai suka ga yayi shigewar sa ciki ya barsu da hangamemen baki cike da mamakin Sarkin.
A lokacin da kowanne bawa ke samu ya kwanta ya hutar da zuciya da gangar jikin sa, a lokacin ne su kuma suke cikin tsananin azabtuwa da kalolin azabobin da ake musu, duk da haka basu taba jin a ransu zasu mika wuya ba, basu taba jin zasu taba sanar dashi abinda yake son sanin ba.
Da sauri duk suka zube a k'asa, cikin kankan da kai suka shiga yi masa kirari, takawa yake yana wuce dukkannin kofofin har ya dangana da inda yake son isa, da sauri wanda yake tsaron wajen ya bud'e masa kofar yana ja baya
"Allah ya baka yawan rai."