Sashe 49
Abinda Ke Cikin Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Wadda aka kira da Feedo din tace tana ajiye kayan hannun ta. Ita dai Amrah bata tanka musu ba, kallon su kawai take dan ba wani gane musu take ba yadda take jin zafin zazzabin na sake karuwa.
Kwalliya ta hau yi mata cikin son nuna kwarewar ta, tana jin yadda Amrah ke fitar da hucin zafi, sai ta rage kwalliyar tayi mata simple sannan ta bata ruwa da paracetamol da Amrah ta nuna mata inda yake ta ballo mata tasha, tayi mata sallama ta tafi.
Tana fita Amrah tayi saurin cire daurin kan, ta kwanta bayan ta rufe kofar dakin da key ta lullube jikin ta gaba daya tana jin sanyi sosai kamar an jefe ta a k'ankara.
***Waige-waige Safwan yake yana neman Sultan, duk wanda ya tambaya sai yace be ganshi ba, haushi ya kamashi ya ciro waya ya kirashi, amma har ta gama ringing be daga ba, maida wayar aljihu yayi da nufin komawa ciki, wani dake tsaye a hanyar fita yace
"Wai sultan kake nema?"
"Eh wallahi, yanzu yanzu fa muna tare."
"Ya tafi ai, shigowa ta kenan naga fitar sa a mota amma be ganni ba kamar ma sauri yake."
"Ok Nagode."
Yace yayi ciki yana jin haushin Sultan din sosai, kenan idan da gaske shi din aka daura wa auren haka zai tafi ya barshi shi kad'ai kenan.
Ciki ya koma suka cigaba da karbar mutane shi dah Mubarak da Adnan.
Bayan kowa ya tafi, suka nufi wajen da suka shirya yin reception, sosai Safwan ya gaji, gashi yana jin wani nauyi a chan kasan zuciyar sa amma ya daure, da yaso yaki zuwa wajen reception din amma yasan hakan zai zama magana a wajen abokan su ace babu shi babu sultan din, dole ya bisu suka je akayi komai aka gama sannan suka nufi gida.
Mah-Mah na zaune cikin yan uwanta tasha gayu sosai ana karbar baki, gefe daya kuma hankalin ta na kan daurin auren, suna jin komai suma daga nan, su Hajiya Umma kuma na ta shiga da fita ana rabon abinci. Ta shigo da manyan coolers din waina da sinasir zata ajiye kenan kunnen su ya jiyo musu abinda mutumin ke cewa. Da sauri duk yan gurin suka kalli juna, sannan suka maida kallon su kan Mah-Mah da ta kusan yin mutuwar zaune.
"Kamar Sultan naji an ce ba Safwan ba fa."
Wata mata tace tana kallon Mah-Mah.
"Haka kuwa nima naji." Wata ma ta fad'a duk suna kallon fuskar Mah-Mah da ta kasa cewa komai sai son tabbatar da abinda kunnen ta ya jiyo mata.
A hankali ta tashi, tayi part din Daddy tana laluben number sa a wayar ta, tana shiga ta rufe kofar ta kirashi, zagaye falon take tana addu'ar Allah sa ya daga dan tasan yana cikin mutane. Ringing din tai tayi amma be daga ba, be masan tana kiran ba dan yadda ya shiga busy ga mutanen da ya tara yana ta kokarin attending ma kowa.
Chanja akalar kiran nata tayi zuwa number Safwan, no answer, Sultan no answer, haka tayi ta kiran duk wanda tasan zata kira amma kamar hadin baki babu wanda ya daga. Burin ta kawai taji halin da Safwan yake ciki, ta kuma ji yadda akayi hakan ta kasance. Toh kodai Sultan ne yayi wani abun da yasa aka maida auren kansa? Tunani tai tayi akan dalilin da zai sa ayi hakan amma ta kasa samo amsa daya. Tashi tayi ta fito, a hanya suka ci karo da Umaima dake ta faman rusa kuka kamar an mata mutuwa, kamar ta make ta haka taji, zata kara mata damuwa akan wadda take ciki da wani banzan kukan ta da ita sam bata ga amfanin sa ba tunda wanda take domin shi be masan tana yi ba.
Zatayi magana ta daga mata hannu da sauri
"Umaimai dan Allah!"
"Bansan me yake faruwa ba ni kaina."
Sai ta wuce ta da sauri tayi gate, har ta kai sai kuma ta fasa, idan ta shiga gidan tace musu me? Komawa tayi ciki tana jiran dawowar su suyi mata bayanin yadda akayi hakan ta kasance.
Rabin hankalin ta ya tafi tunani,bayan Hajiya Umma ta faffada mata magana sai taji da gasken tayi sakaci da yawa, da har bata hana sultan dawowa gidan ba har bayan a daura auren, sai gashi ma da kanta ta neme shi bayan abinda ya aikata a tunanin ta duk kuskure ne, yanzu kuwa da haka ta faru sai taji babu wanda ta tsana kamar Sultan din,musamman yadda aka juya zancen ya koma wani iri daban. Tana nan zaune taji ana ga su Safwan sun dawo, da sauri ta fito, yana tsaye suna magana da wasu yan uwan Daddy, kallo daya tayi masa tasan ba kalou yake ba, yadda yake ta yamutse fuska da yadda ta ga yana fitar da numfashi da d'an sauri yasa tayi saurin isa wajen, ba tare da tace komai ba ta shiga jan hannun sa,bangaren Daddy ta wuce dashi suna shiga ta tura shi sannan ta rufo kofar. Yi yayi kamar zai fadi tayi saurin riko shi tana kiran sunan sa
"Mah-Mah kai na, kai na kamar zai cire, zuciya ta ciwo Mah-Mah, ki taimaka min mutuwa zan, ina jin zafi, ina jin wani iri Mah-Mah."
Kuka ta saka tana jijjigashi
"Me kayi wa kanka Safwan, me kayi, Innalillahi wa Inna ilaihi, nayi da na sanin shigowar ka rayuwar mu Sultan, wannan wacce irin masifa ce. Me kayi Safwan"
"Abinda ya dace shi nayi, shi yafi chanchanta da ya same ta, kuma Shikenan sai a hana shi? Sam hakan ba daidai bane Mah-Mah, me yasa baki fad'a min shi yake son ta ba, saboda karki rasani ko? Saboda ni danki ne ko? Shi kuma bashi da kowa, idan ma ya mutu shikenan ko? Wannan ba Mah-Mah ta bace, Mah-Mah ta ba zata taba haka ba."
"Safwan!" Ta kira sunan sa tana rufe bakin ta
"Karki ce komai, kiyi min Addua Mah-Mah, inajin zafi a zuciya ta, kiyi min Addua ki roka min Allah,ki daina kuka da an kwana biyu shikenan zan manta."
"Kayi shiru, maganar tana kara maka ciwo ne Safwan, ina zuwa, bari na kira Daddy, za'a kaika asibiti zaka samu sauki."
Rike hannun ta yayi da sauri yana lumshe idon sa.
"Karki kira kowa Mah-Mah, ki zauna dani kawai,ki zauna a kusa dani dan Allah."
"Amma kana bukatar likita Safwan,ya za'a yi na barka da ciwo?"
"Toh ki kira min SULTAN." Yace yana kulle idon sa.
***A kofar gidan yayi parking ya dauko waya da niyyar kiran Maigadin, yaaga misscalls rututu, ganin hadda Mah-Mah ya dan saka shi tunanin dalilin kiran. Be bi kiran ba ya kira Maigadin, yana waje kawai yace masa sannan ya kashe, ya kuma kashe wayar tasa dan baya son kowa ya kirashi yanzu.
Karar bude kofar yaji ya dago da sauri, babban mutum ne wanda a kalla zai yi shekaru 50 haka, yana sanye da doguwar riga irin wadda mafiya yawan maza ke sawa yayin zaman gidan, hannun sa rike da wayoyin sa, fuskar sa na nuna tsantsar farin cikin sa. Da sauri Sultan ya balle murfin motar ya fito, suka hadu tun kafin ya karaso wajen motar.
"SULTAN!?"
"Barka da rana." Yace yana dan rissinawa.
"Barka dai." Sai kuma yace
"Bismillah, nan d'in gidan ku ne ai kai ba bako bane."
Ajiyar zuciya Sultan ya sauke dan yana ta tunanin irin karbar da zai masa, sai yaga akasin abinda ya zata, kai tsaye yabi bayan sa, suka shiga gidan yana gaba yana binsa a baya, har suka dangana da main parlour din gidan ba inda yake sauke bakin sa ba, parlour da yake ajiye duk wani bako nasa me muhimmanci.
"Bismillah." Ya nuna masa wajen zama. Zama Sultan yayi yana dan satar kallon parlour yadda ya tsaru, komai na parlour abin kallo ne.
"Ina xuwa." Yace ya fita, chan ya dawo dauke da robar ruwa da cup akan tray ya ajiye a gaban sa.
"Ina cikin tsananin farin ciki yau, Allah ya cika min burin da na dade ina fatan cikar sa, yau gani ga ka Sultan."
"Mun same ku lafiya?"
"Alhamdulillah wallahi, ina Aziza?"
"Ban same ta ba ko da naje gidan, sako ta barmin akan lallai na neme ka, bayan kai akwai wasu mutanen da bansan su waye ba, dalilin da yasa nazo gareka kenan, idan ka san wani abu da ya shafi neman iyaye na, ka fad'a min dan Allah."
Mikewa yayi ya shiga zagaye dakin, Sultan ya bishi da kallo har ya zagayo ya tsaya a gaban sa sannan yace
"Na sani Sultan, nasan kai waye, nasan iyayenka farin sani, sanin da zai yi wuya a samu wanda yayi musu irin wannan sanin."
Da sauri ya mike tsaye,
"Su waye? Aina suke?"
Matsowa yayi ya dafa shi, yayi wani shu'umin murmushi yace
"Relax, kwantar da hankalin ka."
Yace yana wuce shi, ya koma wajen da ya tashi sannan ya nuna masa in da shima ya tashi yace
"Sit."
Zama yayi a gefe, duk ya kasa kwantar da hankalin nasa, yana so yaji wani abu akan su, amma alamu sun nuna ba zai zama abu me sauki ba.
"Sultan." Ya kira sunan sa
"Nasan iyayenka kamar yadda na fad'a maka, kuma nasan inda suke,kuma su ma basu da abun da suka fi burin gani fiye da kai, sai dai hakan ba zata samu ba har sai ka yi wani aiki, aiki me matukar had'ari, idan har ka samu nasara nayi maka alkawarin kaika har gaban su."
"Menene aiki?" Yayi maganar muryar sa ta fito tar dan ya gane wani abu guda daya, akwai abubuwa masu yawan gaske da suke a rufe, da yake bukatar ya bud'e su daya bayan d'aya, zai bi duk umarnin sa domin cimma burin sa.
"Madallah da kai." Yace sannan ya cigaba
"Zagaye take da masu tsaron ta a kalla su goma talatin wanda suka zagaye katangar baki dayan ta, haka daga gate din farko zuwa na biyu akwai masu tsaron wajen su bakwai, daga na biyu zuwa na uku su biyar, kofar da zata sadaka da bangaren akwai masu tsaro su goma.."
Sai ya sake mikewa